Page 7

381 25 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

(An heart touching story)

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_

  *WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

 
   *Page* 7

"Kamar yanda Alhaji Nura da Alhaji Umar suka yanke shawarar haɗuwa a guest house hakan tafaru, da karfe 7:00 ciff motar Alhaji Nura yadanno kai cikin guest house ɗin,  wani wajen shakatawa me kyau naga yanufa,  yana zuwa yasamu wuri yazauna akujerar dake fuskantar Alhaji Umar"

Barka dazuwa cewar Daddy,
Yawwa barka Alhaji,
Alhaji idan har Latif ze zame mana matsala meze hana muyi gaggawar ɗaukan hukunci.

Wani irin hukunci zamu ɗauka kenan Alhaji Nura?
Kasan banason abunda ze kawomin cikass awannan lamarin,  nasa an makantar da Bilal sabida dukiyarshi inason yanuna min komai kafin daga baya insa akasheshi gaba ɗaya yabar duniyar nan.
Amma Wannan Latif yana neman jazamin aiki
Narasa mafita.

"Inada mafita Alhaji"

Mecece mafitar?
Cewar Daddy

Meze hana ayi mishi sharrin shiya turo mutane su watsawa Bilal Acid,  munemo mutane biyu su ɓoye fuskarsu sai suyi videon cewa Su suka watsa mishi kuma Latif ne yaturosu kaga saiya kare rayuwarshi agidan Yari"

Daddy ne yagyara babban rigarshi yace "wato Alhaji Nura ban taɓa zaton zaka kawo good idea kamar haka ba,  to Amma baka ganin hakan zai kawo matsala?"
Babu wata matsala Alhaji kaidai muyi abinda nace kawai.
To shikenan amma idan zeyi gobe nakeson ayi videon domin da zafi-zafi ake dukan karfe,
Karka samu damuwa cewar Alhaji Nura,  nan sukayi ɗan hira kafin daddy yaɗibo wasu maƙudan kuɗi acikin baƙar jaka yabawa Alhaji Nura,  Alhaji Nura yayi godiya yatafi"

"Bilal tunanin daya dami zuciyarshi shine Wayake neman hallakashi?  Meya tarewa meshi?  A iya saninshi bashida abokin gaba,  to wayene wannan,  wayake kokarin illatamin rayuwa?
Haka yakarashe tambayoyinshi babu me bashi amsa,  filo yaɗauko yarungume yana kallon silin ɗin ɗakin, tunowa yayi da kanwarshi Nabila wanda duk lokacin data ganshi cikin damuwa hankalinta baya taɓa kwanciya, Runtse idonshi yayi yana mejin bakon cikin rashin 'yar uwarshi da iyayenshi,  hawayene suka fara fita a idonshi wanda yake ganin hakan shine maslaha agareshi,  awannan yanayin idan beyi kuka ba zhciyarshi zata iya fasa kirjinshi tafito,
Yana cikin wannan yanayin Daddy yayi sallama yashigo,  yadai Bilal?

Lafiya Daddy cewar Bilal,
Zama Daddy yayi agefen gadon yariko hannun Bilal yana shafawa yace "my Son Banaso kasa kanka cikin damuwa, da nayi niyan nakaika India aduba idonka konawa zan kashe idan lafiyar idonka zata samu ashirye nake nakashe, amma kash mumunan labari ɗazu munyi waya da Doctor Shankar babban likitan idanu dake kasar India,  nayi mishi bayanin abunda yafaru yace ai idan an watsawa mutum Acid a ido kuma yamurza idon sosai Aciɗin yabi cikin kwayar idanunshi to bazai taɓa samun sauki ba sai wani ikon Allah,
Bilal am sorry nazama Helpless akanka nakasa taimakonka da'ace zan iya baka nawa idon wallahi dana baka Bilal sabida kai saurayi ne nikuma girma yazo,  kayi hakuri Bilal Daddy yakarashe maganar yana kuka kamar dagaske"

"Bilal shiru yayi yana jin maganar Daddy yasan cewa duk duniya babu wanda yakesonshi bayan Family ɗinshi sai Daddy,
Daddy kadaina kuka Haka Allah yatsaramin rayuwata,  amma dan Allah Daddy inason kayimin amsar tambaya ɗaya"

Zuciyar Daddy wani irin bugawa tayi dakarfi yace am am.. am wace tambaya ce wannan Bilal?

Daddy shin mahaifina yanada Abokin gabane?

Shiru Daddy yayi yana tunani,
Daddy please answer my question,
Ajiyar zuciya Daddy yasauke yace "my son mahaifinka yanada abokin gaba guda ɗaya wanda nasani amma yanzu sun shirya suna abota kamar ba waɗanda suka taɓa gaba ba, 
Daddy wayene wannan?

Abban Latif!!!!   Cewar Daddy,
Abban Latif kuma?
Aganina shine aminin babana kuma babana ya aminta dashi sosai.

Bilal wannan abotar tasu ta BOGE ce bata gaskiya ba,
Mahaifinka yanada tarin dukiya wanda har wani lokacin yakan manta da wasu kadarorinshi,  sun kasance abokai sosai da Abban Latif amma me?  Sai kawai wata rana Abban Latif yayiwa mahaifinka babban sata satar Company Uku.
Da Mahaifinka yagano hakan saiya koreshi a aiki tun daga wannan rana gaba me tsanani yashiga tsakaninsu, nine nakirasu nayi musu nasiha kafin mahaifinka yabashi hakuri sukaci gaba dazama tare.

"Nabaka wannan labarine sabida karka Aminta da mutum sosai, wanda ka amince mishi shine wanda ze cutar dakai"

Abban Latif kuma?  Cewar Bilal.

Daddy ganin yasa shakku azuciyar Bilal ba karamin farin ciki yayi ba,  yasake ɗaurawa da "Bilal banaso kafaɗawa kowa wannan labari kaji?
Bilal yagiɗa kai,
Yawwa sakko muje downstair kadaina zama kai kaɗai aɗaki sabida yawan tunani?
Bilal yace to Daddy"

Hannunshi Daddy yakamo suka nufi kasa,  Afrah nakwance a falo daga ita sai wata 'yar karamar riga da wando skin tired Kanta babu ɗankwali tana cin cingom kasss kass kass rike da wata ƙatuwar waya tana chat da friends nata,  ganinsu Daddy yasa ta tashi daga kwancen tazauna tareda cewa "Daddy kazama ɗan jagora ne?

What are you saying Afrah yayanki nefa kaddara tasameshi,  keda kike sonshi ai kuka yakamata kiyi..... No no no Daddy ai ni nadaina sonshi yanzu,  mezanyi da makaho?  Ai kawayena sai suyimin dariya.  Daddy ni raina ma ya ɓaci .... Bye

Tana gama faɗin haka ta mike santal santal santal kamar nakasasshen rakumi tayi gaba.
Bilal har cikin zuciyarshi yaji zafin kiranshi  makaho datayi amma ba komai zanyi maganinki.
Daddy ya katse mishi tunani dace "Bilal sai kayi hakuri da Afrah kasan yarinya ce"
Eh Daddy ba matsala.
Yawwa yanzu ina makullin Companyn yake kabani saina nemi wanda ze zauna madadinka,  koda shike ga Hafiz nanma ai kaninka ne saiya zauna kawai right?

Mamaki ne yakama Bilal ko kwana biyu beyi ba an farakarɓan makulli?  Yace to Daddy ka kaini ɗaki in ɗauka mishi.

_✔ote comment & share_

✍🏻   *JIDDAH S MAPI*

MAKAUNIYA CE Donde viven las historias. Descúbrelo ahora