page 34

396 24 5
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 34...

"Murmushi kawai Minal tayi, suka nufi d'akin, wani d'akine mai kyau ta kaita ne d'auke da pink & white colour, gadone babba me kyau sai Teddy's dayawa, Baby ce tace " sister colour na d'akin yamiki?"
Cikin murmushi Minal tace "wallahi yamin kyau inason pink colour da fari"
Dariya baby tayi tace "wow kice munason Abu d'aya, shiyasa Allah yahad'amu, bakisan wani Abu ba, tunda naganki naji kin kara burgeni sabida shiru shirunki, Allah yasa dai zamuyi tazama dake"
Minal tayi Dariya tace "Ameen, yanzu tashi muje muyi aiki karmu bar Umma ta gaji, sabida ta gaji a asibiti dayawa".

Baby tace " Haba ke kuma ni ai bana aiki, da zaran nadawo daga school za'a kawomin Abinci inci, akawomin ruwan wanka inyi, sai nayi sallah sai bacci".

Minal cikin mamaki tace "yanzu babba dake sai an kawo miki abinci? Kuma sai an kai miki ruwan wanka?"

Cikin dariya Baby tace "eh mana Sister meye aciki"
Minal shiru tayi.

Baby tace "tashi kiyi wanka sai kici Abinci kisha maganinki kiyi bacci".
Minal tamike tace " to".

"Kwana biyu Bilal ya rame yayi haske sosai, tunani bibbiyu suka taru suka mishi yawa, ga tunanin Minal dayake hanashi bacci, ga kuma tunanin yanda Daddy yake son ya kasheshi, wannan wani irin bala'i ne?".

Afili yafurta "anya yarinyarnan bata koma Nigeria ba?
To Amma waye zai bata kud'in jirgi?"
Tashi yayi da sauri yace "dolene nakoma Nigeria gobe, gashi batada waya, oh God help me out".

Shirya kayanshi yafara da sauri yana tattara abubuwan dayake bukata, drawer yabud'e yaga babu kud'i, murmushi yayi yace "nasan za'a Rina ta tafi Nigeria".

Minal tayi wanka taci Abinci sannan tasha magani,
Suna cikin hira da baby ne mommy ta bud'e d'akin tace " sannunku yarana"
Baby ce tace "yawwa mommyn mu"
Minal dariya kawai tayi.

Mommy tace "yanzunnan Daddynku yacemin gobe zamu tafi Nigeria sabida ana nemanshi a office, so abinda nakeso daku kuzo muje d'akina Ku kintsa min kayana kafin kuzo Ku kintsa naku, Minal kid'anyi aiki kad'an sabida zaki d'an samu saukin jikinki".

" to mommy" shine abinda suka fad'a.
Bayan wasu mintina kad'an suka kintsa kayansu Dana mommy.

_Asuba tagari_

Bilal ne ya d'auko trolleyn shi da wayoyinshi yanata sauri ya iso airport.
Taxi ya kama yatafi babban airport na kasar India, burinshi kawai ya iso Nigeria yaga Beutynshi,
Suna zuwa yaje ya nuna musu visanshi yashige cikin jirgi yayi kwanciyarshi, tareda rufe fuskarshi da handkerchief,
A hankli yace "I miss you beauty" kashe wayarshi yayi duka".

Minal da Baby da Mommy sai kuma Daddy sun shirya kayansu a mota dukda mommy tahana minal yin komai hakan bai hanata shirya kayanba, suna gamawa driver yajasu sai babban airport.

Da zuwansu airport suka tarar jirgi ya kusa tashi, da sauri suka shiga duk suka zauna.
Kowa yana jiran jirgi yatashi.
Daidai lokacin da jirgi zai tashine Minal taji kafar mutum yana cokalin ta, da sauri ta juya tanason tayi bala'i, kawai taga trolley irin na Bilal, lek'awa tad'anyi a hankali taga Meshi ya rufe fuskarshi da handkerchief,
Ido ta tsurawa meshi, hannunshi takalla saida zuciyarta tace dimm, ganin Bilal kwance sabida tasan wannan tabbas zobenta ne,
Da sauri tajuyar da kanta gefe wajen Baby,
Tace "sister kibani Nikab naki mana insa wallahi iska yamin yawa".

Baby tayi dariya tace " to bari na Ciro miki kinsanni dason Nikab kuwa? Hmmm ai lokacin da Daddy zaije Saudiya tsarabar Nikab nace ya kawomin ai kuwa yakawomin dayawa zan baki sauran ma idan mukaje gida"

Minal ganin surutun Baby yana b'ata mata lokaci yasa tace "bari naduba da kaina"
Baby tarikota tace "no ai ke bakida lafiya, bari nad'auko miki"

Minal komawa tayi ta zauna jikinta duk yana rawa tsoronta d'aya kada Bilal yamike ya ganta,
Baby ce tazo da Nikab d'in tace "bari nad'aura miki, ke ai dama Nikab yafi dacewa dake, sabida kinada kyau"
Murmushi kawai minal tayi.
Saida baby tad'aura mata Nikab d'in kafin taji sauki a ranta,
Biro da 'yar takadda tace "baby inason ki rubutamin wani Abu, sabida inason koyan karatu da rubutu".

Baby ce tayi dariya tace " kawo takaddar na rubuta miki, amma kina fad'an abinda zan rubuta"

Minal tace "to yanzu dai muyi misali da mutum d'aya acikin jirginnan, sai muyi akanshi"

Baby tace "okay ta amma dawa zamuyi? Kodai muyi da daddy?"

Minal tayi dariya tace "Aa muyi da wancan Wanda yarufe fuskarshi da handkerchief d'in".

Baby tace " yawwa nima tin d'azu hankalina akanshi, da Alama tunani yake, Amma daga ganinshi fa handsome ne"

Minal ce tayi dariya tace "hmmm wasu mutanen idan kin gansu handsome saikice inama da saurayinki ne, to Amma idan kin zauna dasu zakice inama da ban sanshi ba"

Baby tace "kumafa hakane yanzu kina fad'amin abinda zan rubuta"

Minal tace "ki rubuta, Assalamu Alaikum, bawan Allah meyasa ka rufe fuskarka? Shin akwai wacce kake tsoron ta ganka ne?
Toni sunana Minal, kuma idan nakoma Nigeria bazaka kara ganina ba, na tsaneka, banason ganin fuskarka, ina rokon Allah har na fita a jirginnan kada ka bud'e fuskarka, hasalima ko sunanka aka kira yana sani bak'in ciki, gara ka koma Inda ka tashi domin bazan tab'a yadda kasan inda nakeba, daga Minal wacce aka lalatawa rayuwa sabida kai, ka taimaka mata sabida wani dalili naka, ka b'ata mata rayuwa, Allah ya isa tsakanina dakai.

Baby ce ta d'ago tace "sister wani irin magana ne wannan?"

Dariya Minal tayi tace "ai koyan rubutu zanyi, kede kawai kibani ai ba gani zaiyi ba kawai dai inason in karanta in b'oye sabida wata rana in gwadawa saurayina".

Dariya Baby tayi tace "gashi to ai ba wannan sakon yakamata ki rubutawa saurayinki ba, sakon soyayya yafi dad'i koda Neman tsokana ne, kamar nida yaya Mujahid nawa".

Minal bata kara magana ba, shiru kawai tayi ta karb'i takaddar.

Lokacin da jirgi ya sauka Minal ce tayi sauri zata fita, Baby ce tariko hannunta tace " ya zaki fita ki barni mudai je mu biyu mubar su mommy".

Minal ma tariko hannunta daidai wurin da Bilal yake kwance, tad'an duka kad'an ta cusa Takaddan datayi rubutun acikin Aljihun rigarshi,
Da sauri suka fita.

Bayan su mommy sun fito driver yazo d'aukansu, Hanyar Abuja suka d'auka.

✔ote & comment

_Jiddah S Mapi_

Watpadd @Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now