page 23

382 22 2
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 23...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Nine nake iskancin?"

Shiru tayi batayi magana ba,
Yace "ok shiga ciki"

Shiga tayi tanata gunguni.

Shima zagayawa yayi yashiga,
Yana shiga ya rufe kofar da key, daganan bai sake cewa komai ba.

Minal ce taji shirun yayi yawa tace "yaya Bilal kayi magana don Umma tana jirana kuma idan na dad'e zata min fad'a"

Bai ce komai ba, sai kawai ya rik'o hannunta, ya d'aura a kirjinshi, tareda cewa "Minal kiji yanda zuciyata take bugawa a duk lokacin dana zauna kusa dake, jiya nayi Missing naki sosai, nakasa bacci sabida banji numfashinki ba, Minal abinda baki sani ba shine duk dare saina rungumeki kafin na iya bacci, Amma jiya na wahala sosai, Minal nasan bakya gani Amma kina ji, ina son koda bazaki gani ba to ki kalli idona yanzu"

Minal taji yanda zuciyarshi take bugawa sosai, abin harya bata tsoro, to Amma abinda yake d'aure mata kai shine irin maganganun dayake mata, Lumshe manyan idanunta tayi, nan gashin idonta yabi ya lafe, lips nata tad'an tab'e kad'an.

Bilal ido yazuba mata yana kallon irin baiwar kyau da Allah ya bata, shi a duniya babu abinda yake birgeshi kamar yaga ta tab'e baki cikin shagwab'a, hannun shi yasa akan lips nata yana zagayawa a hankali.

Da sauri ta juya kanta gefe tareda cewa "yaya Bilal niba 'yar iska bace, ka daina tab'amin jiki"

Bilal yace "Minal nima bad'an iska bane, ni mijinki ne kuma inada ikon tab'a ko ina a jikinki"

Da sauri ta janye hannunta daga kirjinshi tace "dama kasan ni matarka ce kuma kake zargina da fasik'anci? Kuma kake barina na kwana a k'asa? Yaya Bilal ka cuceni, ka wulak'antawa ni, yanzu kuma kazo ka yaudareni? to Allah yafika"
Tafad'a cikin hawaye.

Bilal ne ya juyo da fuskarta ya rike, handkerchief ya d'auko yafara goge mata hawayen, janye kanta tayi tace "bud'emin k'ofa in tafi Umma tana jirana"

yace "Minal ki taimaka muje gida yau ki kwana a gefena ko zan samu nayi bacci"

Cikin k'uluwa da b'acin rai Minal tace "yaya Bilal ka bud'emin k'ofa nace"

"Minal wallahi bazan iya bacci ba idan bakya d'akin"

Hawayene yafara fita a idanunta babu kakkautawa tace "wato inje in kwanta a d'akinka kai kasamu kayi bacci, nikuma ko oho ko? Wai meyasa Ku masu kud'i kuka fiye son kai ne? Meyasa Baku damu da damuwar wani ba? Nasan yaudarata kazo yi, sabida inje gidanku Ku samu abin wulak'antawa? To bazan je ba, nida gidanku har a bada..."

Bilal saurin had'a bakinshi yayi da nata Dan bayason yaji sauran maganar nata da baya mishi dad'i a cikin kunnuwanshi.

Waro ido tayi, tanajin yanda yake shan bakinta kamar yasamu sweet, (kuyi hakuri haka yanayin labarin yake)

mintsininshi tafara, tana dukan bayanshi, Amma me? Bilal yatafi wata duniyar, bayama jinta, Karo na farko daya fara kissing na mace kenan a rayuwarshi.
Saida yaga tayi shiru jikinta ya mutu kafin ya saketa yana mayar da numfashi,
Minal a halin yanzu tsoro ma yake bata, cikin dak'ewa tace
"dama abinda ya kawoka kenan? Kazo kaci mutunci na? Ka nunamin cewar ban kaiba, Bilal mu talakawa ne bamuda wadata Amma kasani munada wadatar zuci Allah ya isa tsakanina dakai...."

Bilal shi yama fita a hayyacinshi, jikinshi ya mutu sosai, bud'e kofar yayi, cikin wata irin murya dashi kanshi baisan yana da ita ba yace "fita"

Minal tace "dole ka koreni tunda kagama abinda kakeso"

Bilal yakara cewa "ki fita nace"

Dama ai ba zama zanyi ba, kuma Allah ya isana....

yace "idan baki fita ba komai zai iya faruwa Minal, karki kara magana a Motarnan, muryarki tana d'agamin hankali"

Minal fita tayi a motar tace "Allah ya isana ban yafe ba"

Rufe kofar yayi, yaja motar da mugun speed yabar unguwar, shi kad'ai yasan me yakeji a jikinshi, idan yakara minti biyu tareda ita komai zai iya faruwa, shiyasa yabar mata Unguwar gaba d'aya.

tsayawa tayi tanajin karar tafiyarshi, hawaye ta goge da bakin hijabinta, tace "yanzu ya zata ni 'yar iska ce, shiyasa yayi min haka, Amma insha Allahu bazan kara fita ba idan yazo".

Bilal yana zuwa gida yawuce d'akinshi cikin wani irin yanayi, Hajiya babba ce taga yanda yake tafiya kamar zai fad'i, da sauri takira Afrah tace mata.

"Afrah kinsan me? Yanzu naga Bilal naki yazo ya wuce ko sallama baiyi ba, da Alama wannan Makauniyar Ce ta b'ata mishi rai a Asibiti, yanzu abinda za'ayi kije ki ki jiyo meya sameshi"

Afrah tayi farfar da ido tace "da gaske kike Hajiya babba ta?"

Hajiya babba tace "yo dama karya zan miki?"

Da sauri Afrah tace "bari inje d'akin Mommy Nasa Abayarta tukun, don bayason kananan kaya"

Hajiya babba tace "oya jeki"

Afrah d'akin Mommy ta nufa, tana zuwa tace "Mommy Dan Allah kibani Abayarki d'aya mana zanje wajen yaya Bilal nawa ne kuma bayason kananan kaya"

Mommy ce tace "d'auka mana Auta abayar ma saikin tambaya?"

Cikin jin dad'i tace "yawwa nagode my Mom"

'Daukar Abayar tayi tanufi d'akinta tareda yin kwalliya, tasa Abayr babu laifi tayi kyau
Ta nufi d'akin Hajiya babba tace "Hajiyata Nayi kyau?"

Hajiya babba tace "iye su takwarata anti kyau, irin wannan kyau kamar sarauniya? Kice yau idan Bilal yaganki saiya rud'e, Amma matsalata dake d'ayane, shine wannan jikin naki kamar buhun shinkafa"

Cikin fushi Afrah tace "ai Allah ne ya halicceni haka"

Tana fad'a ta nufi d'akin Bilal knocking tayi.

Bilal a daidai lokacin yagama cire kayanshi ya d'aura towel zai shiga toilet kenan yaji ana knocking.

Cikin b'acin rai yace "waye?"

Ba'ayi magana ba har yanzu kuma ba'a daina knocking ba,
Zuwa yayi ya bud'e kofar, sai kawai yayi arba da Afrah, tsaki yaja yace "what do you want"

Afrah tace "dama yaya naga kashigo ranka a b'ace shine nace ko zan iya taimaka maka?"

Dame zaki taimaka min?

Afrah tace "koma menene yaya, ai shi namiji baya rasa buk'ata"

yace "okay nagode Amma banaso ki kai kasuwa sabida ni jikina a tsarkake yake, kuma bazan b'ata ba, na kiyayeshi ne wa mutum d'aya a duniya, ba kowa bace kuma sai Matata,
Keda kika saba rabarwa maza a titi, kije nabar musu, Nidai bana buk'ata,
Kuma kibi a hankali sabida cutar zamani tayi yawa sosai".
Yana fad'an haka yaja kofar yarufe Gibb, yabar Afrah tsaye.

"Shiga toilet yayi ya kunna shower, ruwa yanabin duk jikinshi, idanunshi a rufe, babu abinda yake tunawa sai moment nashi da ita, yarinyar ta rud'ashi yanda baiyi zato ba, ada idan abokanshi sukace mace zata iya rud'ashi sai yaga kamar karya suke, sai gashi yau yarinya karama wacce bazata wuce 17-18 ba tana Neman hanashi sukuni."

A hankali ya bud'e idanunshi Wanda sukayi jaa, ya sauk'esu akan towel nashi datake d'aurawa idan tayi wanka, tunawa yayi da lokacin da tace badroom, murmushi yayi a hankali ya furta "Badroom"
'Daukan towel d'in yayi ya rungume a jikinshi cikin kasala yace.

"I Miss You"

_✔ote & comment_

Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now