Page 3

549 26 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

#an heart touching story

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_

*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

*Page* 3

"Latif ne yabi bayan Bilal, yana shiga toilet ɗin yaga Bilal yana sheƙa Amai kamar zai amayar da kayan cikinshi, mamaki ne yakama Latif yatsuguna yana tambayan Bilal bakada lafiya ne?"

Bilal ne yaɗago kanshi a zuciye yace "kai wani irin mutum ne Latif? Tayaya zakaci abinda yafito daga hanun wannan ƙazamar? Yanzu fa ina zuwa naga almajirai sun taru akanta suna wawa, shine zaka iya cin abincinta?"

Knocking na kofar office ɗin sukaji anayi, Latif ne yace waye?
Daga waje naji muryar wani yana cewa ku buɗe kofar.

Bilal ne ya umurci Latif dayaje yabuɗe kofar dan yanajin muryar kamar na Daddy, Latif ne yaje yabuɗe kofar, yana buɗewa yace sannu dazuwa Daddy, mutumin baiyi mishi magana ba yawuce ciki, Latif ne yace "to Allah yasa lafiya"

Ina Bilal? cewar mutumin, Latif ne yace "yana toilet Amai yakeyi tin ɗazu"

"Meya sameshi?" cewar mutumin
Latif ne yayi mishi bayanin duk abunda yafaru tsakanin Bilal da Minal.

Numfashi mutumin yasauke sannan yace "kana nufin kacemin yarinyan ma ta tsaneshi?"

Latif ne yagiɗa kai yace "kwarai kuwa Daddy ni abunda yafi damuna shine yanda yake wulaƙanta yarinyan a idon kowa, inda Allah yataimaka yarinyan bata bari itama"

Daidai lokacin Bilal yafito daga toilet yace "sannu dazuwa Daddy ga wajen zama"

Mutumin ne yanemi waje yazauna yana fuskantar Bilal.

Bilal meyasa kake wulaƙanta Afrah?
Katunafa Afrah 'yata ce tacikina,
Inason Afrah yanda bakayi tsammani ba.
Sanin kanka ne ciki ɗaya muka fito da Babanka, inada tabbacin da babanka yanada rai da tuni kadaɗe da Auren Afrah.

"Agaskiya Daddy bazan iya Auren Afrah ba!
Sabida ni amatsayin kanwata naɗauke ta, hasalima ni halin Afrah sam beyimin ba"

Daddy Afrah ba kalar macen dazan Aura bace, ninafi son mace wanda idonta be buɗeba....
Ya isa Bilal, kadakata haka!

Agabana kake cewa bakason 'yata?
To bara nafaɗa maka ko ubanka ne be isa nace "Eh" yace "Aa" ba.

Yaushe aka haifeka?

Daddy nima inada tabbacin da Mahaifina yanada rai bazai taɓa yimin abu dole ba.

Daddy yace nika faɗawa haka Bilal?
Bilal yace "ka gafarceni Daddy"

Fita daga office ɗin mutumin yayi azuciye.

Latif ne yazauna a inda Daddy ya tashi yana fuskantar Bilal,
Yace "Bilal kayi babban kuskure! Meyasa zakace bakason 'yarshi a idonshi? Ai kobaka santa to be kamata kafaɗa mishi ba, Bilal mutane yanzu anaso kabisu ahankali ne badan kana tsoronsu ba".
Saidan bakasan zuciyar wani ba.

Bilal ne yace "Latif lamarin gidanmu ya isheni, su basa duba abinda nakeso kansu kawai suka sani, gara nafito fili nafaɗa musu abinda yake raina, domin ko sama da kasa zasu haɗu bazan Auri Afrah ba".

Latif yace "hakane Amma karage nuna tsanan dakake mata afili sabida tsaro ba tsoro ba"

Bilal yace "ok zan duba nagani"

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now