page 16

353 21 4
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 16...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Ni banida Aljanu hasalima kora kunya kakeyi da hauka, ina kara tunatar maka niba kurma bace ni MAKAUNIYA CE, naji duk abinda tafad'a, sandarta ta d'auko zata shiga bedroom yayi saurin rikewa, " ke me kike nufi? Dan bakya ganin komai shiyasa zaki min sharri? Ni nahanaki gani? Ko ni na toshe idanunki? Wato kina jin bak'in cikin ina kallon duniya ke bakya gani ko? To indai hassada ne haka zaki kare a Makauniya"

"Na yadda yaya Bilal koda nakare a Makauniya Allah yasani ni Makauniya ce a ido, Amma ba'a zuciya ba irin naka, Kaine ka Makance da duniya, kud'in Ku ya makantar daku, daga kai har kannenka, Amma ni idona ne kad'ai a Makance ba Zuciyata ba, tana gama fad'an haka ta sakar mishi sandar tafara Neman hanya da hannunta har ta iso bedroom"

"Kwankwaso yarike yana kallon ikon Allah, lalle yarinyar nan tana Neman ta rainani dayawa, bata da laifi nida nake kyaleta ne da laifin, yana fad'an haka yawuce d'akin Sabir, Sabir yana kwance yaga Bilal, Aa yaya Bilal Kaine?, eh wallahi Sabir nine ya kake? Lafiya lau Yaya, Amm Sabir dama aika nakeson in baka, Pls idan kaje kasuwa ka siyo min bulala irin dogon nan, Dariya Sabir yayi, yace " yaya Dan Allah me zakayi da bulala?"
"Ina ruwanka, kaide kawai kasiyomin".
Yana fad'a yafita a d'akin.

_washe gari_
Madina ce tazo gaida Minal, tambayarta take ya Umma?
" Umma lafiyarta kalau wallahi, tace in gaisheki sosai, kuma in fad'a miki tana kewarki"

Hmm Umma kenan batasan tafita keya bako? Ai yanzu Madina da ace Umma zatazo ta d'aukeni a cikin gidan nan da nafi kowa farin ciki, Madina wannan gidan k'azamin gidane, babu tsafta a cikin ta, kowa yana cutar da d'an uwanshi, ban tab'a ga Family da basa son junarsu ba irin wannan, kiduba kigani Madina, Daddy yana cutar da Bilal, Bilal yana cutar da ni, Hafeez yana cutar da Daddy, domin Akwai wata rana danaji Hafeez yana waya da abokananshi akan su tari Daddy a hanya zai fita da kud'i yanzu, Hajiya babba tana cutar da jikarta, ta hanyar d'aurata akan turban rashin kunya,  Dan Allah Madina wannan Familyn zasu samu Albarka?"

"Gaskiya Minal wannan ba Family bane, to Amma ai ke kinsan gaskiya me ze hana kifad'awa kowa gaskiyar magana ko zasu kintsa Kansu"
Aa Madina babu Wanda ze yadda dani a cikinsu, hasalima duk sun tsane ni, Sabir ne kad'ai nake samun sauk'i a wajenshi, shima yanzu Bilal yace kar in b'ata mishi k'ani, ya zanyi da rayuwata Madina? yaya zanyi? Ni wawiya ce Madina, a lokacin da sukazo tambayar Aurena da nayi bincike da duk haka bata faru ba, Amma babu komai Akwai Allah"

"Gaskiya ne Minal Akwai Allah ki rika yin Addu'o'i safe da yamma, fad'in Alhamdllh da Allahu Akhbar kada yafita a bakinki, sannan Uwa Uba kibi mijinki sahu da k'afa, koba komai Bilal ya Aureki, bai kamata yana fad'a kina fad'a ba, idan kinga ranshi ya b'aci ki bashi hakuri, karki dinga nuna ke ana cutar dake kinji k'awata?"

"Naji Madina kuma na gode, in Allah ya yadda zanyi duk yanda kikace"

"Bilal yafara tausayawa Afrah, koba komai mahaifinta ya rikeni tsakaninshi da Allah, yarinyar tana sona, sannan idan na Aureta zata canja halinta, kuma zan samu lada, na tabba ta da Abbana yana Raye yaga yanda Afrah take sona, to da babu abinda zai hana Auren nan, me ze hana in yadda da buk'atarsu ko sau d'aya ne? Da kuwa Abba na zaiji dad'i"

"Da yamma Daddy yana wajen shakatawa, Bilal yazo ya sameshi, Aa  Bilal ya kake? Lafiya lau Daddy, dama wata magana nakeson muyi dakai,
Zuciyat Daddy ne tabada sauti dumm, to Allah yasa ba wata maganar yaji ba"

"Ina...ina jinka Bilal Daddy yafad'a da alamar rashin gaskiya,
" amm Daddy dama ina son in fad'a maka na yadda zan Auri Afrah".

"Da sauri Daddy yad'ago kanshi, Dan gaskata ko Bilal ne yake magana,
Zaka Auri Afrah? Bilal ka yadda har zuciyarka?"
Eh Daddy na yadda zan Aureta koba komai Afrah 'yar uwata ce, kuma da Abba na yana Raye inada tabbacin shi zai had'a Auren nan,
Kuma Daddy dama ina son fad'a maka, ni ban yadda da hatsarin motane kad'ai ya kashe iyayene da k'anwata ba, tabbas Akwai wata kullalliyaa, koma dai menene saina bincika, kuma saina d'au fansa"

"Jikin daddy ne yafara rawa, cikin in ina yafara fad'an hab...hab...haba Bilal meyasa kafiye bincike da zargine?
Bincike fa ba kyau bakaji Allah yace (wala ta jassasuu) ba, kazomin da maganar farin ciki kuma kana kokarin tuno Min da k'anina wanda yafi kowa sona!, Wanda nayi mishi laifi Amma shi yazo wajena yabani hakuri, karka kara wannan maganar Bilal kana jina? To Daddy insha Allahu bazan kara ba,
Yawwa d'an Albarka, yanzu yaushe kakeson ayi bikin naku kaida Afrah?
Daddy ni koda yaushe ma kawai ayi, to to nan da Sati  biyu yayi maka?
Eh daddy yayi".

" da dare Minal tana kwance a kasa taji gud'a cikin d'aki, tashi tayi ta shiga Falo, Hajiya babba ce tace "abawa masu gani waje suyi gud'a jikata ta kusa zama Uwar gida agidan Bilal"

"Minal bata gane zancen ba, tadai sake kunne tanajin maganar, kamar Almara"

_To readers Afrah zata Auri Bilal, can you emerging yanda  wannan Familyn zata k'aya?_

✔ote & comment

_Jiddah S Mapi_

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now