page 36

412 24 1
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 36...
*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Har d'aki Afrah takaishi, tana zuwa ta ajiye mishi jakarshi, tashige cikin toilet d'in, ruwan wanka ta had'a mishi, tareda fesawa towel nashi turare, fita tayi taje wurin dayake zaune gefen gado ta dafa kafad'arshi tace.

"Yaya kaje kayi wanka sai kayi sallah, sai kaci Abinci kafin ka huta"

Murmushi yayi yace "nagode Afrah"

Afrah ma cikin tausayinshi tace "ka daina godemin yaya"

Tashi yayi yashiga toilet itama Afrah fita tayi da niyar dafa mishi indomie.

Bayan Minti talatin Bilal yagama wankarshi, yana fitowa yaga Afrah zaune kan gado hannunta rikeda Plate, murmushi yayi mata Yawuce yaje ya shafa mai, wardrobe yaje ya d'auko kayan baccinshi, ya koma toilet yasa kafin ya fito,
Afrah ce tace.

"Yaya ga abincinka"

Karb'a yayi ya bud'e yafara ci, gishiri yayi yawa a abincin amma ya zaiyi yarinyar ta damu dashi sosai, dahaka ya daure ya cinye indomie Tass, yace.

"Yayi dad'i"

Dariya Afrah tayi tace "nagode, yanzu ka kwanta ka huta"

Bilal yace "sai nayi sallah"

Afrah tace "oh hakane fa, kayi sallah saika kwanta"

Tashi Bilal yayi, ya idar da sallah tareda yin nafila raka'a biyu, yana idarwa yahau gado ya kwanta zuciyarshi a cunkushe, bayajin dad'in komai, magana ma daurewa kawai yake yi, Afrah ce ta rufe shi da bargo, cikin sanyin murya tace.
"Good Night"

Juyawa tayi zata tafi taji ya riko hannunta, zuciyarta ne ta tsinke, da sauri ta juya Dan tabbatar da shine ya rike hannunta,
Ganin Bilal yana hawaye abin ya matukar tada mata hankali, da sauri ta karasa wurinshi tana tambayarshi ko lafiya?.

Hannunta ya damke yace "Afrah ki taimaka ki nema min ita, wallahi ina cikin matsala, bazan iya bacci ba sai naji muryanta, koda ba magana me dad'i zata fad'amin ba kitaimakeni...."

Afrah jin dalilin kukanshi ba karamin haushi abun yabata ba, ita ta tsani ayi zancen yarinyar a gabanta, ko sunan Minal bataso akira mata, cikin danne fushinta, tafara shafa gefen fuskarshi tana bashi hakuri, a Hankali yadaina kukan yana sauke ajiyar zuciya, Saida yayi bacci kafin tafice a d'akin tana kara jin tsanar Minal a ranta.

Minal da baby suna cikin jin dad'insu, yau suna zaune a falo Mommy tana yiwa Minal kitso tace "Albishirinku"

A tare sukace "goro"

Mommy tace "Daddynku yace zamuje Adamawa gobe idan Allah ya kaimu"

Baby ce tayi tsalle ta diro tace "da gaske kike mommy?"

Hararanta Mommy tayi tace "dama ina miki wasane?"

Cikin jin dad'i Baby tace "yawwa zanje inga baffa na"

Minal ma murna tayi Dan dama zaman gida ya isheta, tashi sukayi kowacce tafara had'a kayanta, Mommy ce tabaiwa Minal wasu dogayen rigunan Abaya masu kyau,
Minal godiya tayi tana kara jin matar a ranta sosai, ji take kamar Ummanta, hawayen da suka fito a idanunta ta share tunawa da Ummanta datayi,
A zuciyarta tace.

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now