page 25

381 23 6
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 25...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Hajiya babba tace "yanzu nasan inada jika, bari nabaki wani kissa, kinga shi namiji? Idan yace miki bayason irin dressing dakikeyi to wallahi karyane, yana fad'an hakane sabida bayason yabada kanshi awajenki, Amma kinsan me? Kiyi dressing naki da kananan kaya, tananne zakija hankalinshi, musamman idan yana ganin surarki, kin gane?"

Dariya Afrah tayi tace "nagane Hajiya babba ta, kina nufin inyi tasa kananan kaya babu wata matsala kenan?"

Hajiya babba tace "hakan take jikata"

"To hajiya babba yauma zanyi hakan"

Bilal kuma yana zuwa gida ya kwanta a k'asa kan tyles ya lumshe idonshi yana tunanin rayuwa.

Knocking na kofar akayi, cikin kasala yace waye? Ba'ai magana ba yaja tsaki yaci gaba da tunaninshi, knocking aka karayi,
Tashi yayi idon shi har yana rufewa, yaje ya bud'e kofar.

Afrah yayi karo da ita tasha wani Wando daidai gwiwa, rigar jikinta da akwai gara babu,
Duk jikinta ana gani,
Bilal juyawa yayi yace "Auzubillahi minashaid'anirrajim"

Afrah ce tace "yaya akwai Abinda kake b'ukata ne?"

"No bana buk'atar komai"

Shiga cikin d'akin tayi tareda dafa kafad'arshi, tace "yaya awannan lokacin kowani namiji yana tareda matarshi kai meyasa bazakaso kazauna da mace ba?"

Bilal yace "wannan ba abinda ya shafeki bane ba, hasalima ni idan mace tasa kayan da suka fito da surarta bata tab'a birgeni"

"Yaya Bilal nasan kana buk'ata ta sosai, kawai nok'ewa kake"

Cikin tsawa yace "Afrah bana buk'atarki ko kad'an, hasalima 'yar uwata na d'aukeki, inajin bak'in cikin yanda kike rayuwa kamar dabba, koba komai ai ke musulma ce, sannan ina gargad'anki da kifita a d'akin nan"

Cikin tsiwa da rashin kunya Afrah tace "bazan fita ba yaya saidai kayi abinda zakayi"

"Okay bazaki fita ba?"

Afrah tace "Eh"

Bilal bulalar daya siya ya d'auko ya nuna mata k'ofa yace "get out of this Room"

Cikin tsiwa tace "bazan fita ba"

Bulalar ya watsa mata, ihu tayi tace "bazan fita ba ko zaka kasheni"

Dukanta yafarayi kota ina da Bulalar, tana ihu.

Hajiya babba wacce ta sake kunnuwa ne taji ihun Afrah, da gudu tanufi d'akin, tana zuwa taga Bilal yana dukan Afrah kamar shiya haifeta.

Cewa tayi "kai bakada hankaline? Da zaka kama yarinya kayita duka haka?"

Bilal dama haushin Hajiya babba yakeji, yasan duk iya shegen Afrah to da bakin Hajiya babba,
Bulalar ya watsa mata abaya daidai lokacin data k'araso wajensu.
Ihu Hajiya babba tafara tana Sosa bayanta, Bilal cigaba yayi da zabga mata Bulalar.

"Hajiya Babba k'ofar fita ta nufa tana k'ok'arin bud'e kofa, Bilal yabita da gudu yakara zabga mata wani, Sosa bayanta take sosai.
Da karfi tace "Bilalu bani bace, gacan Afrah a bayanka"

Bilal zabga mata Bulalar yake tsakani da Allah, da kyar Hajiya babba ta kwaci kanta, tabud'e kofar, tana fita tafad'i akasa, da rarrafe ta isa d'akinta

Bilal Jan Afrah yayi Wanda duk jikinta yayi tsami, ya wullata waje yarufe kofarshi.

"Hajiya babba tana zuwa d'aki tasa sakata,  toilet tanufa da kyar tasamu tayi fitsari, tana sauke nunfashi kamar wacce tayi wasan tsere.

Minal kwance take akan gadonta, tana tunanin Abinda yafaru tsakaninta da Bilal, tunawa tayi da yanda yake fitar da numfashi lokacin dayake kissing nata, yarrr taji ajikinta, " Auzubillahi" shine abinda tafurta.
Lumshe idonta tayi daganan bacci ya d'auketa.

_Asuba tagari_

Daddy ne ya lek'o d'akin Bilal yace "Bilal kasameni a falo"

Bilal yace "to Daddy"

Bayan Bilal yaje falon ne yaga Afrah da Hajiya babba, sai Mommy da Daddy,
Gaishe da Daddy yayi Amma Daddy yaki Amsawa saima tambayar daya bishi da ita na "Bilal meyasa ka daki mahaifiyata?"

Bilal yace "nifa daddy ban daki Hajiya babba ba, Afrah kawai na daka, itama Dan tayimin laifi ne"

"Wani irin laifi tayi maka da zakayi mata wannan dukar, kuma koba komai ai ita kanwarka ce"

Bilal yace "Daddy Afrah tana shigemin sosai, ya za'ayi ta shigomin d'aki da daddare, cikin k'ananan kaya? Kuma tasan matata bata nan, idan wani Abu yafaru laifin wa za'a gani?"

Daddy cikin Mamaki yace "Bilal? Ya akayi kasan tasa kananan kaya? Bacin kai ba gani kake ba"

Bilal jin tambayar da Daddy yamishi saida zuciyarshi tabuga, yarasa wace amsa zai bashi..

_✔ote & Comment_

Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now