page 18

357 23 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 18...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Bilal ne ya yanke shawarar sai bayan Aurensu da Afrah kafin yakaita India"

"Minal datayi sallah Addu'a kawai take Allah yasa ya yadda, da dare ta kara rok'anshi tace " yaya Bilal Dan Allah ka taimakamin"

Bilal yace "naji Amma sai bayan Aurena da Afrah, idan zaki iya jira idan kuma bazaki iya ba sai ki zauna a haka"

Minal tace "Aa yaya Bilal wallahi zan iya hakura"

Yece "dayafi miki"

_washe gari_

Madina ce tazo gidan, ta fad'awa Minal Umma batada lafiya.

"Minal dajin haka yasa ta shirya wai su tafi "

Madina tace "Aa Minal kibari idan Mijinki ya dawo ki tambayeshi idan ya baki izini sai gobe kije ki duba ta"

Minal tace "Haba Madina sai kace bakisan matsayin Umma awajena ba? Umma fa mahaifiyata ce idan banje na dubata ba waye zai dubata? Sabida Bilal bazanki zuwa duba mahaifiyata ba, kinga idan bazaki kaini ba, to bari na tafi da kaina"

Madina tace "Aa Minal kiyi hakuri, muje dama ni ina guje miki fushin mijinki ne, domin yana kawo fushin ubangiji"

Minal tace "okay nasan bakida niyan tafiya, kinga sai Anjima"

"Da sauri Madina ta riko ta tace Aa wane ni? kinga muje"

"Tafiya sukayi zuwa gidan Umma"

Minal tana Shiga tafara kiran Umma!!!
Umma ce taji muryanta sai ta tashi cikin murna ta rungume Minal.

Tace "yata sannu da zuwa"
Minal hawaye ta  share jin muryan Umma tana magana a hankali,
Tace "yawwa Umma ya jikin naki?"

"Da sauki Minal"
'Daki suka shiga Umma ta d'ebo mata ruwa tasha kafin ta tambayeta
"Minal ya naga kin rame? Me yake daminki?"

Minal tarasa me zata fad'awa Umma sai kawai tace "Am Umma nayi rashin lafiya ne acikin kwanakin nan ciwon ciki ne ya dameni, har saida aka kaini Asibiti"

"Asibiti kuma Minal? To meyasa shi mijin naki bai fad'a min ba?"

"Mijina kuma Umma?"

Umma tace "Eh kullum ai yana zuwa nan muyita hira har dare kafin ya tafi"

"Zuciyar Minal ne yabada sauti Dummm, "ta yaya Bilal zaizo gidan nan? Anya ba wani bane yake yiwa Umma karya da sunan Mijina?"

Umma tace "tunanin me kike yi Minal? Ko akwai Matsala ne? "

Minal tace "Aa Umma bawani tunani kawai de bai tab'a fad'amin yana zuwa nan ba"

"To ai ba dole bane ya fad'a miki sabida shi mutumin kirki ne yanada mutunci"

Minal tace "to Umma saidai mu godewa Allah"

Haka suka karasa firansu, Minal ta koma gida da yamma.

"Ta b'angaren Bilal kuma yana zaune a falo yana tunanin ta yaya za'ace Hafeez ya yiwa matarshi jagora? Yakaita gidansu? Da karfi ya furta "dawata akasa".

"Minal ce tafi sallama"

Bilal yace "ke? Ban hanaki Alak'a da Hafeez ba?"

A hankali tace "Hafeez kuma? Me yayi?"

"Okay tambayata ma kike?
Wato ke iskanci a jininki yake, Hafeez ne yayi miki jagora, Kun fita tunda safe shine don bakida kunya sai yanzu zaki shigo min d'aki?"

Minal tace "nifa ban gane me kake cewa ba yaya Bilal, ka fahimtar dani"

"Okay to bari in fahimtar dake, Belt ya ciro yafara zabga mata, kota ina, saida yaga tayi lilis kafin ya tsallakata tareda cewa " kuma nafasa Fitar dake kasar india, saidai kije shi Hafeez d'in ya kaiki"

"Hajiya babba da Afrah Wanda suka lab'e a bakin kofa ne sukayi saurin Baron wajen, Dad'i Afrah takeji, don Bilal ya daki Minal"

Hajiya babba tace "Dama na fad'a miki saikin cire tsoro kafin kiyi nasara, yanzu badan munyi wannan plan d'in ba ai bazai dake ta ba"

Afrah tace "wallahi Hajiya babba baki tab'a birgeni irin na yau ba, nagode miki sosai kakata kuma takwarata"

Hajiya babba tace "ba godiya yakamata kiyimin ba, yanzu zamu fara kirkiro wata munafinci, Wanda zai daina yadda da ita kwatakwata, yaji ya tsaneta".

" to hajiya ke zaki fara kawo shawara"
"Nikuma?" cewar Hajiya babba.

"Ke wai Afrah yaushe zakiyi wayo, bazaki koyi yin Abu da kanki ba? Saidai ni in yi?". To bari kiji daga yau idan baki kirkiro Wani munafincin da za'ayi ba wallahi bazan kara sa bakina a lamarinki ba".

" haba Hajiya gobe ma zan nemo"
"Dayafi miki kam".

"Minal taci kuka harta gode Allah, ita ba dukan ne ya dameta ba zarginta dayake ne yake bata haushe, wannan ai zargine"
Wanka tayi, ko mai takasa shafawa a jikinta tsabar zafi, haka ta daure ta kwanta a kasa, cikin sanyin tiles, ta rufe jikinta da Hijabinta tana tunani, har bacci b'arawo ya saceta"

"Bilal ne yashigo d'akin ya ganta kwance a k'asa, ta takure waje d'aya,
Kawar da kanshi yayi gefe yanajin kamar yayi ball da ita ko zaije sauki a ranshi"

"A zahiri mutuniyar kirki, Amma a bad'ini tafi kowa iskanci, maimakon taji da wannan nakasar Amma tana kara sab'awa Allah chewwww"
Tsallakata yayi yaje ya kwanta yaja bargo.

"Minal ce tafarka cikin dare da zazzab'i me zafi, jikinta har rawan sanyi yake, sanyin tiles d'in ne ya dameta har yakawo mata zazzab'i, tashi tayi cikin rawar sanyi tahau gadon tareda janye bargon Bilal ta lullub'a jikinta dashi"

_Asuba tagari_

Bilal ne yafara bud'e idonshi jin sanyi yayi mishi yawa, sai ganin Minal yayi ta kwanta a kan gadon tana bacci jikinta lullub'e da bargonshi, "ke? Ke? Tashi Dan Ubanki, Ubanki ne yasiya gadon? Shiru yaji babu amsa, ke ba tambayarki nake ba? Shiru har yanzu ba Amsa, bubbugata yayi, yaji batayi magana ba, zuwa yanzu yad'an fara tsorata, hannunta ya d'aga yaga yafad'i, a tsorace yafara bubbugata yana kiran sunanta, Minal!!! Minal!!! Ke? Ke?, har yanzu shiru"

Fita yayi da sauri yaje d'akin Daddy,
Sallama yayi a rud'e.

Yashiga yace "Daddy Minal ta mutu,"

what? Minal kuma ta mutu? Wani irin magana kake?

Kuyi hakuri yau ina busy ne shiyasa banyi typing dayawa ba

✔ote & comment

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now