Page 6

377 25 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

(An heart touching story)

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_

  *WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

 
  *Page* 6

"Mutane sun taru makil akofar gidan Alhaji Umar shikuma Bilal ganin haka yasan da haɗin bakin nakusa dashi awannan lamarin kuma yanada tabbacin idonshi suke nema su ɓata,  daidai lokacin motar Alhaji Umar yadanno kai cikin gidan,  dasauri yafito amotar yana tambaya meyafaru? Wanine acikinsu yace ranka shidaɗe wasu mutanene suka shigo gidannan suka watsawa Bilal Acid a ido,  Acid!!!  Cewar Alhaji Umar, garin yaya haka tafaru? Wani mara mutuncinne yashigo har cikin gidana yawatsawa ɗana Acid a ido?  Lalle kuwa sai hukuma sun shigo lamarinnan saina kulle duk wani wanda yakeda sahanu,  haka Alhaji Umar yayita matsifa kamar dagaske Amma acikin zuciyarshi wani irin daɗi yakeji, 
Karasawa inda Bilal yake yayi yana zuwa yafashe da kuka yace yanzu Bilal shikenan sun makantar min dakai?  Yanzu baka ganin kowa?  Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un,
Bilal yanajin maganar Daddy  abun yabashi mamaki matuka, ganin haka yasashi cewa Eh wallahi Daddy haka Allah yakaddara min zan kare rayuwana amakanta  yanzu idaduna basa ganin komai,  Bilal yafaɗi haka yana me hawaye,  idan kaga yanda Bilal yake acting zakace da gaskene yataɓa idonshi amma shi azuciyarshi yasa kudirin saiyayi bincike alamarin,
Suna cikin wannan halinne saiga Latif yana zuwa yafara tambayar meyafaru?  Daddy ne yayi mishi bayanin komai,  shiru Latif yayi sannan yace yanzu Bilal baka ganin komai?  Bilal yace Latif bana ganin komai kutaimaka ku kaini ɗakina,  latif ne yace wallahi saina gano duk waɗanda sukayi maka wannan aika-aikar  koda kuwa zan rasa raina ne,
Jin haka yasa zuciyar Daddy tabada wani sauti Dummm yasan idan bincike yayi bincike dolene aganoshi"

"wani irin kallo Daddy yake yiwa Latif,  hannun Bilal Latif yarike  domin kaishi ɗaki,  mutane sunata Allah wadai da wanda suka aikata mishi haka".

"Minal damai mashin kuwa asibiti suka nufa,  suna zuwa aka nunawa me mashin ɗakin dazasu samu babban likita, Hannunta me mashin yake rikewa suna tafiya har suka iso office na babban Doctor"

Bubbuga kofar me mashin ɗin yayi daga ciki akace "yes coming"
Shiga sukayi ciki wani bakin mutum ne me jikin gaske yake zaune akan kujeran doctor.

"Meke tafe daku? 
Yallaɓai wasu mutanene suka watsa mata Acid A ido shine nace bari nakawo ta aduba karya zame mata matsala,
Shiru doctor yayi yazubawa Minal namujiya can yacewa me Napep ɗin wannan fine girl ɗin aka watsawa Acid a ido?  Kai gaskiya banji daɗi ba amma ɗan fita kabamu waje mana"

Fita me mashin yayi a office ɗin wanda har zuciyarshi be kawo komai ba.

Tashi doctor yayi awajen zamanshi yaje dab da Minal yazauna,  Minal kawai sai jin hannun mutum tayi yarike hannunta,  saurin janye hannunta tayi tace "Malam me haka?"

Haba 'yan mata yanda kike dakyau ai dolene in kosa,  yanzu nasan bakya kallon komai Right?
Minal tace eh sai me?

"Relax Baby bawani sabon abu bane awajen 'yan matan zamani ace tana harka dame kuɗi kinsan zata huta,  zan taimaka miki idan har zaki bani haɗin kai sannan babu wanda zesan abu haka yafaru tsakaninmu...."

"Tashi Minal tayi dasauri tace haba doctor, kaida mukazo kadubani amma zaka tsaya kanamin maganar banza?  Hakika da ina ganinka babu abunda ze hanani tsinka maka mari mugu azzalimi..." kafin takarasa taji ya rike hijabinta yana kokarin cirewa".

Kokawa suka fara dashi aɗakin tana kokarin janye hijabinta shikuma yana cirewa,  rokanshi Allah da Annabi tafara akan yabarta amma ina sam sam mutumin bashida Imani. Ganin yanason cire mata kayanta yasa tafara ihu tana kiran "Me mashin!!!  "Me mashin!!!

Toshe bakinta yayi da hannunshi daidai lokacin me mashin ɗin yabuɗe kofar dasauri,  saurin sakinta doctorn yayi yaja dabaya.

Me mashin ne yace Doctor menake gani haka?  Me kake kokarin aikatawa?

"Shiru doctor yayi yafara kame kame amm.. Amm..  Dama idontan nakeson dubawa amma taki yadda..."

"Kaji tsoron Allah Doctor kaji tsoron ranar haɗuwarka dashi,  kana tsoran mutum amma baka tsoron Allah?  FYAƊE fa kakeson kayimin, bakaji kunyar Allah ba kanajin kunyar mutum?  Allah ya isa,  bazan yafe maka ba,  abunda kayimin Allah yasa ayiwa 'yarka,
me mashin kataimaka kakaini gida dama nasani rayuwata tana cikin haɗari,  babu masu taimako dan Allah saidan wani abu dazasu samu ajikinka,  Allah ya isa"

Dama ai Allah isashe ne kufita kubar asibitinnan kafin nakira muku security.

"Hannun Minal me mashin ɗin yakama sukabar office ɗin,
Ya tambayi Minal inane unguwarku?  Tace bayan kasuwa"

Me mashinne yataimakawa Minal yakaita har gida kafin yatafi, 
Lokacin dataje gida Umma bata dawo ba haka tazauna a inda take tayi ta razgan kuka.

"Wannan wace irin rayuwace?  Yanzu irin talauci da kuncin rayuwar damuke ciki ace wannan kaddarar tasake afkuwa"

Waze taimaka miki Minal?
Kin cuci kanki,  kin ɓata rayuwarki akan wanda besan dazamanki ba, wanda yatsaneki,  Duk maganar nan tanayi ne azuciyarta yayinda take kuka kamar hawayenta ze kare.

"Tana cikin kukane taji sallaman Umma,  Saurin share hawayenta tayi domin batason Umma tasan abunda yake faruwa,  Aa Minal meyafaru naga kin zauna shiru haka?  Keda nagi zaton kina gidansu Madina,  meyafaru?
Shiru Minal tayi tana kokarin maida hawayen dasuka taru a idonta.
Wai me yake faruwane Minal?
Umma bana ganin komai!!! "

Bakya ganin komai kamar yaya?  Ban ganeba kiyimin bayani dalla-dalla in fahimta.

"Hawayen dasuka taru a idon Minal ne suka wanke mata fuska,  Ahankali tabuɗe bakinta kamar batasonyin magana tace Umma Acid aka watsamin a ido,
Acid!!!?  Garin yaya?  Suwaye suka watsa miki?  Ki amsamin suwaye??
Firgita Minal tayi da yanayin maganar Umma"

Bazaki faɗamin ba Minal ina kikaje?
Umma Dama ina zuwa gidansu Madina ne shine wasu samarai suka watsamin Acid takarashe maganar tana kuka sosai.

Ba kuka na tambayeki ba Minal amsa nakeson kibani ina kikaje yau?

Umma wallahi gaskiya nafaɗa miki ki yadda dani, cewar Minal
Ok bazaki faɗi gaskiya ba kenan?
Umma gaskiya nafaɗa miki....  Tassss kakeji Umma tawanke Minal da mari Bazaki fafamin gaskiya ba Minal yanzu kinzama makauniya wace irin rayuwa kikeson muyi?  Nashiga Uku ni Maryama.
Kuka Umma tafara itama an rasa me lallashin wani.
Ta rungume Minal suna kukan bakin ciki.

"Ɗaki Latif yakai Bilal zaunar dashi yayi akan gado yace Bilal kaɗauki kaddara aduk yanda yazo maka alkhairi ko sharri,  karkasa komai aranka insha Allah zaka fita daga wannan rayuwar,  ba karamar jarabawa bace ace mutum yanada ido ada amma yanzu babu,  saika daure kakai zuciyark da nisa kafin kaci wannan jarabawar.
Haka Latif yayita kwantarwa Bilal hankali"

Daddy kuwa yau babu wanda yakaishi farin ciki jiyake kamar yahaɗa party till down,  waya yaciro yakira Alhaji Nura yace "Alhaji Nura aiki yayi kyau zaka samu babban kyauta daga gareni,  saidai fa akwai matsala!"

Matsalar me kuma Alhaji  Umar?
Latif zaibi diddigin abinda yafaru sabida yace koda zai rasa rayuwarshi saiya gano wanda ya aikatawa Bilal haka.

"Haba Alhaji Umar akan wannan shine zaka ɗaga hankalinka?  Nawa Bilal yake balle Latif?
Idan bazaka damu ba muhaɗu a guesthouse nawa mana Cewar Alhaji Umar,
Ok ba matsala zanzo da karfe bakwai nasafe.
Nan suka gama shawararsu suka kashe wayar...

_✔ote Comment & share_

✍🏻  *JIDDAH S MAPI*

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now