Page 2

586 29 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwane ga yayata Maryam S Mapi_

  *WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

   *Page* 2

"Minal tafiya take tana hawaye yanzu idan naje gida mezan faɗawa Umma na?  Gashi yau ko abincin dazamuci babu, wannan mutumin yacuce ni,  dana sani ma dana karɓi kuɗin wannan Latif ɗin,  to Amma idan Ummana tagani mezan ce mata?  Ita kaɗai taketa maganar,  tana cikin tunani taga wani me keke saura kaɗan ya bugeta,  da gudu tamatsa awajen,  me keken ne yace ke wace irin wawiya ce?  Ana tamiki magana kin share mutane kina tafiya yanzu idan nakaɗeki saiki janyo min matsala wawiyar banza,
Minal ganin yanata zaginta acikin mutane yana mata ihu yasa tace mishi  Malam bana matsa maka ba?  Yazaka tsaya kanamin ihu?  Nifa ba 'yarka bace ba tamm,  yace ko zaki dake nine?  Matsiyaciyar banza kazama,   ran Minal ne yaɓaci tace niba matsiyaciya bace,  yace se waye?  Tace sai kai... Ai kuwa kafin takarasa ya sauko akan keken yaɗaga hannu zai sauke mata mari wani mutum daga gefe yarike hanunshi yace haba bawan Allah tunda ta matsa ba shikenan ba? 
Ke kuma kina mace zaki tsaya kina faɗa da namiji a titi?
Minal ce wanda tuni idonta yafara kawo ruwa tace Baba tinani nake shiyasa yayi tamin magana banji shi ba Amma tinda namatsa ai sai yayi min uzuri.
Mutumin ne yace to yanzu dai kowa yayi hakuri,   Minal ce tajuya tayi tafoyarta tana me share hawayenta.
Azuciyarta tace nikam banida farin jini awajen kowa,   haka harta isa gida,
Tana shiga gida Umma tace Meya dawo dake Minal?  Hala kin manta yaji ko nasanki da mantuwa,   Minal ce tafara kuka zuciyarta tana mata raɗaɗi,   Umma tace haba Minal meyasa kike kuka?  Koso kike nima in fara kuka ne?  Minal tace Aa Umma dama Faɗuwa nayi damuke tafiya shine alalan ya zube,
Umma tace to dan Alale yazube shine zakiyi kuka?  Wanima arana ɗaya yake rasa gidanshi da dukiyar shikuma wancan ya zeyi? Indai akan wannan ne kidaina kuka Allah yasan damu kinji ko?  Minal tagiɗa kai"

_Washe gari_

"Minal ce tafita da Alalenta taje gidansu Madina sun fito tare,  ahanya Minal take cewa Madina nifa inajin kamar in canza wajen saida alale Dan Ummana batasan meyake faruwa ba! Datasani bazata barni naci gaba da saidawa anan wajen ba.  Madinace tace Aa Minal karki faɗa mata kici gaba dakai abunki karki kulashi kinji?
Minal tace tom amma bazan iya daure wulaƙancin shi ba,
Madina tace idan bakya kulashi zai daina.

Shikuma Bilal idan yatuna abinda wannan ƙazamar yarinyan tafaɗa mishi sai yaji kamar yakashe kanshi,
Kwance yake akan makeken gadonshi ya lulluɓa jikinshi da bargo me taushi, jiyake yau kamar kada yaje din bayason ganin yarinyan ko kaɗan.

Knocking na kofarshi aka fara,  ahankali yace Who is that?   Ba'a tsaya da buga kofarba yasake cewa i say who is that?
Muryan mace ne tace "Afrah ce"
Yace me kikazo yi?
Tace "Mom ce tace nazo naduba ka sabida yau kofita bakai ba"
Yace shine inyi miki me yanzu?
Tace "kabuɗe inason inga lafiyarka hankalina yakasa kwanciya"
Wani takici ne yakamashi yanzu yaji da abinda yake damunshi ne ko yaji da nacin Afrah?
Shifa gaskiya yarinyan tafara isanshi dolene yaɗau mataki akanta,  can daga bakin kofan naji tasake cewa "wallahi idan baka buɗe naganka ba zan iya mutuwa"
Bilal ne yaji kamar yarufe idonshi yaganshi a lahira tsabar takaici.

Tashi yayi yaje bakin kofar yabuɗe mata,
Wata yarinya ce wanda zatakai shekara 22 naganta sanye da dogon riga roba roba kanta ba ɗankwali tayi kitson attach kamar ba gobe,  farace ita amma ba sosai ba,  idonta tayi fixing na eyelashes dogo dogo,  tanada jiki kaɗan,  rigan jikinta yakamata sosai,  tauna cingum take yana kara kass kass kass,  tsaya Bilal yayi yana kallonta.

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now