page 11

383 19 2
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi
*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Page 11

Alhaji Nura yayi matukar farin ciki da Umma suka amince mishi, yana fita yakira Daddy awaya yafad'a mishi duk yanda sukayi tareda cewa saidai fa Alhaji sunce sai kazo dakanka, haba Dan Allah ni meze kaini bayan kasuwa anguwanda ko mai gadina bazai zauna acan ba bale inje wai Neman Aure kaidai kawai kugama Idan yasoma kace musu Kaine Uban yaron dukba matsalana bane,
Aa Alhaji dolenefa saika sauke girman kai kafin kasamu abinda kakeso Awajen yaronnan ai Idan kazo dakanka darajarka zai karu a idonshi, dakyar Daddy ya yadda akan zaizo, to naji bani adreshin su, ai wannan babu wani adreshi bayan kasuwa kawai senta har kofar gidansu, cikin kosawa Daddy yace baga irinta ba, ace yaro bayajin magana, gashi zaiyi aure agidanda ko adreshi babu kuma Makauniya, kai Allah yawadaran.
Kashe wayar yayi yatafi d'akin Bilal tareda yin excuse, yana shiga yaga Sabir zaune agefen Bilal yana duba wasu takaddu, Direct b'angaren Sabir yawuce, Sabir me kakeyi da takaddu batareda sanina ba?
Am Daddy ai nina sashi yamin sign Takaddun wasu company ne dasuka kawo mana kwangila....haba Bilal meyasa bazaka aikamin ni nayi sign d'inba?
Daddy ai sign bawani matsala bace Sabir ma zai iya, shiru Daddy yayi daga bisani yace "dama maganar Aurenkane yakawoni an samo yarinyar dazaka Aura yanzu ahakama gidansu zani muje ad'aura Auren Idan yaso daga baya saita tare koba hakaba?
Aa Daddy ba maganar tarewa daga baya kawai Idan an d'aura yau to akawota yau...Bilal meyasa kafiye taurin kaine? Daddy kayi hakuri idana Dalili, bakada Dalili Bilal illa ka kuntatawa Afrah, bara nafad'a maka babu wacce tafi Afrah awajenka sabida ita 'yar uwarkace ta jini, yana gama fad'in haka yafice ad'akin azuciye,
Sabir ne yajuyo yana fuskantar Bilal yace haba Bilal meyasa bazaka bishi yanda yakeso ba, Sabir babu ruwanka tsakanina da Daddy sai Allah yanzu zakaga mun shirya mun dawo normal, dariya Sabir yayi yace hakanefa kuma kunfi Kusa, yawwa gara daka sani"

Minal yau tana cikin farin ciki, azuciyarta tace nakusa warkewa? Idona yakusa fara gani? Wayyo Allah na dad'i kasheni, ai Idan nayi Auren nan nadaina Fad'a nadaina Neman tsokana insha Allahu duk abinda akacemin inyi bazan tab'ayin delay ba tinda zasu warkar min da idona, ganin irin farin cikin datake cikine yasa Umma Amincewa da ayi Auren yau,
Madina ce tashigo gidan da gudu tashige d'akin Minal, tana shiga tace "Minal wai dagaske kina Aure kuma yau?"
Murmushi Minal tayi Wanda yabayyana dimples nata tace Eh Madina yanzuma an tafi d'aurawa waya fad'a miki?
Daga wajen Isa me rake nake yace wai tinda an yaudareshi to mubiya mishi reken dayayi tabamu koya kai kara.. Idan yafasa kai karan ba'a yanka mishi ragon suna ba,
Ke kinsan Isa da fad'a fa, Aa karene shi. Kinga abar maganar nan yanzu wa kike Aura?
Nima ban sanshi ba! What? Baki sanshi ba? Kinada hankali kuwa? Kwarai kuwa inada shi hasalima nafiki hankali zasu kaini kasar wajefa agyara idona...Minal bakida hankali wallahi Amma Umma tasani? Madina kidaina cewa banida hankali hasalima Idan kika kara nuna bakya son Auren nan kece babbar makiyata, Minal karki tafka Kuskure arayuwarki,
Madina zaki iya tafiya Idan shine abinda yakawoki Idan kuma kud'in Isa me rakene ya ajiyeki kije kice mishi bazan bada ba, yanda take maganan zakace wata jarumace,
Allah yahuci zuciyarki, Ameen Cewar Minal"

Bayan sallar Azahar aka d'aura Auren Minal da Bilal akan sadaki dubu d'ari,
Da mangariba su Afrah ne da hajiya Salamatu sukazo d'aukan Amarya da gayya Afrah tace zata bisu domin tinda safe taketa ruzgan kuka, suna zuwa lokacin Umma tagama yiwa Minal fad'a da nasiha, Minal kinga halin damuke ciki kuma nasan halinki, inason kimin alkawarin zakibi dangin mijinki da mijinki sahu da k'afa duk abinda zasuyi miki karki rama kuma karki rike azuciyarki kinga da ace Ina rike abinda dangin mahaifinki sukayimin da yanzu bana raye da bakin ciki yakasheni......ina Makauniya takene? Tin d'azufa muke jiran afito da ita, muryan Hajiya Babba ne yake magana,
Umma atake taji zuciyarta ta tsinka, Amaikon suce mata Amarya sai suce makauniya?
To Allah dai yakyauta,
Tashi muje Minal, to Umma Minal tafad'a tana kukan rabuwa da mahaifiyarta itama Umma dauriyane kawai Idan bahakaba tafi Minal shiga damuwa.
Suna Fita cikin gida suka hango Afrah tayi kitson Attach har baya, tasa wani dogon Riga d'amamme kanta ba d'ankwali tana taunar cingom sai kallon mutane sama da kasa take,
Hajiya babba kuma an rike kwankwaso kamar afilin dambe suke, Ummace takarasa da Minal tace sannunku dazuwa Hajiya..dakata bashi yakawomu ba, Ina Makauniyar? Shiru Umma tayi Kafun tanuna musu Minal gatanan, kinga malama ba Aljana mukace kinuna manaba makauniya mukace kibamu cewar Afrah,
Itace makauniyar bakiga sanda ahanunta ba?
Da sauri Afrah taja da baya ganin wata kyakkyawar yarinya rik'e da sandar makafai Idan kaganta zaka rantse ba makauniya bace,
Murmushi Minal tayi cikin siririyar muryanta me sanyi tace ina wuninku?
Dabamu wuniba Aida bakiji zuwanmu ba kiwuce mutafi malama cewar Hajiya Babba,
Allah yakiyaye hanya Minal Umma tafad'a tana kuka,
Hawaye Minal tashare tace to Umma kikula da kanki,
Dama kunsan kuna sonta kuka sayar da ita kwad'ayayyun banza,
Minal kuka kawai takeyi na rabuwa da Ummanta, ke kirufe mana baki kinsan kinason gidanku kikace zaki Auri d'anmu? Madina ce tazo dasauri tace Minal Ummace tace narakaki gobe sai indawo, To waya hanaki binmu gidanmu ai akwai abinci cewar Afrah,
Shiru Madina tayi tana tunanin wani irin rayuwa Minal zatayi tareda wad'annan mutanen? Allah dai yakyauta.

Sai bayan mangariba suka shigo G.R.A Madina sai ware idanu take tana kallon manyan gidaje, Daidai wani Babban gida Madina taga anyi parking sai lek'awa take tajikin window, Horn driver yayi megadi yazo ya bud'e musu suka kutsa cikin gidan.
Madina sai kallon cikin gidan take azuciyarta tace "Minal Allah yasa nan gidan zamanki ne"
Shiga cikin gidan sukayi har zuwa wani babban falo me d'auke da Kayan Alatu, kujerun d'akin kamar na sarauta suna shiga ciki Hajiya Babba tajuya takalli Madina tareda cewa saiki kaita d'akinshi tabaya yake, Idan kun b'ata Allah yasa ku gane hanya mukam munada abinyi ko Afrah ta?
Haba Hajiya Babba yazakice suje d'akin yaya kinsan fa ni kad'ai yakeso kuma Idan sunje  Koran kare zeyi musu kigan jikinsu mana very dirty,
Aa Afrah barsu suje ai ba ganinsu zaiyi ba,
Ke Aljana kitsaya a iya matsayinki karki wuce gona da iri acikin gidannan don gidan masu kud'ine Idan bakya gani kawarki tana gani zata fad'a miki, kazaman banza matsiyata, tana matsifa taja hannun Afrah sukayi d'akinsu.

"Minal wannan wani irin rayuwane? Anya zaki iya zaman gidannan? Tabd'i wallahi saina fad'awa Umma yanda sukayi mana...Aa Madina Dan Allah karki fad'a mata mutanennan zasu kaini kasar turawa agyara idona kiyi hakuri madina kinji?
Shikenan tinda kin zab'i wulak'anci akan Gata Allah yasa hakan yafi Alkhairi, Ameen Madina, Yanzu ina zamu farabi Minal bansan ko inaba gidan yayi girma dayawa, kibari kawai muzauna anan Allah zai kawo Wanda ze nuna mana,"
Haka suka zauna cikin falon har bayan isha babu Wanda ya tanka musu ga yunwa ga ishi Minal harta fara gyangyad'i saiga Hafeez yashigo falon Madina ce ta tashi ta sunkuya har kasa Ina wuni?
Harara Hafeez ya bank'a mata meye hakan 'yanmata?  Am.. Am Dama d'akin Wanda yayi Auren mukeson kanuna mana,
Chewww Idan kunbi senta karku tsiya zakuga d'akin, yana fad'in haka yabar wajen yana dariya.
Madina ranta yafara b'aci wannan wani irin wulak'anci ne?
Minal nifa zan tafi gida bazan iya jure wulak'anci ba.
Kiyi hakuri madina Idan kin tafi dawa zan zauna? Kiyi hakuri kawata.
Suna zaune harsun fara bacci Sabir yashigo yaga mutane kwance akasa ga sanyin tyles bubbuga Jikin bango yayi yana tashinsu, Da Saudi suka mike atare yace "lafiya 'yanmata kukayi kwanciyarku akasa,
Minal ce Wanda fuskarta ya kwab'e da janbaki tafara kuka tace, Nice Amaryan da akamin Aure da d'an gidannan,
Cikin mamaki yake kallonta to amma meyasa suka barku anan? Kuma ai shi makauniya ya Aura,
Nima MAKAUNIYA CE bakaga sandata ba?
Shiru Sabir yayi yana kallonta gata kyakkyawa kamar India kuma idonta babu alamar ciwo, to Untyna muje nakaiku kidaina kuka kinji untyna?
Share hawayenta tayi tace to mungode, D'akin Bilal yakaisu ya Ajesu afalo kuzauna anan bari nakawo muku Abinci ko Untyna? Minal tace to mungode, Aa kidaina godiya kefa untynace kinji Amaryan yayana? Rufe fuskarta tayi tana dariya"

Wai hayaniyar me nakejine Sabir? Muryan Bilal ne sukajiyo acikin falon, da sauri Minal tamike jin muryan Wanda tafi kowa tsanarsa aduniya Wanda sanadiyyarshi tazama makauniya Mara galihu,
Shima tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, wannan yarinyan me kamada Aljanun kuma me takeyi agidannan?
Yakuma naganta da Sanda? kaddai itace Daddy ya Auromin? To ai idanunta lafiya suke, shikenan na d'ibo ruwan dafa kaina, yana cikin tunanin yaji tace "kamar muryan Bilal nakeji? Saura kad'an yace "mata eh saime?....amma bayason asirinshi yatonu, Madina ce tace eh Minal shi kika Aura shima naganshi da Sanda,
Minal tace Allah shikara ai daba makaho yazama ba da gurgu ne mugu kawai,
Bilal ranshi yab'aci yace " ke karkimin rashin kunya zanci Ubanki Idan kika rainani danasan ke za'a Auramin da saidai inmutu ba Aure k'azamar banza....haba yaya? Aina Kasansu dahar zaku fara fad'a kaida bagani kakeba? Cewar Sabir Wanda yashigo da Plates na Abinci guda biyu ahannunshi,
Kame-kame Bilal yafara Am..Amm Dama naji suna hirane kuma ina bacci shiyasa nake musu fad'a, yaya ai  dakasansu dako tsawa bazakayi musu ba kawar Amaryace da Amarya, yafad'a yana murmushi,
Bilal ne yafara magana azuciyarshi shikenan nashiga uku na cuci kaina.
Wannan me kamada Aljanarce mamata, wayyo Allah ya zanyi? Anya bazan janye Aurennan ba?

(Nikuma nace waya fad'a maka ana janye Aure Bilal?)

✔ote & Comment

Jiddah S Mapi✍🏻

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now