page 40

403 18 3
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Page 40...

  By
Jiddah S Mapi

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio

  ~had'a kayanshi yayi ko kallon inda Latif yake bai kara ba, yana gamawa ya Ciro waya ya sanarwa manager cewa kwana biyu bazai zo company ba, Latif da kallo yake kawai yake binshi, shi abun har mamaki yake bashi wai ace Bilal ne ya rud'e akan soyayya haka? "To Allah dai ya kyauta"

   "Amma Baby kina ganin karatu da cikin nan zaiyi kuwa?" Minal tafad'a cikin hawaye azuciyarta kuma tanajin Bakin cikin abinda Bilal yayi mata, Baby ce ta share mata hawayen tace "mata nawa suke karatu da ciki? Mata sunfi dubu, meyasa zaki tada hankalinki? Kowa da nashi kaddarar ki godewa Allah daya kawo miki naki ahaka"
Minal rungume Baby tayi tana kuka, Baby bubbuga bayanta take alamar rarrashi, suna cikin haka mommy tayi sallama, ganin yanayinsu ba karamin tausayin Minal taji ba, itama karasawa tayi ta rungumesu duka tana rarrashinsu, saida taga Minal ta daina kuka kafin ta saketa, tace "Daddynku ne yace nakiraku"
Mikewa sukayi dukansu sukabi bayan Mommy, suna zuwa babban falo Minal da Baby suka zauna a kasa inda Mommy kuma ta zauna agefen Daddy, gyaran murya yayi yace.

    "Am Minal? Naji sakon da kika tura Baby tafad'amin kuma naji dad'i da kikace kinason karatu, to Amma raina yayi matukar b'aci da ke bakizo da kanki kika fad'amin ba, daidai da rana d'aya ban tab'a d'aukanki bare agidannan ba, dake da Baby duk 'ya'yan cikina na d'aukeku bakuda bambanci awajena, daga yau idan kina bukatar Abu kizo da kanki ki tambayeni karkiji tsoro, nima Uba nake awajenki kinji?"

   "Insha Allah Daddy zanyi yadda kace nagode da kulawan da kuka bani, Allah ya biyaku da gidan Aljanna"
Tafad'a tana goge hawayenta da gefen d'ankwalinta.

   Daddy yace "Ameen, to kuma akwai wata Alfarma danakeso awajenki, inason kifad'amin gaskiya idan kinaso ko bakya so, inason in had'aku Aure da Hamma Yarda, Wanda asalin sunanshi Abubakar, jikan Innace wacce mukaje wurinta a yola, mahaifinshi ya rasu sanadiyyar cutar Hanta data dameshi, an kaishi kasashe da Dama Amma ba'a dace ba daga baya sai mutuwa da yayi, Abubakar takwaran Mijin Inna ce, anace mishi Hamma Yarda ne sabida takwaran baban babanshine, yayi karatu secondary anan gida Nigeria, sannan yayi University a kasar England, kasancewar yayi karatu a kasar turai hakan bai hanashi riko da addininshi kem kem ba, na yadda da tarbiyyarki sannan na yadda da tarbiyyar Hamma Yarda, na tabbata idan kika Aureshi zakiji dad'i, Za'a bar Auren saikin haihu tukun"

   Wasu hawaye masu d'umi ne suka fara bin kuncin Minal, zuciyarta sai dukan Tara Tara take, tarasa ta ina zata fara yiwa Daddy bayanin tanada Aure, gashi sun nuna mata so bana wasa ba, Mommy ce ta katseta tace "Minal idan har bakya son Hamma Yarda kifito ki fad'a mana mu bazamuyi doleba"
Minal dukar da kanta tayi cikin jin kunyar karyar datayi musu abaya, cikin kuka me tsuma zuciya ta bud'e bani da kyar tana har hard'e zance tace

   "Ku gafarceni Mommy da Daddy da Baby nayi muku karya tin rana ta farko da kuka bugeni da mota, banyi Dan ra'ayina ba, nayine don in tsere daga sharrin Mijina.....kukane ya kubce mata, tashiga yi ba tsayawa.
Mommy ce ta taso daga kan kujera ta riko Minal tace "me kikeyi haka Daughter? Idan bakya sonshi ai babu dole"
Minal juyawa tayi tana fuskantar Bedroom sabida batason had'a ido dasu, sakamakon karyar datayi musu, tana kuka tace "Mommy inada Aure, kuma ba soyayya mukeyi da Hamma Yarda ba, soyayyan da mukeyi ta 'yan uwantaka ne a matsayinmu na musulmai, kuma na d'auki Hamma Yarda kamar yayana ne yanda Baby ta d'aukeshi, ya zan Baku labarin Mugun Mijin Dana Aura Wanda yayi sanadiyyar makancewata daga baya ya wulakanta ni, babu abinda yake b'atamin rai kamar idan na tuna ranar Aurena da aka kaini gidan mijina, a kasan tyles cikin sanyin AC muka kwanta nida kawata" share hawayenta tayi taci gaba da basu labarin irin wahalar datasha sanadiyyar Mijinta, Abu biyune ta b'oye musu shine Sunan Bilal da kuma sunan Daddyn Bilal.

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now