page 35

393 21 3
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 35...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Abuja zone 2 shine unguwar su baby, wani Babban gida me kyaun gaske aka driver ya tsaya yayi horn, me gadi ne yazo da gudu ya bud'e musu yana d'aga hannu yace " barkanku da dawowa"
Suma d'aga mishi hannu sukayi kowanne fuskarshi d'auke da murmushi, parking yayi a parking space, duk suka fito kowa yanajin dad'in yadawo kasarshi, Baby ce tariko hannun Minal tace "muje mu huta a d'akinmu ko"
Minal batace komaiba tafara binta, Minal dataga kyaun gidan a zuciyarta tace "tabd'i Ina ganin gidansu Afrah kamar Aljanna, Amma na tabbata idan Afrah tazo gidannan saita raina kanta"
Wani babban falo ne me d'auke da lemon green and White colour suka shiga, cikin show glass d'in akwai wani Abu me yalk'i Wanda ya k'awata d'akin, da kwalaben turare kalala, gefe kuma wani zungureren TV ne a kunne, mutanen cikin TV d'in kamar zasu fito tsabar girman Tivin, Chinese carpet lemon green da fari ne a shimfid'e a kasa, sai wasu luntsuma luntsuman kujeru set, (tsaya a lissafa kayan falon da kyaun gidan b'ata lokacine)".

Baby ganin Minal tana bin ko ina da ido yasa taja hannunta tace "muje d'akinmu muyi wanka Dan nifa na gaji sosai"
Minal tayi murmushi tace "raguwa kawai"
Jan hannunta kawai tayi zuwa d'akinta,
Minal ganin d'akin Baby yasa ta saki baki tana kallon ikon Allah, wani gado pink and white colour ne acikin d'akin, Teddy's kamar na siyarwa, sai wardrobe bango to bango, da wasu manya manyan kujeru guda biyu gefen gadon, sai bedroom freezer, Wanda aka cikashi da drinks da kayan d'anye irinsu Ayaba, Apple, lemo, kankana, babu Wanda babu.

Minal a fili tace "ya Allah Kaine kayi masu kud'i, kayi talakawa, kayi wasu da lafiya wasu kuma babu lafiya, wani me kud'in ysnada lafiya wani kuma ga kud'i ba lafiya, wani talakan yanada lafiya amma bashida ko sisi, wani talakan bashida lafiya kuma bashida ko sisi, wani me kud'in yayi kyauta ya taimakawa mutane, wani me kud'in ya wulak'anta Wanda basu dashi, wani talakan kayishi da zuciya wani talakan kayishi babu zuciya, Ya Allah kada ka bamu kud'i Wanda zai hallakar damu, ya Allah kabamu kud'i Wanda zai amfanemu duniya da lahira, takarashe maganar tana kuka, tunawa datayi da mahaifinta Wanda sanadin dukiya aka kasheshi.....Baby ce ta katseta ta hanyar rungumarta itama tana kuka tace  " hakika kin fad'i gaskiya Minal, dazan baki labarinmu dasai kin tausaya mana, Amma Daddy ya hanani maimata abinta ya wuce, banason in tuna baya ko kad'an natsani dukiya Minal....." Da sauri tashare hawayenta tace "kije kiyi wanka, nikam sai nayi waya da Yaya Mujahid nawa, Dan har yanzu baisan na dawo ba, Minal toilet ta nufa bata kara magana ba.

Bilal yana bacci acikin jirgi, Saida akayi Kusan 30mins da sauka su kuma pilot d'in babu Wanda ya tasheshi, Saida ya farka dan kanshi kafin yasan sun iso, da sauri ya tashi yad'auki kayanshi, motar Gombe ya kama yasa kayanshi aciki, Sun d'au hanya ne yasa hannu a aljihu zai d'au wayarshi yaci karo da wata takadda, baiyi gigin bud'ewa ba sabida yanayin dayake ciki, ganin takaddar karamace ba wata babba ba yasan babu wani Amfani, can gefe ya wurga takaddar, bai kara ko kallo ba, 4:30 na yamma suka iso Gombe, da sauri ya fita a motar burinshi kawai ya iso gidansu Minal, har ya fita a motar yaga wata mata data zauna a gefenshi tad'au takaddar da yasar tana karantawa, ranshi a b'ace ya warce takaddar ya mayar Aljihunshi, "wannan ai rainin wayone ya zan yasar da takadda ta d'auka ta karanta?".

Unguwar su Minal direct ya nufa yanata Addu'an Allah yasa ta dawo, daidai kofar gidansu yaji zuciyarshi tana tsinkewa, tsayawa yayi yakasa shiga gidan, wata zuciyar tace mishi " yanzu idan ka shiga bata dawo bafa ya zakayi?"

Wata zuciyar kuma tace "to idan baka shigaba ya zakasan ta dawo ko bata dawo ba?"

"Runtse idonshi yayi, ya daure yayi sallama"

Cikin gida kuma Umma tana zaune ta rabka tagumi kamar kullum tana tunani, taji sallama a kofar gida, da sauri ta Amsa ta d'auko hijabinta tasa a zuciyarta tace "Allah yasa an samu Minal ne".

Tana lek'awa tace " wayene?"

Bilal ne yayi shiru,
Umma tad'an fita kad'an lokacin Bilal ya d'ago fuskarshi, Ummace ta zabga mishi wata muguwar harara cikin b'acin rai tace "lafiya? Me kazoyi? Bawan Allah tun kafin na kira maka yara suyi maka duka ka b'acemin dagani, banason ganinka na tsaneka, sanadiyyarka 'Yaya ta makance, kuma sanadiyyarka rayuwarmu ta lalace babu ita babu dalilinta, Allah ya isa tsakanina dakai"

Bilal kasa ya durkusa yace "Umma ki yafeni na Tuba nabi Allah, wallahi inason Minal, tsakani da Allah....."dakata malam ka tashi kabar kofarnan, kafin natara maka yara".

Cikin sanyin jiki ya tashi yana kuka yatafi, shikam duk wulak'ancin da matar zatayi mishi tausayi take bashi, dayasan idan idon Minal ya bud'e zai jawo musu matsala daya barta da makanta, yaci gaba da kula da ita, karkashin bishiya yaje ya zauna ya aje kayanshi idonshi yana fitar da hawaye,
A hankali yace " where are You beauty? Karki gujeni a wannan lokacin danake cike da buk'atarki, Saida kika lasamin zumarki kafin zaki gujeni? Kitaimaka ki dawo beauty"
Shi kad'ai yaketa surutunshi, Saida mangariba ya gabato kafin ya tashi ya nufi gida jikinshi duk a mace.

Yana zuwa gida lokacin Afrah tana zaune tayi tagumi, tana tunanin Bilal, Sallama yayi muryanshi a toshe, da sauri Afrah ta d'ago kanta tana kallin kofa, ganin Bilal ne d'auke da jaka yasata tashi da gudu taje ta rungumeshi, shima runtse idonshi yayi ya rungumeta sosai domin a wannan lokacin yanada buk'atar haka.

"Afrah jin bai hantareta ba yasa taji jikinta duk ya mutu da ganin yanayinshi, ya rame sosai saiya kara haske fuskarshi tayi fayau,
'Dago kanta tayi tace " Yaya meya sameka haka duk kabi ka rame?"

Idonshi ne yacika da hawaye a wannan lokacin idan baiyi magana ba zuciyarshi zata iya bugawa, cikin muryan Kuka yace "Afrah soyayyace, soyayyace tasa nazama haka, ta gujeni"
Kara rungumeta yayi yaci gaba da kuka kamar karamin yaro.

Jikin Afrah ne yayi sanyi, ganin yanda yake kuka, a hankali tafara bubbuga bayanshi tana lallashinshi,
Da kyar tasamu yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, Amma har yanzu yaki sakinta.

Hajiya babba ce taga Afrah ta jima, d'ankwali ta d'aura tafito tana kiran "Afrah ina kika shigane.....turus ta tsaya ganin Afrah rungume da namiji, Salati tafara tana tafa hannu, tace " shikenan Afrah kin zauce, yanzu tsabar rashin kunya zaki gayyato kato cikin gidannan da rana tsaka ki rungume? Hawaye tafara sharewa da bakin zaninta tanata salati.

Afrah ce ta saki Bilal, Hajiya babba tana ganin Bilal ta zaro ido, tace "La haula wala kuwwata illa billahi, Bilalu? Kaine ka rame ka fige kayi bak'i kamar d'an kasar Kenya?"

Bilal bai kulata ba ya d'au jakarshi zai wuce, Afrah ce tayi saurin karb'a tace "kawo nakai maka d'aki Yaya".

"Murmushi yayi ya mika mata suka Wuce Hajiya Babba data saki baki".

✔ote & Comment

Wattpad  @Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now