page 26

404 27 4
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 26...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Shiru Bilal yayi dan baisan Amsar dazai bashi ba.

Daddy yakara cewa "Bilal tambayarka fa nake ya akayi kasan kananan kayane ajikinta?"

Bilal yace "Daddy jikina ne yabani, sabida nasan sune kayan datake sawa, maganar duka kuma nasan Afrah kawai nadaka Amma ban tab'a Hajiya babba ba, Daddy inada haukane zan daki Hajiya babba?"

Hajiya babba ce ta harzuk'a tace "yo hauka na nawa kuma? Kana mak'aho ina zaka sani? Yanda kayita zabga min bulala abayana kamar kasamu jaka, tin jiya Addu'a nake yanda kayita zabga min bulala, Allah yasa mala'iku suyita zabgawa Uwarka guduma"......Bilal da ranshi ya b'aci yace " Hajiya babba kada ki kara sa uwata a wannan lamarin, sabida tana kabari batasan meyake faruwa ba"

"Kabaro Bilalu ba Kabariba, ai nima Uwata tana kabari kuma ka zage kayita jibgana"

Bilal bai k'arayi mata magana ba, kawai yatashi yafice a d'akin.
Gidan ma gaba d'aya yafita mishi arai.

Yana shiga d'aki yafad'a akan gado, cikin zuciyarshi yace "yanzu da Minal tana nan koba komai zan kalli fuskarta inji dad'i, to Amma meyasa takemin haka? Wata zuciyar tace mishi "kodai Dan kaki ka kaita India aduba mata idonta ne take wannan fushin?"

Wani tinani yayi kafin yatashi da sauri yanufi wardrobe ya d'auko Riga da wando yasa, makullin motarshi ya d'auka, tareda barin gidan gaba d'aya.

Gudu yake shararawa akan kwalta, bai tsayaba saida ya iso kofarsu Minal, yana zuwa dab yaji jikinshi yayi sanyi, duk zafin daya d'auka.
Yana zaune kusan minti talatin, harya cire ran zata fito, sai kawai yaga Madina tazo wucewa harta shiga gidan, "Alhmdllh" yace sabida yasan dolene tafito yanzu tinda ga kawarta.

Saida yakara kusan minti talatin akalla yayi Awa d'aya zaune awajen, kafin ya hangosu sun fito daga gidan, Madinace agaba sai Minal dake bin bayanta, tana kokarin sa hijabi.
Saida yabari suka wuce motarshi kafin yabud'e yafito.

A hankali yafara bin bayansu, cikin sand'a yasa hannu ya d'auke Minal,
Minal kuma jin an d'agata sama yasa tafara kiran "Madi....kafin tak'ara ya rufe bakinta da hannunshi, saida yakaita motar kafin yasake mata baki.

Minal da duk ta tsorata tace "wayene? Dan Allah kuyi hak'uri ni makauniya ce"

Shiiiiii Bilal yafad'a, "karki sake magana anan idan bahaka ba saina kwakule idonki nakaiwa kare ya cinye"

Minal takara mugun firgita  muryar Bilal, tasan zai iya tunda ya tsaneta, jikinta ne yafara Rawa,tace "Dan Allah yaya Bilal kayi hakuri wallahi bazan kara aika maka bak'ar magana ba na tuba, nabi Allah"

Bilal kunna mota yayi yad'au hanya da mugun speed, kamar zai tashi sama.

Minal Addu'a tafara afili tace "Subhanaka inni kuntu minazzalimeen".

_✔ote & comments_

Jiddah  S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now