page 27

346 18 1
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 27...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Banda Addu'a babu abinda Minal takeyi,
A b'angaren Bilal kuma dariya ma take bashi, bai wuce ko Ina ba sai Airport, parking na motarshi yayi kafin yaja hannunta suka fito, Minal tana ta rok'anshi Dan Allah kar yayi mata komai, ticket ya yanka musu kafin yawuce da ita wajen jirgi, yana zuwa yace kitsaya anan kar kiyi kuskuren fita sabida nan ba gidanku bane kinaji?
Gyad'a kai tayi tace "Dan Allah yaya Bilal karka cutar dani"
Bilal ko kallonta baiyi ba, yawuce yaje ya siyo abinci da drinks.

"Oya kici"
Minal kuka tafara tace "banajin yunwa ka maidani gida kawai"

Bilal yace "ok karki ci kizauna da yunwa, nidai nafita a hakki"

Kuka Minal tafara, kamar anyi mata mutuwa.
Daidai lokacin aka fara announcing cewa jirgi yakusa tashi kowa ya shirya.

Minal kukanta ne ya tsananta jin hardasu jirgi,
Bilal zama yayi a gefenta yana kallon yanda take kuka kamar anyi mata mutuwa, dariya ma abun yabashi, saida yayi daidai son ranshi kafin yariko hannunta yace "haba mana beauty meyasa kike kuka haka? Nifa gidan yankan kai kawai zan kaiki a kasar waje, kinga ai addu'a zakiyi ko?"

Ihu Minal tafara tana bubbuga kafarta a kasa, tace "nashiga Uku na lalace nahad'u da d'an yankan kai, shikenan nawa yakare, Umma ki yafeni na saci kud'inki na siya awara a makaranta"

Bilal dariya yake harda rike ciki, wayarshi yad'auko yafarayi mata video.
Lokacin da jirgi ya tashi, wani irin runguma Minal tayiwa Bilal tsabar tsorata, jingina jikinshi yayi da kujerar shima ya rungumeta sosai ajikinshi.
Minal baccine ya d'auketa.

Bilal tausayi yarinyar take bashi, ganin da tana ganin komai amma yanzu bata ganin komai sai duhu, yanason ya tambayeta meya sameta har idonta ya makance Amma yana ganin kamar bazataji dad'i ba.

6:30Pm daidai suka sauka a kasar India.
Hotel Bilal ya kaisu a kwalkwata.
"Inane nan yaya Bilal?"

"Wajen yankan kai ne, Akwai matsala ne beauty?"

Bata kara magana ba.
Bilal hannunta yaja har zuwa d'akin daya kama musu.

Suna shiga yace "oya cire kayanki kiyi wanka"
"Ni bazanyi wanka ba a wanke nake"

Cikin tsawa Bilal yace "tashi kiyi wanka nace, umarni nabaki ba ra'ayinki na tambaya ba"

Ta tsorata da maganar tashi, dama gata gwanar tsoro, ka kaini toilet d'in tafad'a cikin cikin tsoro.

_✔ote & comments_

Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now