page 19

361 24 2
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  By
Jiddah S Mapi

Page 19...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Kayi hauka ne?  Meya kasheta?"

Bilal yace "Daddy ni na kasheta, dukanta nayi, da hannuna"

Daddy yace "muje d'akin naku"

"Dasauri suka nufi d'akin Bilal, wurin shiga d'akin ne Bilal tsabar rikicewa, yayi tuntub'e da k'ofa, saura kad'an ya fad'i,
Daddy ne yayi saurin rikeshi, Bilal kabi a hankali mana, kasan ba gani kake ba, meyasa zakayi sauri? Bilal yace " ba komai muje kawai Daddy"

"Suna shiga d'akin, Daddy ya karasa inda Minal take kwance, kallo d'aya yayi mata yagane cewa doguwar suma tayi, yad'an d'aga hannunta yakuma. Sakewa, a hankali ya furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un Bilal meyasa kayi kisan kai?"

"Bilal ne ya zauna a kasa jin wani irin jiri dayake Neman kada shi, yace " Daddy tamutu ko?"

Daddy ne ya girgiza kanshi tareda cewa "Kwarai kuwa, karo na farko da aka fara kisan kai a Family d'inmu, yanzu abinda za'ayi dolene mukira 'yan sanda su San abinda ake ciki, sabida tsaro, kafin akaita makwancinta"

Bilal yace "Daddy 'yan Sanda kuma? Meya kawo kawo 'yan sanda cikin wannan maganar da wuri haka?.

Daddy yace " Aa Bilal kiran 'yan sanda shine mafi muhimmanci" dasauri yasa hannu a Aljihu ya kira DPO tareda sanar dashi abinda yafaru, DPO yace "Alhj Ku kaita Asibiti kafin muzo muyi bincike"

"Bilal ne ya d'auketa yasata a mota, suka nufi Asibiti, suna isa likitoci sukayi Emergency Room da ita, gwaje gwaje aka fara har suka gano tanada rai, Dogon suma ne tayi sakamakon zazzab'i daya damera"
Ruwa aka d'aura mata tareda yi mata Allura"

Bilal yakasa zaune yakasa tsaye, zagaye cikin Asibitin yake yi. Azuciyar shi yace "yanzu idan ta mutu ni nakasheta? Ni Bilal nayi kisan kai?
Allah kasa ba mutuwa tayi ba"

"Yana cikin haka sai ga likitoci sun fito, da gudu Bilal yakarasa wajensu yana tambaya, " doctor ta mutu ko?"
Doctor ne yace "no bata mutu ba, Amma tana dab da mutuwa, kai mijinta ne?"
Bilal yace "eh ni mijinta ne"

Doctor yace "okay biyoni office akwai  wata magana da zamuyi"

Da sauri suka nufi Office na doctor.

Doctor ne yacewa Bilal "zauna mana malam Bilal ka kwantar da hankalinka zata samu lafiya"

Bilal yace "doctor ya kake ganin zan samu kwanciyar hankali bayan baka da tabbacin zata Rayu?"

Doctor yace "magana nake son muyi dakai, magana kuma me muhimmanci"

Bilal ne yasamu waje ya zauna, fuskarshi duk zufa.

Doctor yace "Malam Bilal ko zaka iya fad'a mana me matarka taci last kafin faruwar hakan?"

Bilal yace "Doctor me ya kawo maganar abunda taci, nidai nasan munyi fad'a da ita kuma na daketa da Belt shine kad'ai abinda nasani"

Doctor yace "To a zahirin gaskiya munyi iya gwaje gwajenmu mun gano cewa matarka guba taci, hakan yakawo mata muguwar zazzab'i, anyi amfani da gubar da baza'a gane ba sai likitoci, sabida haka muna buk'atar abinda taci last, zamuyi gwaje gwaje akai"

Bilal ne ya mik'e a tsorace yace "GUBA kuma doctor? Okay ina zuwa"

Da sauri yafita yabar office d'in yanufi wajen daddy yace "Daddy Inason muje gida yanzu"

Daddy yace "komai dai lafiya kam Bilal?"

Bilal yace "kaidai muje kawai Daddy"
Driver suka d'au hanya"

Suna isa gida Bilal yatara duk ma'aikatan gidan da kuma mutanen gidan A babban Falo.
Bayan kowa ya zauna ne Bilal yayi gyaran murya yace.

"Waye yasawa matata guba cikin Abinci?"

Falo yayi tsit babu Wanda yayi magana.

Bilal yace "ba tambayarku nake ba? To wallahi idan Baku fad'amin gaskiya ba gaba d'aya yau saina koreku a aiki".

" ma'aikatan ne suka fara baiwa Bilal hakuri, dacewa su basu San waya bata abinci da guba ba"

Hajiya babbace ta mik'e tace "Kai baka isa ka kori ma'aikatan gidannan ba, sabida ba gidan Ubanka bane"

Bilal yamike yace "Hajiya babba ki tsaya a iya matsayinki kada ki kuskura ki kara samin Baki a magana na, kina ji"

Daddy ne ya mik'e yace "haba Bilal ya zaka tsaya kana yiwa mahaifiyata tsawa? Okay sabida ba ita ta haifi Babanka ba?"
Wa kake tunanin zai baiwa matarka guba? Kasani fa ita makauniya ce zata iya cin komai ba tareda ta sani ba.....Bilal ne ya katseshi da cewa "Daddy Dan ita Makauniya ce sai a cuceta? A iya sanina babu guba a d'akinmu, dolene akwai Wanda yakai mata tasha, kuma saina samo meshi"

Bilal yace "daga yanzu na sallami duk wasu ma'aikatan gidannan"

Da sauri inna wacce take dafa abinci a gidan ta tashi tace "inada magana"

Bilal yace "muna jinki"

Inna tace "wallahi yallab'ai gaskiya zan fad'a maka, sabida idan narasa aikin nan ban San ina zan samu wani ba, kuma Babar 'ya'yana da yunwa a can gida kauye"

Bilal ne yace "kiyi maganarki muna ji"

Inna tace "d'azu ne ina zaune a kitchen shine Hajiya Babba da Afrah suka shigo, suka mik'amin wani Abu acikin farar Leda, suka ce in sawa Minal a cikin abincinta na rana sabida tasa damuwa a ranta bata iya bacci, nikuma ban kawo komai a raina ba saina sa mata, na zata ko maganin bacci ne, saida ta cinye kafin naji Hajiya babba tana cewa yau karshen Makauniya yazo, daganan sai na fara zargin ko dai maganin mutuwa ne, yallab'ai shine iya gaskiyar abinda nasani"

"Gaba d'aya Falon aka d'au salati kowa yana Allah wadaran da wannan halin, banda Hajiya babba da Afrah da Daddy da suketa kallon kallo a tsakaninsu"

Bilal ne yace "dama ina zargin wani Abu, Amma tunda gaskiya yafito, Hajiya babba da Afrah sunyi yunk'urin kashe matata, to ina me Sanar da mutanen gidannan, nafasa Auren Afrah kuma bazan Auri Afrah ba har  abada, m
Ke kuma inna zan sallameki da makudan kud'ad'e Wanda zasu isheki keda yaranki, na sallameki a gidannan"

Inna ce tafara kuka tana rok'an gafara,

"Bilal baiyi magana ba yatashi yafita, daidai bak'in kofa yaji karan motar 'yan Sanda Wanda Daddy yakira su"

Juyawa yayi wajen Daddy yace "sai kasan yanda zakuyi da 'yan Sandan da ka kira".

_"ina kara Baku hakuri a 'yan kwanakin nan bazan iya typing dayawa ba sabida wasu dalilai nawa"_

_✔ote & Comment_

Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now