Chapter two

2.6K 197 4
                                    

Wanene Abdulshakur

Abudulshakur dane ga Alhaji Yusuf Ashaka, wanda yake haifaffan dan garin kano, Alhj yusuf ashaka su biyo iyayensa suka haifa daga shi sai kanwar shi me suna yasira, mahaifiyar su ta rasu lokacin da ta haifi yasira, sun tashi a kano ciki da so da kulawa a gurun mahaifin su har lokacin da suka iya rike kansu.

Alhj yusuf ashaka babban dan kasuwa me, domin sunan shi ma yayi fuce a kano da wasu fannin na nigeria yana da shekaru 26 kad'ai ya gina kamfani dinshi me suna Ashaka Limited,

Kamfani nin sosai dake sarrfa kayan abinci da dai sauran su, yana da shekaru 28 ya hadu da Aisha wacce take y'a ga yayyan mijin yasira, Aisha wacce take da shekaru 20 fara ce sosai ka kyau mutuka kamar balarabiya gata bafulatana gaba da baya,

bada jimawa ba bayan haduwar su soyyaya tashiga da kuma shakuwa mai karfi, tuni suka fahimci juna aka fara shirye shiryen biki, bayan bikin da shekara daya Aisha ta haifo yar ta me kyawun gaske, ansha murna ba iyaka kuma Alhj yusuf yafito da kudi anci ansha da sunan ta, sannan aka rada mata suna Zainab, taci sunan mahaifiyar Alhaji yusuf,

zainab nada shekara uku aka haifo mata kanwa, nanma anyi murna sosai ita aka rada mata khadija, ita kuwa sunnan mahaifiyar Aisha aka saka mata,

haka suka cigaba da cin rayuwar su, ga business din Alhj yusuf sai kara bunkasa yake bayan shekara uku da haihuwar Khadija, Aisha ta sake samun ciki, murna kuwa a wajan Alhj yusuf bata misaltuwa, bayan watanni Tara cif ta haifi santalelan danta, anyi murna saboda shine farkon haihuwar da namiji da tayi, anyi suna wanda ba'a taba gani ba naira tayi kuka, haka aka saka mishi suna ABDULSHAKUR wanda sunan da hajia aisha take so mutuka ta saka ma danta namiji duk randa Allah ya bata,

Abdulshakur kuwa yasha kyaututuka masu yawa gurin abokana Alhj yusuf, daga mai bashi fili sai mai bashi gida, (niko nace wai kunji dan jaririn da bai wuce kwanaki bakwai a duniya ake ma wannan kyautar).

Abdulshakur ya tashi da so mara misaltuwa, shekarun shi basu wuce hudu ba amma duk abokanan shi masu kyau ne, yace bazai yi abokai da munana ba, saboda shi duk wanda ya sani suna da kyau, mommy dinshi, duk kuma yayyan shi mata suna da kyau sosai, har ma daddy dinshi, duk da daddy dinshi baki ne amma yana da kyau, harma cewa yake abu mumuna yana bashi kyankyemi,

Haj aisha ba yadda bata yi ba ta canza mishi dabi'a, amma yaki, da dan karamin shekarun shi amma sai taurin kan tsiya, mahaifiyar shi kuwa sai hak'ura tayi a cewar ta in ya girma zai daina.

Haka rayuwa ta cigaba da gudana a gidan, ga kwanciyar hankali.


Shekaran Abdulshakur sha biyar a duniya aka haifi yan biyu, bilkisu da rukayya ana ce ma bilkisu Amal,rukayya kuma Amra, yan biyu na da wata 7 a duniya Allah ya yima mahaifin Alhj yusuf rasuwa, mutuwar da ratsa masoyan sa amma ba yadda suka iya saboda duk mai rai mamaci ne, a haka har aka yi arbain rayuwa kuma ta cigaba da gudana.

Haj Aisha ta cigaba da kula da yayan ta kuma dora su a hanyar addinin musulumci duk da kan kantar shekarun su suna da addini mutuka,

Abdulshakur na babar secondary school ah kano makarantar na da kyau sosai, tun da ya shiga secondary mata suka mishi sha aka ko wacce mace tana so ya kula ta barin ma matan class din su, duk abun ba burge abdulshakur yake ba saboda matan basu ma gaban shi, yace ya tashi aure balarabiya can zaije ya aura me kyau saboda matan nigeria duk munana ne,

Haka ya ci gaba da rayuwarshi cikin miskilanci da rashin san magana, sam baya shiga harka mutane ko kadan, rayuwar shi yake sai kuwa yan abokanan shi da basu wuce guda hudu ba, yana kaiwa ss1 miskilanci ya kara nikuwa gashi kuma ya kara kyau fiya da da ya fara zama namiji.

Abudulshakur na gama secondary school, ya tafi dubai yin degree dinshi akan businesses administration, saboda yana san yin kasuwanci kamar baban shi, mahaifiyar shi bata so ba, taso abar mata tillon danta na miji gaban ta yayi karatu amma sam baban shi baya san yayi degree a nigeria, haka ta hakura domin ita mesan farin cikin mijinta ce kuma ta lura Abdulshakur shima yana san zuwa,

lokacin da Abdulshakur ke shekara ta biyu shi a jami'a aka yima zainab da khadija aure, anyi biki kuwa an kashe kudi masu mugun yawa, khadija doctor da aura me suna Nura, ita kuwa zainab ma aikacin banki ne me suna Ahmad, suna da kudin su dadai gwargwado, yayyan nashi sunso ace dan tilon kanin su yazo bikin su amma Abdulshakur bai samu daman zuwa ba sobada jarabawa da ta saka shi ah gaba, haka suka hakura akayi biki ko wacce amarya ankai ta gidan ta, amma duk ba'a kano suka zauna ba, zainab na lagos, Khadija kuma tana abuja.

Haka abudulshakur ya cigaba da rayuwanshi yama ki dawowa nigeria sai dai iyyayen shi da kannan shi suje su ganshi, sam yaki dawowa har saida ya gama university din shi tsab, yana gama wa su mommy da daddy suka je graduation dinshi ya fita da sakamako me kyau Alhamdulillahi, ya kuma karbi kyaututuka masu yawa, ana gamar hidimar graduation mommy tace su tattara su koma nigeria tunda ya gama abunda ya kawo shi, haka suka kuma duk da bai dan ya so ba,

Suna isa kuma gida ya cika makil da yan uwa su ya zainab da ya khadija suma duk sun zo, ya zainab da yar babynta wacce bata wuce shekara daya ba mai suna hudallah, ana ce mata huda, ya khadija kuma da tsohon ciki sai yan biyu a gefe da yanzu suke primary school a saint louis, haka aka tarbe su anci kuma ansha sannan kowa ya watse.

Bayan wasu watanni Abudulshakur ya tafi NYSC dinshi abu ba wuya yana farawa bada dadewa ba ya gama, yana kuwa gama wa ya wuce London yin masters dinshi nama shekaru biyu yayi ya dawo, lokacin da ya dawo nigeria abudulshakur ya kara mahaukacin kyau haka saje ya zauna mishi ga gashin kanshi baki kirin ya kwanta luf ga fatar jikin shi fari kal ga yayi fresh ya koma kamar badan nigeria ba, ka kalli cikin idanunshi kamar gray ne color din ba baki ba aikuwa mata sukai mai ca aka daga yayan ministers sai yayan senators sai yayan governors kowa so yake abdulshakur ya soshi, kullum mata na cikin mishi shishigi saboda tsaban kyuan da Allah ya bashi amma shi duk basa gaban shi saboda har yanzu matan nigeria basuyi mishi ba, duk a munana ya dauke su komai kyaun su, ga shegen miskilinci da taurin kai, da wuya kaga yana murmushi kullum fuskar shi a murtuke take tam amma haka ba karamin kyau yake mishi ba, mata mutuwa suke a kanshi amma ko a jikin shi kullum yana cikin cewa friends dinshi yake bai taba ganin matan da basu da class ba kamar matan nigeria (kunji fa).

Abdulshakur nada shekaru 26 Alhj yusuf ya sauka ya bashi kujerar shi ta CEO, ya danka mishi komai a hannun shi na kamfanin Ashaka acewar shi yanzu ya tsufa ya kamata ya dan huta, aikuwa Abdulshakur ya karba hannu biyu kan kace me Ashaka ya kara bunkasa yama nininka na daa, kudin ya kara ninkuwa bila adadi, a shekar shi ta biyar a company din ya karan bude branches a duk states din nigeria, da wasu African countries din, kan kice me Abdulshakur ya shiga cikin forbes richest people under 35 ba wanda baisan sunan sa ba a Afirca.

Ya zama muti millionaire haka ya cigaba da rayuwan shi cikin miskilancin da taurin kan shi.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now