Chapter forty-three

1.5K 196 10
                                    

Har yanzu baya ganin dadai, bayan wani mugun ciwo da kanshi ke mishi, wata mota ce tayi kanshi, sauri yayi yai gefe tara da saka birki, ya tsaya cak ya fara maida numfashi, jikin shi rawa ya fara ga zazzabi ya gama rufe shi, ga kirjin shi da har lokacin bai daina ciwo ba, wayar shi ya samu ya laluba ya d'auko da kyar ya iya kai kan number d'in usman, ya samu ya saka a kunnan shi, yana ji ta fara ringing ya jingina bayan shi da kujerar motar tare da lumshe idanunshi, usman na d'aukar wayar ya umarce shi da yazo ya kaishi gida baya jin dad'i yana gama fad'a ya kashe wayar bai jira jin mai zai ce ba, dan ko magana wuya take bashi, ga hucin zafi da ke fitowa daga bakin shi in yayi magana tsabar jikinshi yayi mugun zafi, Har lokacin idanunshi a rufe suke, baka jin k'arar komai sai k'arar motoci na wucewa a titi,

Yana ji in har ba gawar shi aka kaima samira ba baza ta tab'a jin tausayin shi ba ta daina gaya mishi mugayen kalaman nan nata, kalaman dake azabtar dashi iya azaba, mene laifin shi dan yana santa, mene laifin shi dan yana nuna damuwar shi da kulawar shi akan ta, bai jin ya cancanci wulaqancin da take mishi, a ganin shi ko mak'iyin ta bata ma irin wulaqancin da take mai, amma ya zaiyi, dole ne ya jure saboda santa yabi jinin jikinshi ya shiga cikin zuciyar shi yayi mata mugun kamu, k'ara yin wata ajiyar zuciyar yayi, bacci ne yayi gaba dashi baima sani ba tsabar yadda yake jin jiki,

Knocking d'in window d'inshi da akayi ne ya farkar dashi daga baccin da yake, usman ya gani a tsaye, hamdala ya shiga yi dan har bayan shi ya gaji ya fara ciwo, bud'e murfin motar yayi ya saka k'afarshi ya fito, yana fara takawa jiri ya d'ibe shi, yayi k'asa zai fad'i usman yayi saurin taro shi yana subhanallahi, bai tab'a ganin abdulshakur ba a cikin yanayin, har abun sai da ya bashi tsoro da yaji zafin da jikin shi yayi, haka ya kama shi ya saka shi a cikin mota, shima ya koma ya zauna a drivers seat, yana shiga ya tambaya ko asibiti zai kaishi, abdulshakur girgiza kai yayi yace kawai ya kaishi gida kuma ya k'ara umartar shi da ko sunje gida kada ya gaya wa kowa, usman sai da ya bishi da kallo, taya zai gaya mishi haka bayan yana cikin wannan yanayin, baya san kanshi ne, ya tambayi kanshi, haka ya bi umarnin shi dan ba yadda zaiyi ya fara tuk'a motar yana sak'e sak'e a ranshi.

Suna isa gida, ya paka motar tare da yin sauri ya bud'e gaban motar ya k'ara kama shi suka shiga side d'inshi, bedroom d'inshi suka wuce direct, suna isa abdulshakur ya k'wace jikin shi ya rarrafa ya haye kan gado ya lulub'a da blanket wani irin sanyi yake ji, yaji usman dai yayi magana baisan me yace ba, yana gani ya juya zai fita can kuwa ya dawo ya d'auki wayar da ya ajiye akan bedside drawer ya saka a kunne ya fara magana, shima baiji mai yace ba kawai ya kulle idanunshi bacci ya k'ara yin gaba dashi.

Muryoyin mutane da yake ji sama sama ne ya tayar dashi, bud'e idanunshi yayi a hankali yayi kicibis da y'an gidan su, dukkan su kowa na d'akin har daddy, hankalin su baya kanshi amma shi yasan maganar shi suke, ji yayi ya gaji da kwanciya ya fara shirin mik'ewa, abu yaji ya d'an soke shi a hannu, yana kai idanunshi yaga igiyar drip, lumshe idanunshi yayi, gaskiya shi da samira soulmates ne, tana can a kwance ba lafiya shima gashi anan a kwance,

"Ya tashi"

muryar amra yaji tana fad'a, mai da idanunshi wurin su yayi, yaga mommy na saurin k'arasowa inda yake, fuskar ta d'auke da tsan tsan damuwa, daddy ma na gefan ta, dukda shi fuskarshi bata nuna ba yasan shima ya damu,

"Haba abdulshakur, kana da hankali kuwa, ka kwana da irin zazzabin nan amma ka kasa gaya wa kowa, muna kuma gida d'aya, yanzu da ban aika Amal tazo kiran ka ba dan naji ka shiru baka shigo ba da sai dai muzo muga gawar ka, ka kyauta kenan?"

Mommy tayi magana cikin fad'a amma a hankali, tare da k'ara cewa,

"In kai baka san kanka mu muna sanka atleast kayi considering wannan"

Wallahi yana san maman shi, amma dan Allah zata daina yin kamar wani terminal illness yake dashi, zazzabi ne kawai ya zata in har yayi bacci zai tashi ya ji shi garau, ya fad'a a zuci yayin da azahira yace

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now