Chapter forty-four

1.4K 193 3
                                    

K'awayen amaryar na cikin makeken parlor d'in antyn d'in farida da yake yafi kusa da event center d'in, yayin da ango da amryar su kuma na shan photoshoot kan a k'arasa wurin dinner, sunyi masiffan kyau, farida ta saka silver shi kuma khalifa ya saka ash, ga fuskar amaryar tasha make up, k'wayen amaryar ma ba'a barsu a baya ba, kowa a cikin su yasha kyau a cikin ankon su na dark blue ga fuskar ko wanne a cikin su ta d'auki kwaliya,

Samira na gefe tana jiran shigowar nabila dan yanzu sati biyu rabonta da ita, har ta gaji da kiran wayar ta ga bata sami kanta ba tana ta rashin lafiya tunda suka dawo daga lagos sai kwana shida da suka wuce, ga mama tak'i barinta ta fito da tun yaushe taje gidan su, sai da amma tayi magana da taga kowa na zuwa duba ta amma banda ita, k'arya ta shirga mata tayi mamaki da ta yarda, jiya ma bata samu tazo kamu ba balle su bridal shower mama tace ta k'ara samun sauk'i tukun ta murmure,

Nabila ce ta shigo parlor d'in, tayi masiffafan kyau, ga ta daman fara me kyau kuma ga dark color a jikin ta, samira zumbur tayi ta d'ago daga jinginar da tayi akan kujera ta zuba mata ido, tana ganin tana gaisawa da sauran k'awayen har taje wurin farida ta rungume ta tare da gaisawa da khalifa, tana jira taga tazo wurin ta kawai taga tayi wurin su meena, ko kallonta bata yi ba kamar bata wurin, gabanta ne ya fad'i, har yanzu bata manta ba, wata zuciyar ce tace mata taya zaki ga babbar k'awarki da saurayin ki ki kasa jin zafin abun,
haka ta ci gaba da bun nabila da kallo, su kansu sauran abun bai musu dad'i ba abunda nabila tayi, amma haka suka share,

Ji sukayi anyi sallama, muryar abokan ango, zuciyar ta ce ta fara mahaukacin bugawa tayi saurin sauke idanunta, abunda take bala'in jin tsoro wanda tunanin ma ya hana ta samun ishashen bacci jiya, had'uwa da abudulshakur, shima rabonta dashi tun wulaqncin da tayi mishi a asibiti, sanadiyar jin da tayi bashi da lafiya ya saka ta k'ara kwanaki a asibiti, me makon tayi kwana uku tayi sati d'aya, rashin lafiyar ta ta k'ara yin tsanani,

Tana ji suma suna gaisawa da k'wayen amarya daman su ake jira dan duka tare zasu tafi, ji tayi Al-ameen da shahid na mata magana, ba daman ta share su, dake wa tayi ta d'ago da kanta tagan su a tsaye sunyi kyau sosai suma sunsha ankon getzner sky blue da babbar riga, mazewa tayi suka gaisa kamar ba abunda ke damun ta, maida kanta k'asa tayi tai shiru, can taji baza ta iya ba sai ta saka shi a idanunta, kwana da kwana ki bata ganshi ba ga shima yayi rashin lafiya, so take ta gani da idanunta ya sami sauki, sacen kallon shi tayi tagan shi a tsaye shi da khalifa suna magana suna dariya, numfashin ta taji yayi sama, ji tayi wani sonshi ya k'ara bugar mata zuciya, tunda take bata tab'a ganin namiji me kyan halita ba kamar shi, tunda take bata tab'a ganin namiji da manyan kaya ke ma kyau ba kamar shi, kayan sun sake cika shi sun k'ara fito da kwarjinin shi, garin sacen kallo ba sai Samira ta wuce ba, yanzu sosai kallon abdulshakur take, ta tabbata matan wurin suma sacen kallon shi suke dan yayi bala'in kyau bazan iya kwatanta muku ba, ga yayi wani fresh ya k'ara haske ga saje ya sake cika mishi farar fuskarshi, amma in ka dad'e kana kallonshi zaka ga ya rame, juyowa yayi sai ga idanunshi cikin nata, azababbiyar kunya ce ta kamata tayi saurin sauke idanunta, duk bata ga harara da nabila ke mata ba,

Wannan wana irin abun kunya ne, ta tabbata yaji kallon da take mishi yayi yawa shi ya saka shi juyowa, ji tak'e dama k'asa ta tsage ta shiga,

"Oya oya ku taso ku taso mu tafi dan ana can ana jiran shigowar amarya da ango"

Nasir ne ya fad'a, wani dad'i taji a ranta ya taimake ta, kowa mik'ewa yayi suka fara barin d'akin, samira itama tashi tayi, zata fita kenan farida ta jawo hannunta,

"Ina zaki, ai dake zamu tafi tare a motar abdulshakur"

Ji tayi gabanta yayi mummunar fad'uwa, wane abdulshakur kuma, yaushe ma sukayi haka da farida, abdulshakur d'in da shine mutum na k'arshe da bata san su had'u ko wani abu ya had'a su, sauri tayi ta fara waiga wa dan ta kamu hannun wata acikin k'awayen ta had'a ta dasu, amma wayam ba kowa duk sun watse, lumshe idanunta tayi, shikenan an gama da ita, kai idanunta wurin shi tayi taga har lokacin magana suke yi da khalifa, sunkuyar da kanta tayi ta fara ma farida magana a hankali kamar bata so suji,

"Me yasa sai ni?"

Ta tambayi k'awartata, farida kuwa abun yaso bata dariya,

"Yace bazai d'auki kowa a motar shi ba in ba ke ba"

Ta maida mata da amsa itama a hankali, samira ajiyar zuciya tayi, ta dad'e bata ga mai taurin kai ma kamar shi, yanzu ya zatayi ga ba damar guduwa, ta tabbata sauran har sun kusa isa venue d'in,

"In kun gama rad'an ai sai mu tafi ko"

Khalifa ya fad'i, muryarshi d'auke da wasa da farin ciki, samira d'agowa tayi dan ta kalli mai maganar amma sai ga tayi kicibis da idanun abdulshakur, wannan manyan idanun nashi ya kafa mata, samira sai da taji wani abu tsi ya wuce ta tsakiyar kanta, ga zuciyar ta da ta fara mahaukacin bugawa, khalifa ne ya k'araso inda suke ya kama hannun farida suka fita daga parlor d'in, samira na ganin sun barta ita k'ad'ai dashi ta fara sauri itama dan tayi saurin bari d'akin.

Abdulshakur na driver's seat na tuk'i, samira na gaban mota amarya da ango na baya, yadda yake tuk'in shi kanshi sai ka kalle shi ka k'ara kallo, hannu d'ayan da yake tuk'i yana sanye da Rolex ga jijoyin hannun suma sun fito, wai dan tayi kwanki bata ganshi ba shine gaba d'aya ta rikice komai nashi ya dawo bata sha'awa, wani irin haushin kanta take ji, tunda ya shigo bai nuna ya damu da ita ba, gaba d'aya ita ke hauka akan shi, in tace abun bai b'ata mata rai ba tayi k'arya, ya kalle ta sau biyu amma da abudulshakur d'in daa ne da tasan bazai gaji da daina kallonta ba, ga magana ma dai bazai daina yi mata ba, gabanta ne ya fad'i, kada dai abun da take jin tsoro ya faru, ya gaji da wulaqancin ta ya hak'ura, wani gumi taji ya keto mata dukda akwai sanyin ac a cikin motar, in ya daina kulata tana cikin bala'i dan ita yanzu ma ta fara sanshi, wata zuciyar ce tace mata ba haka keko so ba daman, ya daina kula ki, ji tayi kamar ta kurma iho a cikin motar, gaba d'aya hakalinta ya fara tashi, jin k'arar bud'e k'ofar da akayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin ta sai a lokacin ta lura sun isa venue d'in.

Zayyan ne a tsaye yana yi ma amaran magana, juyawa tayi taga abdulshakur na shirin fita daga motar, itama fitowa tayi taga ana ta d'aukar amarya da angon hoto a cikin motar har photographers d'in, an dad'e ana abu d'aya sai can suka fito, suna ji mc daga cikin makeken wurin yana jawabin yanzu amarya da ango zasu shigo,

Dukan su sun jeru sun saka amarya da angon a tsakiya, kowa da partner d'inshi, samira partner d'inta Mubarak ne, abun ko d'aya baiyi mata dad'i ba, kuma a lokacin ta sake sani akwai matsala dan tasan da kwanaki ne bazai tab'a barinta ita kad'ai ba, haka ta dunk'a satar kallon shi da yake a bayan shi take, ga ya dage sai hira yake da partner d'inshi wato Asiya, abun ya bata mamaki dan tasan ba haka yake ba, shi da kwata kwata ba ya shiga harkar mata, wani abu taji ya tsaya mata a mak'ogaru ga wani haushin Asiyan da take ji kamar ta mangare ta, gaba d'aya yanzu bikin ya fita daga ranta, ji take kamar ta koma gida, kuka ne keson kub'oce mata tayi saurin sunkuyar da kanta da danne shi da kyar ta maida kwallar ta, wak'a aka saka musu, suka fara takawa a hankali dan shiga wurin.

(DOUBLE UPDATE!!!

So nake na gama da novel d'innan dan ina jin tsoron za'a iya komawa makaranta a ko wane time ga ana komawa sai exams, dan haka kuyi expecting update kullum in ma ba guda biyu ba a rana,

yadda update d'in zai kasance, d'aya da rana d'aya kuma da daddare,

PLEASE VOTE AND SHARE ❤️❤️ and check my new book MUGUN MIJI)

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now