Chapter thirty

1.6K 162 8
                                    

Suna idar da sallar isha dukkan su suka fito yin walk da d'an ganin unguwar, abdulshakur na can baya da chewing gum d'in shi nabila sai faman surutu take zuba mishi, shi kwata kwata bai maso zuwa ba amma kawai saboda ya saka ma ismail ido, duk abunda yake ya zamana a gaban idanunshi yake, ya tabbata sai ya takura ma y'ar baiwar Allah,

Samira na gaban shi itama da chewing gum d'inta ismail, shi kuwa bada ban yasan asalin nabila dashi ismail d'in ba da yace ciki d'aya suka fito tsabagen masiffafan nacin su, shi wallahi yanzu har kunya yake ji ya kira Ismail abokinshi, sai wawanci da shashanci yake zubawa tunda suka zo trip d'innan, yarinya ta nuna maka bata so ba sau d'aya ba ba sau biyu ba ace kak'i gane wa, wani irin dogon tsaki yaja a ranshi,

Yana ganinta ta tana sunkuyar da kanta da matsa wa in ismail ya matso dab da ita, wata irin harara yake yima k'eyar shi, ji yake kamar yakai mishi wani irin naushi,

Haka sukayi ta tafiya har suka d'anyi nisa, har lokacin bai tanka ma nabila zancin da take faman zuba mishi, saboda ma gaba d'aya hankalin shi baya wurinta, yana wurin Ismail da samira wanda ya tabbata bama su san yana yi ba saboda gaba d'aya sun bada mishi baya, haka sukayi ta tafiya ba zagin da ismail bai sha ba yau a zuciyar shi.

Samira ce tayi kamar zata ci k'asa wato zata fad'i, abdulshakur bai san lokacin da ya d'an fara gudu dan yayi saurin taro ta koda rik'e hannunta ne yayi saboda ba wani nisa a tsakanin su in har ta fad'i a wurin ya san tabbas sai taji rauni, shi kuwa ya tsani abunda zai tab'a lafiyar ta harta jikinta gabaki d'aya, amma Ismail ya riga shi, gaba d'aya rungumota jikin shi yayi, abdulshakur shi kuma cak ya tsaya a wurin, tsabar abun ya bala'in daure mishi kai, amma gaskiya ismail d'an Iska ne na ajin farko, akwai hanyoyin da dama da zai yi ya taro ta ba lallai sai yayi mata irin wannan rigumar ba, gashi dab da ita ai ko hannunta zai iya kamo wa, yana gani samira tayi saurin k'wace wa daga jikin shi.

Ci gaba da tsayawa yayi ya zuba musu kallo ko takan nabila baya yi itama da take mishi wani irin kallo, irin kallo mai da kake shirin yi, su kuwa sauran abokan nasu ma sunyi nisa sosai ko hango su basa yi,

A gaban idanunshi Ismail ya tsuguna ya dauke wani dutse daga wurin sannan yana ji da kunnuwan shi yana gaya nata takalminta ya tsinke, k'ara gani Ismail yayi ya fara shirin cire takalminshi ya saka su a gabanta daman shima slippers ne a tashi k'afar, Samira kuwa girgiza kanta tayi alamun aa, amma Ismail sai da ya tsuguna har k'asa ya dauk'i kafafunta ya saka su a cikin wannan takalmin, sannan ya tashi daga inda yake ya zuba mata murmushi,

Abudulshakur wani mugun tsaki yaja tsabar takai ci kuma wannan karan ya fito fili har sai da samira da ismail suka juyo, sai a wannan lokacin suka kula da suna bayan su, wata irin harara ya daka musu gaba d'aya su biyun sannan ya juyo ya fara koma wa gida,

Bazai tab'a iya tsayawa yaga wannan irin iskancin ba, ya tabbata in har ya k'ara sakwan d'aya a wurin to sai sun kwashi y'an kallo da ismail,

Haka ya d'unk'a sauri shi kad'ai dan wannan karan nabila bata biyo shi ba, shi baima kula ba sai da ya isa gida, saboda ko tana tare dashi da ita da banza duk d'aya suke a wurin shi, yana shiga d'akin shi yayi ya fara cire kaya sannan ya fad'a bathroom, dole ne yayi wanka ko ya rage wannan masifar ta cikin zuciyar shi.

$$$$$$$$$$$

Y'an trip kuwa har an kwashi kawana hud'u a lagos kamar wasa, garin wani dad'i yake musu, ga wani irin having fun da suke, kullum sai sun fita, ga wata shak'uwa da ta shiga tsakanin abokan ango da amarya, sun Saba yanzu sosai, ko Samira ta Saba da su yanzu tana sakayewa suyi wasa da dariya da hira, har ismail d'in yanzu tana sakar mishi fuska ba kamar da ba, yanzu ya d'an rage shishigin da yake mata, gashi shima sun d'an saba,

Shire take da kowa acikin abokan ango amma banda shakur, har yau suna jiya ih yau, ba abunda yake had'a su, ko k'awayen amaryar shi kad'ai ne basu saba dashi ba, ko side d'insu cin abinci baya zuwa tunda ya zo ranar farko, sai dai a saka mishi nashi a flasks daban nabila ta kai mishi can side d'insu,

Abun yana mata dad'i saboda zuciyar ta na samun sukuni, ta samu ta d'an rage rad'ad'in da takeyi mata, in har sun kasance wuri d'aya ko sun fito yawo gaba d'ayan su ba wanda yake kallon d'aya ballantana wani acikin su ya kula wani ranar kuwa zata nemi sukunin ta ta rasa, abdulshakur kullum fuskar shi a had'e take, bata ma baka dama ka masto kusa dashi balle kayi mishi magana.

Yau kowa ya shirya za su k'ara fita outing d'insu, tunda asuba samira da ta tashi cikinta ke mata ciwo, irin period cramps d'innan, kuma in ya tashi mata tana shan wahala soboda haka ta sanar da nabila baza ta iya zuwa ba, nabila kuwa tasan bak'ar azabar da take sha saboda haka bama ta misa mata ba, haka kuwa kowa ya watse bayan nabila ta ajiye mata wani pain reliever a kan bedside drawer d'inta, tace mata kada ta manta tasha in ta tashi daga bacci, aka barta ita kad'ai a cikin wannan mak'eken gida.

$$$$$$$$$$$$

Wani k'atan private beach sukayi renting gaba d'aya na wunin ranan, mazan na zaune mata na can wajan ruwa,

Shi kuwa abudulshakur tunda ya iso wurin ya samu wuri ya zauna akan wata beach chair ya saka shades d'inshi sannan ya d'auki wani book a gefe ya fara karantawa, duk da hankalin shi nakan book d'in amma kunanshi na sauraron abokan shi, yana ji shahid da al-ameen suka tashi, wai za suje wata unguwa su ga wani secondary school friend d'insu da suka dad'e basu gani ba, koda suka yi ma abdulshakur sallama, d'aga musu hannu yayi bai d'aga da kanshi daga kallan litaffin da yake ba,

Can bayan irin minti awa d'aya aka kira ismail a waya, shima mik'ewa yayi yace urgent call ne da zaiyi taking time bari ya samu wani wuri ya amsa, abdulshakur shima ko kallon shi baiyi ba dan yanzu gaba d'aya ya daina shiga sabgar ismail ko wata maganar zafi basa yi saboda tsabar haushin shi da yake ji, abokan su sun gane akwai wani abu a tsakinin su amma ba wanda yayi mishi maganar saboda baima basu fuska ba, ga basa san problem d'inshi,

Shima yana haka, ya d'an yi nisa a kartun shi yaji tashi wayar ta fara ringing, yana d'auka yaga sunan daddy a screen d'in, sauri yayi ya mik'e sannan ya latsa wannan greeen button d'in ya kai wayar kunan shi tare da yin sallama, daddy ne ya gaya mishi akwai wani important meeting da zasuyi ta zoom (wato video call) saboda akwai wasu mutane da yake so yayi briefing akan progress d'in company d'insu, yau zasu kama hanyar tafiya daga kano, abdulshakur tom yace mishi amma baya gida yanzu zai koma in har ya koma zai kira shi,

Yana kashe wayar da daddy, ya kalli abokan shi yace shi dai zai koma gida, suma d'in mik'ewa sukayi suka ce kawai bari su biyo shi tunda yamma ta fara yi ga tun safe suka fito,

Nasir ne yayi inda matan suke dan yayi musu magana, shi kuma abdulshakur gaba kawai yayi daman shi kad'ai ne a cikin motar shi.

Yana isa gida direct bedroom d'inshi ya nufa ya dauki MacBook d'inshi da wasu takardu sannan yayi pallor, ya fiso ya baje akan dinning dan zai fi zama comfortable.

Yana shiga parlor d'in har ya fara takawa yaji wani irin iho har sai da ya d'an firgita, tsayawa yayi ko zai k'ara jin ihon, ko kuma kunnan shi ne suka fara jiye mishi ba dai dai ba, k'ara jin wani ihon yayi wanda yama fi na daa, idanunshi yakai wurin garden, tabbas daga nan ihon yake, fara takawa yayi a hankali dan isa wurin, bud'e k'ofar yayi itama a hankali sannan ya shiga, da farko da ya shiga baiga komi ba tsabar girman garden d'in, ya dunk'a waige waige, harda zai juya ya koma ciki kawai ya k'ara jin wani irin rikitaccen iho, sauri yayi yakai kallonshi inda yaji,

Wata irin mutuwar tsaye abdulshakur yayi, baisan lokacin da ya saki duk kayan hannunshi ba, har MacBook d'inshi da takardun shi, tsayawa yayi cak baya mosti, jikinshi wani irin rawa ya fara, har hannuwanshi da k'afafun shi,  ji yake zuciyar shi na taso mishi har mak'ogaron shi bayan bugawar da take kamar zata tsage a cikin ki'rjinshi, idanunshi sun cika taf da k'walla tsabar tashin hankalin da yake gani a gaban shi,

Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un ya fara ambata a k'asan ranshi, a lokacin har hawaye sun fara zuba a fuskar shi, idannunshi sun rik'id'a sun zama jaa ja wur,

K'ara wani ihon akai, a lokacin ya dawo daga duniyar da yake, taku d'aya , taku biyu, taku uku, haka ya fara takawa, sannan kuma can ya fara gudu, gudu yake dan yayi saurin isa wurin ga Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un da take fita daga bakin shi a fili k'arara kowa naji.

(Me kuwa abdulshakur ya gani da ya tada mishi da hankali haka 🤔

Anyways.... I will start to rush things from now onwards and don't forget to vote. Xoxo ❤️)

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now