Chapter twenty-four

1.6K 163 1
                                    

(This chapter is kinda long, and duka nayi ta akan point of view d'in abudulshakur, Allah yasa tayi muku dadi)

Yau ya tashi wani iri yake jin jikinshi, duk ba k'wari ko kuzari, ji yake kamar bashi da lafiya, jiya bayan ya dawo daga kai lefin khalifa kawai ya tarar da ya zainab da ya khadija da y'ayansu a gida har su mommy basu dan da zuwan su ba, wai kawai surprising d'insu suka yi,

Khadija na da y'ayaya uku a yanzu da huda, haidar da husna ita ce auta bata wuce shekara biyu ba, sai zainab nada y'aya biyu, ni'ima da na'im,

Duk da yanzun yana side d'in su khadija wanda yanan a gidan sai sun zo ake bud'ewa a gera musu shi, yana zaune akan kujera a parlor husna na kan cinyar shi, na'im kuma yana gaban shi da toys d'in pj masks d'inshi yana ta zuba mishi surutu da labarai kala kala, shi kuma sai murmushi yake mishi duk da baya jin dad'in jikin shi, yana mutuk'ar san yara kowa ya sanshi da wannan.

Huda ce ta fad'o parlor din daga cikin d'aki tayi wurin uncle abdul da yake haka suke ce mai dan ta karb'i husna da sa mata kaya dan kuwa dukkan family d'in fita za suyi lunch,

Daman kwana uku za suyi jibi zasu tafi dan flight d'in na safe ne so suke gobe kawai gaishe gaishe da ziyara za suyi yau kuma gaba d'aya time d'insu na family d'in su ne.

Abdulshakur shikam a shirya yake, cikin gray jeans da gray shirt sannan da blue jeans jacket yayi mutuk'ar kyau, ga k'amshi dake tashi a jiki shi ko ta Ina,

K'ara kallon na'im yayi, yana suraron shi, atleast yana d'an rage mishi damuwa,

"Na'im wai me yasa ka fiya surutu ne uncle abdul d'in ma baza ka kalle shi ba da shirman labarikan ka na cartoons, shi da bama ya kallo" ni'ima da ke shirin samun wuri ta zauna kusa da abdulshakur ta fad'a harda d'an dungure ma k'anin nata kai,

Abdulshakur kallanta yayi shima ya d'an rank'washe ta akanta har sai da tayi k'ara,

"Ke dai babbar kabo ce, ace kullum da tilon k'anin ki zaki dunk'a fad'a ko kuma tsokana, haka kika ga maama (mamanta) na mun iye" muryarshi dauke da wasa duk da idanshi ya nuna he's very serious

Ni'ima narai narai ta fara yi da ido tana so ta fara kuka,

"Kada ki fara shirin kuka kullum sai na miki fad'a akan ki dunk'a jan baby brother d'inki a jiki amma ba abunda kika sani sai bullying d'inshi, in wasu suka ganki kinayi ai suma yi mishi za suyi" zainab ta gaya ma y'ar tata yayin da khadija da huda dake dauk'e da husna a hannunta suna biya a bayan ta dukan su sun shirya sunyi kyau,

Na'im ne yayi saurin zuwa ya rungume maman tashi itama shafa kanshi tayi,

Ni'ima da ke kallan su har suka k'arasa shigowa pallor d'in tace "tabd'i ai wallahi ba wanda zai tab'a mun k'anina a duniyar nan in k'alle shi, ni kad'ai zan iya cin zalin shi,

Yadda tayi maganar ya mutuk'ar bawa kowa na wurin dariya, har abdulshakur sai da yayi dariya sosai dukda halin da yake ciki, shikam yaran yanzu idanun su a bud'e yake ga bakin masifa

"Wannan bakin naki" ya fad'a ma ni'ima tare da had'a duka lips d'inta ya jaa, murmushi dukkan su suka k'ara saki

Amal da amra suka shigo, duk suka bi kowa da kallo,

"Me ya faru ne nagan ku duka kuna washe hak'ura" amra ta fad'a ita fuskar ta dauke da murmushi duk da bata san na mene ba,

Amra ce ta katse huda me shirin fara bama anty Amal labari, ta sanar dasu mommy da daddy na waje na jira,

Abdulshakur mik'ewaa yayi sannan yace "wanda za subi motata suyi sauri" sannan ya fice.

$$$$$$$$$$

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now