Chapter sixteen

1.6K 164 1
                                    

Abdulshakur ne da abokan shi baje a k'asa a gidan Al-ameen, duka squad dinsu kowa ya hallara, wasu na gefe na playing PlayStation , wasu na chess, wasu na hira da dai sauran su,

wai duk sun zo ne dan a fara planning bikin khalifa da ya rage nan da wata biyu da rabi, me yakon suyi abunda ya kawo so amma tunda suka zo, wajan karfe hudu kawai hayaniya ake har yanzu da karfe tara tayi, abun ya fara b'ata mishi rai, tunda ya shigo gidan yaga baza ai abun arziki ba yayi gefe ya zauna, sai mubarak da suke hira jefi jefi,

nasir ne ya taso daga inda yake ya zo kusa da abdulshakur ya zauna, yake ce mishi, "for 5 hours muna zaune a nan ba abunda muka tsinana, tomorrow is monday I'm very sure dukkan mu muna da abun yi and wasun mu nada iyali, time na kure wa in bamuyi abun nan yau ba I don't know when zamu samu muyi, dan Allah talk to them, suna d'an jin maganar ka",

juyawa ya dubi pallor din da abokanan nashi ke zaune, sannan ya fara, "Guys, guys" aiko yaci sa'a dukkan su sun juyo sun kalle shi, "I think ya kamata muyi abunda ya kawo dan time na k'urewa"

ya d'auka baza su kula shi ba, can kuma kowa ya fara sa baki kan kice me har sun gama planning abunda za suyi a matsayin su na abokanan ango har wani trip sukayi shirya da kawayen amarya da ita ma amaryar kanta irin sati biyu kan a fara biki, gashi ma sune za sukai lefe shi kuma ana saura wata d'aya biki, suna gama abunda suke, kowa ya kama hanyar gida lokacin karfe 11 tayi.

$$$$$$$$$$

Ismail ne ya ajiye abdulshakur a gida, a gajiya yake sosai ya rasa me yayi da yasa mishi gajiya, bud'e kofan pallor dinshi yayi,

yana shiga yayi sallama da kayan da samira ta aiko mishi da suke baje akan carpet, ya ma manta haka ya barsu a wurin saboda yana sauri, murmushi yayi sannan ya samu wuri kusa dasu ya zauna,

k'ura wa kayin ido yayi, kwata kwata ba taste dinshi bane, amma kuma yana so ya ajiye su saboda ita ce ta siyo mishi, zab'inta ne, yanzu shi mai san duk abunda zai had'a shi da ita ne komai k'ank'antar shi,

fara jawo kayan yayi, ya ware shirts guda hud'u, jeans guda biyu, jackets guda hud'u suma, belts, ties da shades guda bir biyu, sannan ya ajiye su a gefe, way'annan sune abunda ya keji zai iya sakawa, gobe in zai fita office zai ma securities din gidan maganar suzo su dauki sauran dan ba abunda zaiyi da su,

tashi yayi ya nufi bedroom dinshi, kayan jikin shi ya cire sannan ya fad'a bathroom, sai da yayi wanka sannan ya fito, wun wurin standing mirror dinshi yayi, gashin kanshi yake goge wa da towel din hannun shi, duka duka yaushe yayi aski, amma suma ta fito ta cika mishi kanshi ga sajan shi ya k'ara fitowa, yana gamawa yayi hanyar closet dinshi kaya marasa nauyi ya saka ajikin shi bayan ya feshe jikin shi ta turarruka masu dad'in kamshi,

remote ya dauka yayi dimming fitulun d'akin sannan ya hau kan gado, wayan shi ya kunna sannan yakai hannushi kan message din da samira ta aiko mishi, k'ara karantawa yayi sannan ya saki murmushi, tuna duk abunda ya faru yayi d'aya bayan d'aya, wayar su, message dinta, kayan da ta siyo, k'ara sakin wani murmushin yayi, zuwa yayi kan recording din wayar su da yayi d'azu ya kunna, bala'in so yake yaji muryarta in ba haka ba bazai tab'a iya barci ba,

yana saka recording din yaji wani irin farin ciki ya kama shi, in tana magana kamar wak'a take rera wa, muryarta akwai dad'in sauraro, haka yayi ta playing yana murmushi baisan sanda bacci yayi gaba dashi ba.

$$$$$$$$$$$

Yanzu aji d'aya ne ya rage musu su gama da classes dinsu na yau, ta gaji sosai saboda tun 8 take makaranta,

Nabila ta jata gefe tunda suka gama class dinsu na farko, ta bata hakuri sosai abunda tayi mata, tace mata wallahi tana fita tayi dansanin duk abubuwan da ta gaya mata tasan samira baza ta tab'a cutar da ita ba, tana kuka tana bata hakuri, samira itama kukan take tare da jawo ta jikin ta, tasan so ne ya sa tayi abinda tayi, ta gane kuma bata dauke she da zafi ba, sai da suka gama shan kukan su sannan suka goge hawayen su suka koma inda suka baro friend dinsu farida, ita tana ganin su bakinta ta saka tsabar mamaki, sannan ta tambaye so ko kuka sukai saboda yadda idanun su sukayi ja, dariya suka saki sannan suka ce mata ai ya rigada ya wuce, farida kuwa tasan halinsu shi yasa bama ta k'ara tambayar su ba,

Yanzu suna zaune su uku a wani restaurant suna cin abinci, basu samu sunci lunch ba saboda classes dinsu, samira ce ta kalli farida, "ke, kince mun akwai abunda zaki gaya mun muka had'u a school, tunda muka zo aji muke shiyasa ban tambaye ki ba, yanzu gaya mana muna jinki",

farida ta ajiye spoon din da ke hannun ta sannan ta tattaro dukkan nutsuwarta ta kalli samira da nabila da suma kallanta suke, "Aure zanyi nan da december"

shiru sukayi ba wanda yayi magana, an d'anyi sakwanni a haka, sannan samira da nabila suka saki wani ihu a tare, har mutanan da suke zauna a wurin sai da suka juyo suka kalle su wasu ma harda daka musu harara, amma ina su ko ajikin su, bayan sunyi ihun suka mik'e shima a tare sukayi kan farida suka rungume, farida itama rungume su tayi tana sakin dariya, sai da suka gama sannan suka koma wurin su suka zauna, nabila ce ta fara magana "me sunan shi, a ina yake, a ina kuka had'u" samira binta tayi da kallo "ke yanzu har inda suka had'u sai sun gaya miki?" Sannan ta kalli farida " share da fara gaya mana sunan shi mana k'awata kinyi shiru" farida dake faman dariya ce tace musu "Maybe nabila ta sanshi saboda abokin saurayin ta ne abdulshakur" tana fad'an sunan gaban samira yayi wata mummunar fad'uwa, abunda ke bata haushi shine duk sanda akai maganar shi to dole sai gabanta ya fad'i, bayan tama manta dashi a duniya gaba d'aya, ita ta kasa gane kan abun,

muryar nabila taji tana cewa "eh kuwa, nasan wasu a cikin friends dinshi wanne daga ciki?" farida na murmushi tace "sunan shi khalifa" tana fad'an suna samira takai duban ta ga nabila, ta tabbata bata san sunan abokanan abdulshakur ba balle har tasan fiskar su, zai iya yuwa abokanan shi sun santa amma ita ba lallai tasan su ba, yaushe ma suke had'uwa ko waya da har zata san wani abu game dashi, ga shegen girman da yayi mishi yawa, da nabila zata ji shawarar ta da ta rabu dashi saboda san shi ba abunda yake tsinana mata sai dai whalala, nabila ce ta k'ara da "eh kuwa nasan khalifa" nan yira ta tsarge tsakanin kawayen su uku, harda cewa zasu had'u da weekend su fara planning biki.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now