Chapter fifteen

1.6K 181 2
                                    

Samira ta shirya cikin wata free bubu jaa ta material, sannan ta dauko bak'in mayafi ta saka a kai, handbag dinta ta dauka tare dayin dak'in mama dan ta sanar da ita zata fita, tana shiga taga safiya zaune a k'asa tana karanta wani english novel, wata harara ta dalla mata sannan takai idanun ta kan mama, ce mata tayi zata fita kan ma ayi magrib insha Allah zata dawo, mama tace mata a dawo lafiya, tana fita ta fad'a cikin mota tayi hanyar boutique.

Expensive boutique din da ake ji dashi a kano taje, da ta isa ta samu wuri tayi parking motar ta sannan ta fito, takawa ta fara har ta is cikin wurin, wajan da aka tanada musamman na maza ta shiga, nan ta fara siyayya, expensive shirts ne, expensive jeans ne, expensive shoes ne, har da su ties da glasses/shades, haka dai duk abunda ta gani dauka take, wala me kyau wala mara kyau ita ko a jikin ta, tana gama wa tayi wurin cashier take yiyi mata bill dinta 500k cif, daman abunda take so kenan, samira ta bud'e jakarta da dauka atm card dinta ta dank'a mishi, binta yayi da kallo yana wage hak'ora

"hajia duk wanene mijinki gaskiya ya cab'a irin wannan kaya haka da kika siya mishi, aiko bazday(birthday) dinshi albarka yasin"

kallon shi tayi sannan ta daka mishi wata muguwar harara, bata bashi amsa ba saboda irin way'annan mutane masu shegen surutu basu canci a amsa musu ba, da yaga bata da niyar kulashi, shi ne ya kira wasu yara daga gefe ya umarci su da su daukar mata kayan sukai mata mota, haka suka fara jidar paper bags din masu dauk'e da logo din boutique  din suna kaiwa motar ta, ita kuma tana binsu a baya, boot din motar ta bude musu nan suka fara zuba kayan, sai ta tabbatar sun gama sun kulle boot din sannan ta  bud'e jakarta ta zaro 1000 ta basu, godiya suka shiga yi mata har suka bar wajan, samira shiga motar ta tayi ta zauna, yanzu sai me kuma?, ina zata san gidan su shakur, ga ba dama ta kira nabila ta tambaye ta, tasan dai a bompai suke kowa ma a kano yasan wannan amma bata san tak'a maimai gidan ba, zuciyarta ce tace kawai kije unguwar kya tambaya, haka ta fara tuk'in mota kuwa har ta isa uguwar,


Tana shiga ta samu wasu mutane zaune a k'ofar wani gida, sallama tayi musu sannan ta had'a da tambaya sun san gidan yusuf ashaka, dariya suka shiga yi, wanda baisan gidan shi a unguwar nan ba ai sai dai bak'o, can suka fara mata kwatance, tako ci sa'a ta gane, haka ta k'arasa har ta isa gidan. Samira na isa ta samu wuri tayi parking, bakinta ta hangame saboda abun da ta ke gani a gabanta, makeken gida ne bari kawai na kirashi da mansion, gidan ya had'u bazan tab'a iya kwatanta muku ba, samira tace hmm, ji gida kamar baza'a a mutu ba, shi ya sa aka ce duk kano ba gida irin wannan kuma a gaskiya ba'ai k'arya ba, seatbelt dinta ta cire ta fara shirin fitowa, k'arasawa tayi wurin securities din da suke zaune a gaban mak'eken gate din, yi musu sallama tayi, sannan tace dan Allah ta kawo sak'o wurin abdulshakur, nan suka shiga yi mata tamboyoyi itama ta basu amsa, tare da tsaro karyaryakun ta, sunko yarda da ita, har suka ce bari su kirashi a waya tace ba ma sai sunyi ba kawai su biyota su karb'i sakon dan kayan suna da yawa, haka suka k'arasa motar ta, ita kuma ta bude musu boot, sai da suka kwashe komai sannan tayi musu sallama hadda cewa a gaishe shi, ta hau motar ta tayi gaba.


Abdulshakur tunda samira tayi mishi text din yake dariya, dariya yake yi sosai ya kasa dai na wa, ko yanzu da ya tashi yana shirin fita sai da ya tsaya da shirin da yake yayi dariyar shi me isar shi da ya tuna da message dinta, kwata kwata message din da ta mishi bai b'ata mishi rai ba, in fact wani farin ciki ya sa shi da anushuwa, ya tabbata da wani ne daban yayi attempting gaya mishi way'annan maganganu da sai yayi dana sanin zuwa duniya, kullum tana cikin bashi mamaki, bai tab'a zata mace zata yi mishi haka ba a rayuwar shi, ya kara jin wani feeling ya mamaye duka gab'ob'in jikin shi, tana mutuk'ar burgeshi, yazai yi da ita, tana so ta zama babban abun dake sashi farin ciki a rayuwarshi, bayan ya gama shirin shi tsab, cikin blue jeans da sky blue shirt had'e da d'ora white jacket a sama wacce tasha buttons da rolex watch din shi a hannun shi, yayi masifar kyau, ga ya kasa boye murmushin shi da yake k'ara mai azababban kyau, daukan wayar shi yayi ya k'ara duba text din ta tayi mai,

"1) In ma so kake ka nuna mun ni talaka ce to ka sani, ina da rufin asiri na, ban tab'a rokar wani, wani abuba a duniya kuma bazan fara daga kanka ba, ni ba irin matan da suke bin maza saboda kudi bace, wallahi ina bala'in jin haushin matan da ke hauka akanka, ni wallahi tsoro fuskar ka take bani saboda kama kake min ta fatalwa, tunda ana sai da man blicin na tabbata ana sayar da man maida farar fata bak'i da zaka ji shawarata ka siya ka fara shafawa saboda akwai da yawa iri na da kallanka ke basu tsoro.
2)  ba ni na aika maka da account details dina ba, tunda nace maka nayi maka saboda Allah ne haka yake har zuciyata amma kuma da ka yarda da kar ya yarda duk ba damu na sukayi ba, saboda ba abunda zai k'ara had'a ni dakai a duniya, zan tabbata duk inda kake bana wajan, shawara ta ta biyu da zaka taimaki kanka ka rage girman kannan da yayi maka yawa shi zai kaika ya baro ka in har bakayi wasa ba
3) zan nuna maka ni wacce."

K'ara fashe wa yayi da dariya, harda hawaye yayi this time around, ya karanta message din yafi sau goma and duk lokacin da ya karanta sai yayi dariya ba yar karama ba, yana gani bai tab'a irin dariya ba kamar ta yau, yana cikin haka yaji ana kwad'a sallama daga wajen pallor dinshi, wayarshi ya saka a aljihu yayi hanyar waje, yana fita daga bedroom dinshi yaga securities sunkai hud'u a tsaya a k'ofar pallor dinshi da paper bags a hannun su, kallon su ya shiga yi idanun shi akwai alamar tambaya, wani daga cikin su ne ya fara magana

"yallabai wata mace ce ta kawo sak'on kaya tace a kawo maka"

Abdulshakur ci gaba yayi da binsu da kallo, wani ne ya k'ara cewa

"wai tace kai ne kayi order dinsu har gida, kuma tana sauri bamu tambayi sunanta ba, har cewa mukayi zamu kira ka tace mu barshi, kawai dai mu gaishe ka"

sa hannun shi yayi akan hab'ar sa kamar yana d'an nazari, shi dai yasan da hannun shi bai yi order wasu kaya ba,

"kuma ce muka tayi ni, sunana ta fad'a?" dukkan su suka d'aga kya alamun eh,

abudulshakur yad'an yi shiru na wasu sakwanni, wanda yayi maganar farko ne ya k'ara cewa

"wata doguwa, amma ba can ba, bak'a, bata da k'iba sosai, tanada b'ular hanci da manyan idanu"

ya k'arasa maganar da ka gane ta?, Abdulshakur hangame bakin sa yayi, harda zaro ido waje, tabbas samira suka kwatanta, amma kuma wana kaya ta kawo mishi?, da yaga ya bar securities din a tsaye, ya matsa musu tare da musu nuni da su shiga su ajiye kayan, suna gama ajiye wa suka kama hanyar fita, yana ganin su gama wucewa ya koma parlor tare da zama da akan kujera, can ya jawo bags din ya fara fito da kayan ciki, shirts da jeans yayi ta gani dasu jackets harda ties sai da ya gama duba komi tsab, sannan yabi kayan da suke baje akan carpet da kallo, tunani ya shiga yin tunani me yasa zata aiko mishi da kaya, can abun ya zo mai, kada ace duk 500,000 din da ya akai mata ta kashe mishi, shi ne abunda take nufi da zata nuna mishi ko ita wace?, dariya ya saki, wato tafi k'arfin kud'in da ya aika mata, tunda yak'i aika mata da account details dinshi shi ne tayi wannan, wata dariya ya k'ara saki, dariya yake sosai harda ruk'e cikin shi, yau dai ba abunda yake tunda ya tashi sai dariya yana cikin wannan yanayin yaji sallamar abokin shi ismail, yana shigowa cikin parlor din ya tsaya cak yana bin abdulshakur da kallo wanda yake ta faman dariya kamar tabbab'e,


"lafiya ka saka kaya a gabanka kana ta zuba wannan uban dariya haka?"

d'aga idanunshi yayi ya sauke akan
ismail, baima san yaushe ya shigo ba, still ya kasa controlling dariyar shi, sai can da aka d'an jima sannan abudulshakur ya tattro dukkan nutsuwan shi ya kalli abokin nashi,

"kada ka damu ba wani abu bane"

har lokacin da yayi maganar fuskar shi na dauk'e da farin ciki da raha, isamil ya dai kasa jurewa

"kasan ban tab'a ganin ka a haka ba sai yau, kullum fuskar ka na dauke da wannan serious and intimidating look din, wallahi kafi kyau a haka, da zaka ci gaba da irin wannan fara'ar ai da kowa yaji dad'i"

gyad'a kanshi yayi, hakika haka yake tunda ya had'u d samira rayuwarshi ta canza gaba d'aya, zai iya cewa ita kamar haske ce a cikin rayuwar shi, wani irin jinta yake acikin jinin jikinshi shi, dan yayi allkwari bazai tab'a gayawa abokanan shi mganarta ba da kuwa yau zai fayyace musu komi dukda baisan mai zai kira abun da yake ji ba game da ita, mik'e wa yayi yace ma da ismail,

"muje ko? nasan sauran sun gaji da jiran mu"

haka suka fito suna hira har suka isa inda ismail yayi parking dan yau a motar shi zasu fita baisan yin driving.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now