Chapter twenty-nine

1.4K 163 2
                                    

Dukkan su suna zaz zaune suna hira kawai suka ji sallama, farida ce ta mik'e sannan ta basu izinin shigo wa, haka sukayi ta shigo wa cikin pallor, samun wuri suka zauna sannan aka fara gaisawa da yin ya gajiya hanya,

Tun da suka shigo Samira ta lura ba abdulshakur, tambayar kanta ta fara ko me yasa be biyo su ba, ta san sun d'auko gajiya beci ace baya jin yunwa ba,

Khalifa ne ya fara magana yana amsa tambayoyin Samira kamar ya shiga cikin ranta ko tayi maganar a fili, sanarda su yayi abdulshakur na nan shigo wa ya d'an tsaya yin abu ne,

"Har ina shirin tambayar ku Ina ya shiga, sai gashi kuma ka fad'a mana" nabila tace fuskar ta d'auke da fara'a

Nan suka d'an yi wasa da dariya kafin suyi hanyar dinning d'in.

Tun da suka shiga Samira ta lura da irin kallon da ismail yake mata, tasan sarai yasan tasan yana kallonta amma ko kunya bai jiba, haka ya ci gaba da zuba mata kallo ko ajikin shi, duk hankalin sauran na kan hira ta tabbata basu lura ba, gabanta sai faman bugawa yake, idanunta na kan carpet d'in parlor d'in bata saka musu baki hira da suke saboda bama tasan me zata ce ba,

Gaba d'aya ta gaji da kallan da ismail yake mata ga jinta take a wani takure, a ce mutum ya dunk'a kallon ka haka sai kace maye, ko kunya baya ji kada mata wurin da suke zaune su ganshi, ya manta abun da ya faru d'azu airport ne abun kunya da ya shuka,

Sallama akayi da wata murya da ta dake kunnuwanta da kirjinta, wace ta fitar ta ita daga duniyar tinanin da take, jin wani abu tsi taji tunda kanta har zuwa tafin k'afarta, bata ankara ba kawai kanta yakai inda taji yo murya me dad'in gaske, idanunta suka sauka akan sa, ta sani sarai wane, ko magigin mutuwa take sai ta gane muryar shi, wata irin deep husky voice yake da ita da bata tab'a jinta wurin ko wane d'a namiji ba a duniya, lallai shakur daban ne, ba sa'an sa acikin maza,

Fuskar shi d'aure take yadda dai ya Saba, ko k'ad'an bashi da shirin sakar ta, nabila ce tayi sauri ta wuce dinning area ta jawo mishi kujera sai iyayinta take da ya zama mata aboki in har taga abdulshakur, ce mishi tayi yazo ya zauna daman shi suke jira muryar nan tata a mak'e ko dad'in ji babu,

Tana maganar abdulshakur ya sake had'e fuskar shi, kamar dai bazai biye mata sai can kuma yayi wurin ta, wani irin arnan murmushi nabila ta saki, duk abunnan dake faruwa gaba d'aya a idanun samira, tama manta wai wani ismail na zuba mata kallo, haka sauran dake wurin bama su san suna yi ba saboda wata irin hira da suke, Allah ma yasa sun san abdulshakur d'in ya shigo,

Samira k'ara saukar da kanta tayi, ta shiga yin wasa ta yatsun ta, wani irin zafi zuciyarta take mata, bata da right d'in da zatayi kishi da abun da ba nata ba, abun da ba mallakin ta ba kuma abun da yafi k'arfinta, tun farko abdulshakur ba nata bane, na aminyar ta ne, me yasa zuciyar ya take shirin kwaso abunda yafi k'arfinta, me yasa zuciyar ta keson saka kanta cikin kaunci da rad'ad'in rayuwa, me yasa zuciyar ta ke neman jefa ta acikin rayuwa me munun gaske, dama d'an Adam zai iya rayuwa ba zuciya da sai ta sadaukar da tata, bata cancanci tayi ma nabila haka ba, bata ma so tayi tunanin ranar da nabila zata gano sirrin zuciyarta, bama ta so ta kai wurin,

Asiya ce ta tab'a ta har sai da ta d'an firgita,

"Kowa ya gama hallara a dinning ke ake jira"

Aikuwa Samira na kai dubanta ga parlor d'in ta ganshi wayam ba kowa ta k'ara kai dubanta da dinning ta gansu duka a zaune matan na tsayie na serving d'insu, sauri tayi ta tashi, ta zauna tana zuba tunani bama tasan sun tashi ba,

Tana isa dinning area d'in idanta akan abudulshakur ya sauka wanda yake tsakurar abincin shi a nitse da kasaita ga wani kwarjini da ya rufe shi, duban kallanta tayi ta sauran mazan da suke faman zuba loma ko ajikin su,

Wai yaushe ta fara comparing (had'a) abdulshakur da sauran maza ne?

Share nabila tayi da ta zauna kusa da abudulshakur sai turo mishi jikinta take da fuskar ta, be dame ta ba zubar da mutuncin ta da take yi a gaban idanun kowa, shi gogan naku ko kad'an bai juyo ido ya kalle ta ba kamar bata wurin,

Duk wurin a cike yake kowa ya samu seat ya zauna sai kusa da ismail me kad'ai empty, ita kuwa kwata kwata hankalin ta bai kwanta dashi ba, amma haka ta daure ta zauna, shi kuwa yana ganinta ya fara wage hak'ora shi yayi serving d'inta da kanshi duk da ta nuna mishi bata so, ga ya cika mata kunne da magana, ji take yi kamar ta kurma iho, ita ko taga ta kanta.

$$$$$$$$$$$

Wani irin takaici da bak'in ciki ne suka cika mishi zuciya, ga nabila dake faman takura wa rayuwar shi, ga Ismail da yake san yaga ya haukace, abubuwa goma da ashirin sun taru sun yi mishi yawa, gani yake yanzu duk duniya ba wanda ya tsana yake jin haushi kamar ismail, dukda tunda ya fara cin abinci bai d'aga ya kalli kowa ba amma gaba d'aya hankalin shi nakan samira da ismail, wani irin takaici yake ji, ace mutum duk yabi ya takura wa yarinya haka kawai,

Mik'e wa yayi daga zaman da yake bayan ya ajiye spoon d'in hannun shi, bazai iya zama a nan wurin ba ko na sakwan d'aya ne jinshi yake kamar baya nimfashi, kallan y'an wurin yayi yace musu shi dai ya k'oshi zai koma inda ya fito wato side d'in su, ya d'an saki fuskar shi yayi ma matan godiya saboda a ganinshi sun cancanci hakan yana juyawa wa zai bar wurin ya k'ara had'e fuskar shi, ko kula nabila bai yiba dake faman yi mishi magana balle har yakai duban shi inda samira da ismail suke a zaune.

Yana fita nabila tace ta k'oshi itama sannan tabi bayan shi,

sukayi mazan wurin sai da suka ci suka k'oshi sannan sukayi hamdala, k'ara komawa pallor d'in matan sukayi suka saka wata sabuwar hira basu suka tafi ba sai da la'asar, koma har lokacin nabila bata dawo ba daga bin abudulshakur d'in da tayi, kafin suka tafi sai da suka sanar da matan bayan isha zasu d'an je walk cikin unguwar in har za suje kafin gobe su fara outing d'insu, suma sun ce musu eh suka nuna yardar su da kyar ismail ya iya barin wurin saboda Samira sauran nayi ta mishi dariya.

(Wayyo, littafin nan gaba d'aya baya sauri, in na tuna akwai abu buwa da yawa a nan gaba sai gabana ya fad'i 😭😂 yau ma wallahi na k'ara wata tafiyar duk a gajiya nake shi yasa banyi ma updating da wuri ba )

BA KYAU BA ✔️Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu