Chapter forty

1.6K 205 5
                                    

Samira da take kwance a gadon ta na asibiti, ita kanta bata san rashin lafiyar tata har takai da sai da aka yi admitting dinta a asibiti, tana ji doctor din yana ma ya muazzam bayani, yadda wasu abubwa na jikinta sunyi low, calcium d'inta, blood pressure d'inta, ga kuma malaria ya gaya mishi magungunan da zai siyo, ya muazzam da safiya ne suka fita wai ita ta k'arbo maganin shi kuwa zai koma gida ya taho musu da abinda suke buk'ata dan zasuyi kwana uku a asibiti, suna fita samira ta kulle idanunta sai bacci, daman ga jiki ba kwari,

Tana bud'e idanunta bayan ta tashi taga ba koma a d'akin, kai idanunta tayi kan agogo taga k'arfe hud'u da rabi, har yanzu basu dawo bane ta fad'i a ranta,

"Kin tashi?" Jin maganar taya bata san daga ina ba, sauri tayi ta kai kanta inda taji muryar ta taga abdulshakur ya kafa mata idu, yana tsaya ya saka hannayen shi a cikin aljihun wandon shi, gaban tane yayi wata mummunar fad'uwa, san da take mishi har ya fara sata gane  ne, tasan ba abdulshakur bane saboda mene zai kawo shi nan, taya ma yasan tana asibiti, rufe idannunta tayi ta fara girgiza kanta, anya bata fara zarewa ba, ji tayi anyi dariya, ta k'ara saurin bude idanunta ta ganshi a gabanta, ya ci gaba da zuba mata kallo, wannan kallon nashi da yake sata susuce wa,

"Ba mafarki kike ba, nine a tsaye" yayi maganar ciki zolaya, tare da mik'a mata hannun shi, "ga hannu na tab'a in baki yarda dani ba"

Zuciyar Samira bugawa take, taya yasan tana asibiti, tasan a gidan su ba wanda ya sanshi balle har a kira shi a waya a gaya mishi, so take ta raba zuciyar ta dashi amma abun na so ya zama me wuya, dan ta lura yanzu duk inda take yana nan, fuskar ta tayi saurin had'e wa sannan itama ta kafa mishi ido, tana sa kwayar idanunta a cikin nashi zuciyarta ta k'ara harba wa, wayyo wannan masifar san nashi zai kaita ya baro ta, so take tayi mishi masifa amma ta kasa, tsabar yadda yake kallanta, laulausan idanun nashi sunyi narai narai da su, ga smiling din da yake ta gefan baki, sauri tayi ta kwada kanta ta taga zuciyar ta nason cin galaba akanta,

"Ai ni nasan yadda kika dunk'a yin kuka shekaranjiya ba tsaya wa sai kinyi rashin lafiya, kuma d'akin ku a lagos akwai sauro ne har ya cije ki malaria ya kama mun ke?"

Dan Allah taya zata daina sanshi, bayan yadda yake nuna kulawar shi a gareta, dama abdulshakur d'in da zai dawo, me girman kai wanda kwata kwata baya ma bi ta kanta, da cire shi a zuciyarta zai fi mata komi sauki, bud'e bakinta ta fara danyin magana da taga kallon da yake mata yayi yawa,  ko kifta idanunshi baya yi,

"Me kake yi anan" ta tambaye shi amma har lokacin idanunta na gefe, suna kallon fridge din dake ajiye a d'akin,

"Na zo wurin budurwata, doctor dinki da nurses dinki already sun san ni saurayin ki ne, haka dai sukayi assuming ni kuwa bani da intention d'in correcting din su" yayi maganar da serious face d'inshi,

Samira sauri tayi ta kai idanunta wajan shi, me yake nufi, yaushe har suka saba haka, nabila fa?, me yasa be damu da ita ba, dole ta nuna mishi matsayin shi a wurin ta yadda zaiyi saurin rabuwa da ita ya koma kan nabila,

"Kaje ka gaya musu ni ba budurwar ka bace kuma bazan tab'a zama budurwar ka ba, banga abunda kake yi a asibitin nan ba saboda ba abunda ya had'a ni da kai, dan haka ka kwashi kafafun ka kayi waje kada ka sake dawowa" ta fad'a muryar ta a had'e,

Tana gani fuskarshi ta fara canzawa, idanunshi suka fara yin jaa, lumshe su yayi sai da yayi kusan minti d'aya, sannan ya bud'e sun dawo yadda suke, bai ce mata komi ba ya juya, ita tasan ranshi a mugun bace yake, bin bayan shi tayi da kallo, ji take kamar ta tashi da ruga ta k'ankame shi ajikinta ta bashi hak'urin maganganun da ta gaya mishi, wallahi basu kai zuci ba, bata son baccin ranshi, kwalla ce ta cika idanunta da taga har yakai bakin ko'fa zai fita, ji take kamar ta kwala iho tsabar yadda zuciyar ta ke yi mata ciwo da rad'ad'i, ta tsani ganin shi a cikin yanayin nan, amma kuma kullum ita ce silla, jikinta yayi wani irin sanyi ga daman mata da lafiya, gaba d'aya ba kuzari a jikinta, sauri tayi ta kulle idanunta dan bama taso taga fitar shi, jira take taji k'arar kulle k'ofa amma taji shiru, bud'e idanunta tayi ta k'ara ganin shi a tsakiyar d'akin, fuskarshi ta koma abun tausayi, idanunshi sunyi jajawur,

"Duk lokacin da kika gaya mun irin wannan maganganun ji nake kamar an d'auki katon k'arfe an saka shi acikin wuta har sai da yayi jaa sannan aka d'od'ana mun a cikin zuciyata" yayi maganar a hankali kamar bashi ba, yana gamawa ya juya zai fita sai gashi an turo k'ofa,

Ya muazzam ne da safiya, cirko, cirko suka tsaya suna kallan abdulshakur wanda yayi saurin sakin fuskar shi, ya mik'awa muazzam hannu, shima d'in hannu ya mik'a mishi fuskar shi d'auke da alamar tambaya, abdulshakur dake wa yayi ya kalle yayan samira yace dan Allah suje waje zai gaya mishi wani abu, muazzam ajiye kayan hannushi yayi sannan yabi bayan shi,

Suna kulle k'ofar safiya ta daka wani wawwan tsalle, amma Samira bama ta d'ago ta kalle ta ba, hankalinta har lokacin nakan k'ofa ta zuba mata kallo, ga hawaye na kwarara a fuskarta,

"Kuka kike yi?" Tambayar da safiya tayi mata ce ta saka ta saurin dawowa daga duniyar tunani da take, hannunta ta saka ta share hawayen da bama tasan sun zuba ba, sannan ta maida hankalinta kan k'anwarta,

"Nace me ABDULSHAKUR YUSUF ASHAKA yake a d'akin ki na asibiti?,"

Samira banza tayi da ita, ta tsani surutun safiya,

"Kukan da kike yi, akwai wani abu a tsakanin ku ko?, tsaya kowa ma ya gani yasani saboda da muka shigo akwai wannan tension d'in a cikin d'akin nan, dan Allah a ina kika sanshi, dole na kira kawaye na na fad'a misu nagan shi yau, wayyo dad'i"

Safiya ta dunk'a zuba surutu da basu da kan gado, samira da ta gaji da hararar ta kawai taja bargonta ta rufe kanta, yanzu ta shiga uku, safiya baza ta tab'a k'elleta ba,

Hawaye ne masu zafi suka sake zuba a fuskarta, ba abunda ke cikin kanta irin maganar k'arshe da abudulshakur yayi mata kansu safiya su shigo, abun tausayi k'ara ra a fuskar shi, dole tayi sauri taja mishi burki, ko badan kowa ba dan shi, ko ta samu ta daina hurting d'inshi,

Tana ji aka k'ara bud'e k'ofa aka shigo, ya muazzam ne ya tambayi safiya tayi bacci, safiya tace bata sani ba, yace to shi zai wuce, in ta tashi ta gaya mata gwaggo da mama zasu zo da daddare yana gama f'ad'a ya fita, ji take kamar ta tashi ta bishi ta tambaye shi me abdulshakur ya gaya mishi, tana kwance tana sak'e sak'e bata san lokacin da bacci yayi gaba da ita ba.

Tana farkawa ta ga d'akin a cike, mama, Gwaggo, ya murjanatu da safiya har baba tabawa, suna magana a hankali, kina ji kinsan dan basa so su tashe ta ne, idanunta na ya koma kan iman wacce take yawanta a cikin d'akin, wani farin ciki samira taji d'ata ganta,

"An iman d'ita zo nan kinji" maganar da tayi ne ya saka kowa a d'akin juyowa ya kalleta, suna gani ta tashi dukan su suka fara mik'ewa suka yi kanta, suna mata ya jiki, samira ba abunda take in banda murmushi ga ta d'ora iman a cinyarta, tana san family d'inta sosai,

"Na rantse da tabawa da sauko k'asa a guje tana fad'in samira ta suma, sai da nima naji jiri, na d'auka zuciyata bugawa zatai yadda ta dunk'a bugawa" Gwaggo ta fad'a, samira ba abunda take sai murmushi,

"Mene ya same ki kika saka tunani a ranki haka har jinin ki yayi wannan irin low d'in, wani abu ne ya faru a lagos ne" ya murjanatu ta tambaye ta, gaban Samira ne yayi fad'i, ga zuciyarta da ta fara bugawa, tambayar ta bata so ayi mata kenan, saboda baza ta tab'a iya bada amsa ba,

"Zata f'ada ne, wannan yarinyar me shegen zurfin ciki tsiya" Gwaggo ta yi maganar rai a bacce,

Mama ce tayi saurin cewa ya isa haka, a kyelta taji sauki tukunna ayi mata dukan tambayoyin, samira wani dadi taji harda yin ajiyar zuciya da taga kowa yaji maganar mama,

Nurse ce ta shigo d'akin, ta canza ma Samira drip d'inta sannan tayi mata allura har guda uku tana gamawa ta fita, haka su mama suka saka mata fruits a gabanta suka ce sai ta sha, dan sunsan baza taci abinci ba shi yasa bama suyi mata tayi ba, haka Samira ta daure tasha ba laifi,

Dukan su suna zaune suna hira suka k'ara ji an jawo k'ofa tare da yin sallama, gaba d'aya hankalin su ya koma kan k'ofar suna jira su ga wane zai shigo,

Gaban Samira ne yayi wata irin muguwar fad'uwa, zuciyarta ta fara bugawa a kirjinta kamar zata fashe, ta zaro manyan idanunta waje, me abdulshakur yake anan, sake dawowa yayi bata ce mishi bata so ta k'ara ganin shi ba, gashi yanzu duk y'an gidan su na wurin, ta shiga uku ya zatayi yanzu.

(Double update!!!

Please vote and share ♥️♥️)

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now