Chapter fifty-three

1.9K 189 7
                                    

Tun biki saura sati biyu Samira ta hana abdulshakur zuwa ganinta, ba irin magiyar da nacin da baiyi mata ba, ba kuma da wanda bai had'ata ba har mommy da su ya zainab sai da ya saka dan Allah su kira ta su bata hakuri ta daina azabtar dashi haka, da suka kirata k'ara zuga ta sukayi suka ce kawai ta kyale shi, wata rana sai da ya zo ya k'araci zaman shi a d'akin ya muazzam amma baza ta tab'a fitowa ba, ga mama da antya larai matar yayan mama sun duk'ufa wajan yi mata gyaran jiki, ba kallar kayan da basa jik'ata dashi, yanzu ko kaya samira ta saka sai kamshi ya zauna a jikin su, duk wurin da ta dosa kawai k'amshi kake ji, bayan wani laushi da fatar da tayi ga bak'in fatar jikinta ya k'ara kyau, ranar da farida me da'uke da ciki wata uku, tazo ganinta sai da tayi ta santi tace in har abdulshakur ya ganta sai ta rikita mishi kwakwalwa haka sukayi ta dariya.

Duk Africa tasan an kusa bikin Abdulshakur Yusuf Ashaka, kullum shine zancen a gidan radio ta tv, kowa jira yake a fara biki. Ko lefanta ya khadija da ya Zainab ne suka je Dubai suka had'o mata shi, ya kuwa tsaru iya tsaruwa an kashe mak'udan kud'i, akwati ashirin da hud'u kowa yazo gani sai ya tafi yana santi.

Yau ne kamu, gaba d'aya gidan a cike yake mak'il da jama'a kuma wai a haka ba a gidan su za ayi event d'in ba, dukda abdulshakur ya d'auke musu nauyin komi mama dai tace ya barta tayi kamunta, dan haka yau duk y'an uwansu na nesa da na kusa sun hallara gidan, tsabar jama'a samira ta tattara ta bar gidan ta koma gidan ya murjanatu, dukda shirin biki na d'auke mata kewa tayi bala'in missing shakur d'inta, wayar da suke bata tab'a isar su, murna ce fal cikinta yau zata ganshi a wurin bikin dukda ba wani dad'e wa zaiyi ba sai ma kusan k'arshe zai zo dan kawai a d'auki pictures,

Make up artist ta saka ta a gaba zai zane fuskar ta take yi, ga wayarta ta bata bar k'ara ba amma bata da shirin d'auka, tasan sarai shakur ne, ta gaya mishi waya baza ta yiwu ba ana mata make up amma sam yak'i ji, ya murjantu da su ya fiddausi cousin d'inta dake zaune a wurin sai tsiya suke mishi, ya fiddausi ce tace,

"Akan Samira za'a fara amaryar da ana event d'inta tana waya da miji, saboda abdulshakur bazai tab'a yin hakuri ba"

Dariya suka saki gaba d'ayan su, ya Murjantu ta k'ara da,

"Jiya har kusan asuba naji su suna waya, kinsan dana zo tayar da ita salla kawai naga waya a kunne kati na ta tafiya basu katse ba, gashi ita tana ta sharar bacci, dana d'auki wayar na saka a kunne naji shima yana ta nishi alamun baccin yake, sai da na koma d'aki na bama baban iman labari dan abun akwai dariya"

Wannan karan har make up artist d'in sai da ta dakata da kwaliyar tayi dariya, samira kuwa kamar k'asa zata tsage ta shige, wata irin azababbiyar kunya ce ta kamata, in har ita da shakur ne sun saba haka, har ya zaman musu jiki, basa tab'a kashe waya sai in har sun tashi sallah, haka akayi ta wasa da dariya a wurin har aka gama kwaliya.

Sanye take cikin wani red deola sagoe me masifar kyau, wanda yasha d'inki buba da zani da stones, kana ganinshi kasan an kashe kud'i, harta head d'in kanta red ne tayi azabban kyau, sai wani shek'i take, su ya murjanatu kuwa da suka ganta sai da suka hangame baki tsabar gaba d'ayanta canza, ya karimatu wace ita kuma babbar k'awarta ya murjantu ce ta ke fad'in,

"Mu da muka ganki mun susuce in abdulshakur kuwa ya ganki ba magana"

Samira sunkuyar da kanta tayi had'e da shigewa bayan k'ofa,

"Dan Allah ku daina tsokana ta"

Yarda tayi maganar a shagwabe, kamar zata saka musu kuka, dariya suka shiga yi mata kuma suka ci gaba da tsokanar tata a daidai wannan lokacin sai ga wayarta ta fara ringing, dukan su suka had'a baki suna ga mara hak'urin ango ya kira, samira na d'aukar wayar ta shige ban d'aki dan ta gaji ta tsiyar su.

Biki yayi dad'i anci an sha kuwa an rawsaya, sai da aka kusan zuwa k'arshe mc ya fara jawabin yanzu ango zai shigo da abokan shi, gaban Samira ne ya fad'i, murna ta k'ara kama ta, ji take yi kamar ta tashi ta k'arasa wurin shi a guje, tunda ya taka k'afa a cikin hall d'in kallonta yake, bata d'ago kanta ba amma ta sani sarai saboda ta ji idanunshi akanta, sai da ya k'araso ya zauna a kusa da ita Samira ta d'ago ta kalle shi gabanta taji yana fad'uwa saboda gaba d'aya ya canza mata, sati biyun da bata ganshi ba, ya d'an rame amma yayi fari sosai, ya d'an rage sajan fuskar shi sai fuskarshi ta k'ara yin kyau kuma ya saka lips d'inshi k'ara fitowa, yana sanye cikin maroon, d'inkin yayi masifan kyau ga babbar rigar da k'ara mishi kyau, samira ji tayi munfashin ta nayi sama tsabar kyan da yayi mata gashi wani irin kallo da yake binta dashi k'allon da yak'e d'auke da tsan tsan kwana da kewa, tana gani ya matso ya rad'a mata

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now