Final chapter

2.8K 235 26
                                    

Ta fiya suka a cikin gidan, ya rungumota ta baya, gaba d'ayan ta tana cikin jikin shi har suka zo kitchen, yau sati d'aya da bikin su samira zata fara girki, ba yarda baiyi da ita ba ta bari ya d'auko mata cook amma tak'i yarda, shagwab'a ta dunk'a yi mishi dake saka shi susuce wa tana r'okanshi ya bari ta dunk'a yi mishi girki, shima yanzu ya saba da cin grikin ta dan kan suyi aure ya wanci kullum a gurinta yake cin abinci amma tsakani da Allah baya san ta wahalar da kanta, haka ya hak'ura ya kyaleta.

Tana sanye da croptop pink da bum shorts bak'i, ba dankwali a kanta, shi kuwa yana sanye ta 3quarter blue da white shirt suna rungume suna kallon tv dan yanzu ya d'auki hutun wata biyu a office, yace yunwa yake ji bari yayi wa y'an biyu waya su had'a musu ambinci su aiko tayi zumbur tace ita zatayi. Yanzu suna kitchen still tana mak'ale a jikin shi, shi kuwa ya shigar da fuskar shi cikin wuyanta yana ta shak'ar daddad'an kamshin ta, yanzu yana ji yana santa fiye da daa, tunda ranar farkon su ya gano a budurwarta aka kawo mishi ita ranar darajar ta da k'imar ta ya k'ara nin kuwa fiye da daa a idanunshi ranar har kukan dad'i yayi, muryar ta ce ta dawo dashi daga tunanin da yake,

"Yanzu dan Allah sweetheart a haka zan yi girki,"

A shawgab'e tayi maganar tasan in har tayi mishi shagwab'a sai ta susata shi ta rikita shi yasa take amfanin dashi duk lokacin da take san wani abun a wurin shi, lumshe idanunshi yayi ya k'ara k'ankame ta, wallahi baya san sakin ta, shi in tashi ne su wuni a haka a bar abincin, jinshi da tayi yayi shiru ta saka hannunta ta cire hannun shi da yake kan cikin ta da kyar sannan ta juyo ta zamana tana kallon shi, shima kallonta nata yake, hannunta ta rataya a kan wuyan shi tare da matsowa da fuskar shi ta sumbace shi a baki sannan a kumatu, wani dad'i da nishad'i abun da tayi mishi ya saka shi, jin kanshi yake a sama, k'ara janta yayi ya saka bikin shi cikin nata ya fara sumbata har sai da gwiwoyinta suka fara yin sanyi kamar zata fad'i sannan ya sake ta, idanunta a lumshe tana bud'e su ya sakar mata murmushi, jin santa yayi ya k'ara bin jinin jikin shi da gab'ob'in shi, yana gani ta tattro nustuwar ta sannan ta saki wuyan shi,

"Ka je ka zauna nayi maka abinci kace yunwa kake ji"

Shagwab'ar dai ta k'ara yi mishi, kara ji yayi bazai iya matsawa ko nan ba in har bata tare dashi, kallon cikin idanunta yayi,

"Gaya mun mai zan taya ki, gwanda mu wahala mu biyu akan ke kad'ai ki wahala"

Dariya ya bama samira, zumb'uro bakin shi yayi waje da yaga tana mishi dariya, wata dariyar ta k'ara yi,

"Tom shikenan"

Tana fad'a ta kwace daga jikin shi ta wuce store ta d'auko mishi albasa da garlic ta dawo ta ajiye a gaban shi ta d'auko wuk'a da chopping board sannan ta k'ara komawa gaban shi ta ajiye, tana sane tayi mishi haka, kallon shi tayi tace ya yanka, abdulshakur kallon ta yayi jikin shi ya bashi mugunta take shirin yi mishi, haka ya share ya fara yanka albasar bayan ta gaya mishi ya zaiyi, tana fad'a ta k'ara komawa store, abdulshakur baiyi yanka uku ba yaji ya cika mishi ido ya fara hawaye, nan ya fara mita da raki, samira ba abunda take in ba dariya ba, haka ya hak'ura da taya ta girkin ya zuba mata ido, duk inda tayi a kitchen d'in yana biye da ita kamar chewing gum, a haka har suka gama, akan cinyarshi ta zauna suka ci abinci kuma a plate d'aya da yake ba wani abincin zafi tayi ba, spaghetti da mince meat sauce tayi musu, haka sukayi ta bama junan su abun sha'awa cik'e da so da k'wana.

Bayan sun gama cin abinci suna kwance a d'aki manne da jikin juna, wayar abdulshakur tayi k'ara, d'auka yayi ya da kunnen shi, be dad'e da magana da na d'ayan bangaran ba ya kashe wayar, mik'ewa yayi ya shiga closet d'in Samira ya d'auko mata abaya da mayafi sannan ya koma cikin d'aikin ya mik'ar da ita taga kwanciyar da take sannan ya saka mata abayar, tare da yafa mata mayafin, duk abunda yake Samira ta kafa mishi idanu sai tambayar shi take ina zasu, shiru yayi mata, sai da suka fito wajan gidan sannan ya saka hannunshi ya kulle mata idanunta, had'e da rik'e ta a jikin shi har ya kawota gaban wurin, a hankali ya cire hannunshi daga idanunta, yana gani ta zaro manyan idanunta waje, tare da hangame baki, sannan ta juya tana kallan shi, fuskarta d'auke da alamar tambaya, d'aga mata kai yayi, yana d'aga mata kai ta saki wani wawan iho har sai da ya toshe kunnan shi had'e da buga tsalle sannan ta d'ane kanshi ta rungume tana nagode nagode, shi kuwa k'ara janta jikinshi yayi, in har motar da ya siya mata ta saka ta murna haka zai iya sai mata ashirin d'insu dan kawai yaga irin reaction d'innan dan farin cikin ta yafi mishi komi a duniyar nan, usman da yake tsaye shima dariya ta bashi, suna koma wa cikin gida ta d'auki waya ta dunk'a kiran y'an uwa tana gaya musu abdulshakur ya siyar mata mota BMW X1, shi kuwa yana gefan ta Yana ta murmushi.

Sati biyu da bikin su suka kama hanya suka bar k'asar, sai da suka fara zuwa landon sukayi sati d'aya sannan Dubai shima sati d'aya sai aka wuce umara, sun dad'e a makkah dan sunyi kusan sati uku. Ranar da zasu dawo sunga ta tarb'a duk y'an gidan su abdulshakur sai da suka zo airport, har su ya zainab da ya khadija da y'ayansu, in kinga Samira ta k'ara kyau tayi k'iba, shima ta b'angaran abdulshakur haka ne, yayi fari, yayi fresh ga shima ya zuba k'iba, da su ya murjanatu suka ganta sai da suka dunk'a tambayar ta ko ciki ne da ita tsabar yarda Samira ta canza.


$$$$$$$$$$

Samira tsohon ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe, cikin ya saka bak'ar fatar ta ta k'ara kyau ga wani laushin jiki da ya saka ta, dukda tasha wuya farkon cikin laulayi tayi sosai wanda in taci abinci sai amai ko kad'an baya zama a cikinta sai dai ai ta saka mata drip, ga bata san k'anshi, shima in ta shak'a sai amai, ko mijinta baya zuwa kusa da ita in har ya saka turare ko ya shafa wani abun mai k'amshi, abdulshakur kuwa harda shi akayi laulayin dan shima yaji jiki, gaba d'aya ya tsure ga tausayinta da ya kama shi, barin ma in yaga tana amai bayan cikinta ba komi in har ba ruwa ba, sai dai ya tsugunna a kusa da ita a b'and'akin yayi ta shafa gashin kanta yana "Sannu My Love", ga ya hana kowa yin jiniyar ta, da kanshi yayi komi ya k'ara da'aukar hutun office, abunka da kamfanin shi ne ba wanda ya isa yayi mishi magana, Allah ya taimake ta cikin na kaiwa wata shida laulayin yai sauk'i.

Yanzu tana gida tana jiran haihuwa, kan abdulshakur ya barta ta dawo gida sai da aka sha rigima har sai da daddy ya shiga cikin maganar sannan ya bari, shima sai da ana saura sati d'aya EDD d'inta.

Bayan sun gama hira da gwaggo an tuk'a mata tuwo miyar kuka tasha daddawa taci tayi nak ta zauna mai da numfashi, ba ayi awa uku da cin tuwo ba sai ga nak'uda ta taho garan garan tuni suka d'iba sukayi asibiti, tun kan a k'arasa gaba d'aya an sanarwa kowa, abdulshakur da yake tsakiyar meeting haka ya fito a guje, bai iya tuk'i ba sai usman ne ya tuk'a shi tsabar yarda jikin shi ya dunk'a rawa bayan hankalin shi da yayi mugun tashi, yana isowa kowa ya hallara, mommy da su amal sunzo, ya murjanatu da safiya da kuma gwaggo har farida tazo babynta me suna Munir, samira kawai ake jira ta haihu, ba ayi cikken awa hud'u ba sai gashi ta haifo santalelan d'anta namiji, saboda tsabar murna da farin ciki abdulshakur bai san lokacin da ya rungume mommy ba yana kuka.

Ansha suna, yaro ya gaji sunan baban su daddy haruna ana ce mishi Aiman, k'anwar daddy hajia yasira ta zuba mishi kyauta, ba'a magana, haka dangin da y'an uwa da abokan arziki suma suka dunk'a nuna tasu bajinta, an nuna mata so da kwana, yay'an su yaya khadija da ya Zainab ba murnar da basuyi ba, har haidar d'an ya khadija da Na'im d'an ya Zainab suka dunk'a fad'a sai an basu sun tafi gida dashi.

Rayuwar Samira da abudulshakur haka ta ci gaba da gudana cikin farin ciki da kwanciyar hankali, basu tab'a daina son junan su ba dukda yanzu suna da y'aya uku, Aiman, ne babba sai yan biyu, Amira da Amir, wanda Amira taci sunnan maman mommy rahama shi kuma Amir yaci sunan baban su samira, bashir. In kaga Samira ta zama cikkakiyar mace meji da ilimi da kud'i, kana ganinta kasan tana cikin hutu da kwanciyar hankali, yanzu ta zama cikkakiyar doctor, a wajan abdulshakur shima d'in haka ne, ya k'ara kyau da manyanta saboda shekaru sun fara zauna mai, ga hutu da jin dad'i, kuma arzik'i da kud'i ba'a magana, business yanzu kamfanin su yayi suna a k'asa shan waje, ga son junan su da har yanzu bai ragu ba ko bayan shekara da shekaru.



(Alhamdulilah, Ba abunda zance wa Allah sai godiya da ya bani damar rubuta wannan littafin da gama shi.

Sabon littafi na MUGUN MIJI ya kamata duk ku saka shi library d'in ku.

Godiya dubu ga musu voting da commenting wallahi harda k'arfin gwiwar da kuka bani ya saka na gama littafin nan. Allah ne zai biya ku nagode sosai da sosai.)

BA KYAU BA ✔️Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora