Chapter forty-eight

1.5K 180 13
                                    

Gaba d'aya ta kasa gane alamarin nabila, wai bata ji tace mata zata bar mata abdulshakur bane, a ganinta namiji bai isa ya shiga tsakanin su ba, so take ta k'ara yi mata bayani amma nabila kwata kwata tak'i sauraron ta, rashin yarda da ita da ta kasa yi yana mata ciwo, tunda shekara da shekaru suna tare yaci ace yanzu ta gama sanin halinta tasan tana san farin cikin way'anda take so sama da nata, ko dai nabila bata d'auki k'awancen su a bakin komi bane shi ya saka har tage zarginta da k'wace mata saurayi, haka ta dunk'a tunanin alamarin nabila har ta isa gidan bikin, ta ajiye had'uwar ta da abudulshakur a gidan su nabila a gefe duk da tana san sanin me yakai shi gidan su.

Fitowa tayi tare da kulle motar ta ta shiga cikin gidan ta tarar dashi a cik'e, k'arasawa ciki tayi tana kuwa shiga ta had'u da umman su farida, tsugunawa tayi suka gaisa tace mata farida da sauran na d'akinta, tana shiga d'akin ta tarar duk k'awayen sun zagaye amaryar da take faman kuka, sauri tayi ta k'arasa wurin tana tambayar ya akayi, ilham ce tace mata ai kukan rabuwa da gida take nan kuwa suka saka ta a gaba suka dunk'a mata tsiya har dai suka samu tabar kukan.

Samira na ruk'e da hannun farida wacce ke sanye da alkyabba a jikinta za'a tafi kaita gidan khalifa, amaryar ta ruk'e hannunta gam tak'i saki ga kukanta yanzu ya dawo sosai, samira itama k'wallar take ita wallahi in za'a kaita gidan miji ranar akwai kallo, a rabata da mama da gwaggo akwai babbar matsala, tsayawa tayi da tunanita da taga wane ya fito daga cikin motar, bata tab'a ganin shi da wannan motar ba, har kayan jikin shi ya canza, yana sanye da yadi shi kuma fari yayi azabar kyau, yana sauko wa daga motar suka had'a ido, sauri tayi ta sunkuyar da kanta, yau ma a motar shi zasu kai amaryar, ta shiga uku dashi a bikinan, so tayi ta k'wace hanunta daga cikin na farida tayi sauri ta sallallab'a tayi baya amma Ina farida tayi wa hannunta mugun kamu, haka ta hak'ura, wata tsohuwa ce ta ruk'e d'aya bangaren farida suka fara takawa dan isa wurin motar shi, gashi a wajan ya kicime ana ta gud'a da shewa wasu kuma na shiga mota za'a tafi gidan amarya, baya suka shiga wata mata kuma ta shiga gaban motar bai dade ba shima ya shigo, aka fara convoy aka yi gaba.

Farida har lokacin bata saki hannunta ba kuma ba abun da kake ji a motar sai k'arar kukan ta, ita kuwa Samira ta d'ora d'aya hannunta akan nata tana shafawa alamun rarrashi, ga kanta a k'asa itama tana jin tsoro ta d'ago idanunta dana had'u dana abdulshakur wanda tasan yana ta kallonta ta rear view mirror d'in motar, haka da take da maze kamar kallon baya damunta. Suna isa unguwar da farida zata zauna wato sharad'a phase 2 suka fara tsayawa a gidan su khalifa tunda unguwa d'aya ne, sai da aka shiga da amarya ciki aka kaita ta gana da iyayen mijinta da y'an uwanshi sannan suka tafi gidan amarya.

Gidan farida ya tsaru iya tsaruwa ko daga wajan, gida ne me bene, ko da suka shiga ciki shima sunsha kallo an saka mata kayan d'aki masu kyau masu tsada, sama akwai bedrooms guda uku da parlor k'asa akwai bedrooms biyu da parlor biyu. Su da friends d'insu na zaune a bedroom d'in farida bayan kowa ya watse su sun tsaya sai abokan ango sunzo, samira bata so tsayawa ba amma farida ta hanata ta tafiya, da kanta ta kira mama ta rok'eta dan Allah ta barta ta k'ara dad'ewa sunci sa'a mama ta yarda, hira suke sosai a tsakanin su, can farida ce ta tashi tare da kama hannun samira suka shiga wani d'aki farida ta saka muk'ulli da kulle k'ofar sannan ta jawo ta suka zauna akan gado, k'ura ma k'awarta ido tayi sai kuma can ta bud'e bakinta,

"Me ya had'a ku da nabila, tunda nake daku nan tab'a ganin ku a rana ba, me ya faru"

Samira shiru tayi, kamar karta gaya mata, amma da tayi tunani matsayin farida a wurinta, itama kamar babbar k'awarta ce, tana santa kamar yadda take san nabila, ajiyar zuciya tayi sannan ta kwashe komi ta gayawa k'awartata, shiru ba wanda yace komi bayan ta gama bayanin, sun dad'e a haka, farida ce ta fara magana,

"Kina san shi"

Abunda tace mata kenan, gaban Samira ne yayi mummunar fad'uwa, tana sanshi sosai fiya da tunanin kowa, tana ji tana sanshi fiye da yarda take san kanta, amma baza ta tab'a iya fitowa ta fad'a ba, abinda farida ta k'ara ce mata ne yayi mugun tayar mata da hankali,

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now