Chapter eight

1.7K 186 3
                                    

Yana fitowa daga office dinshi yayi hanyar inda motan shi me kirar Range Rover take, unlocking dinta yayi sannan ya fada ciki ya kunna ya fara tuk'i, securities na ganin ya tun karo gate din sukayi saurin bude mishi tare da daga mishi hannu, gida ya nufa, yana ko shiga bedroom dinshi ya fada ya fara cire kayan jikin shi, ya gama tsab ya rage daga she sai boxers sannan ya fada bathroom, yayi wanka atleast ya kaishi 20 minutes sannan ya fito da towel a jikinshi, jikin nan nashi duk a murd'e ga six pack abs dinshi nan nashi abun sha'awa, yin wurin makeken standing mirror dinshi yayi hade da dago hannun shi da ke rike da wani towel din ya fara goge sumar da ke kanshi da ya gama tsab yayi hanyar closet dinshi, white t-shirt ya dauko tare da wani black jeans, sannan ya koma cikin bedroom dinshi yayi duk abun da ya zaman mai al'ada, yayi kyau masha Allah kamar balaraben can, bin jikin shi yayi da turararuka masu kamshi sai da ya wanke cikin shi tsab dasu sannan ya dauki muku lin motar shi yayi ya nufi hanyar waje,

yana fitowa side din mommy yayi dan ya gaishe ta bai gaishe ta ba dazu da safe yana sauri, yana ko shiga yayi arba da amra da ke faman danna waya da kuma amal dake kallan tv, amra ce ta fara kai idonta gare shi ta sakan mishi murmushi

"kai yayana ina zuwa haka"

amal tayi saurin juyowa tare da binshi da kallo, dariya ta saki

"lah ko dai zance zaka je gurin ya nabila",

Abudulshakur ya sha kuna ya had'e girar shi ta sama da kasa fuskar nan tashi ba walwala

"wallahi kun rainani sosai, ace mutum bai isa ya shirya ba sai ace zance zai je to wallahi ku kiyaye ne danni ba sa'an ku ba ne, kinsan hali na zan daka ku kuma ba wanda zai ce mun k'ala"

amal da amra suka kalli juna sauran k'iris su fashe da dariya badan mommy ta shigo pallor din ba

" wai ku me yasa baku da kunya ne iye, duk kunbi kun raina shi tsaban rashin kunya, ni da Allah ku tashi ku bani wuri"

Amra da amal suka mik'e sum sum suka yi dakin su, mommy ta dawo da kallonta kan tillon dan nata

"yaushe ka shigo gidan ne"

abdulshakur sun kuya wa yayi ya gaishe ta sannan yace

" na d'an jima, nazo na gaishe ki ne saboda dazu ban samu nazo ba"

mummy tayi murmushi

"Allah ya maka albarka kaji, kadai ci abinci ko?"

abdulshakur shima murmushin yayi

" eh, nayi order da ina office"

tare da mik'e wa daga zaman da yayi

"toh nidai zan dan fita zuwa supermarket, akwai wasu abu buwana da suka kare ina san siyan wasu"

nan dai yayima mommy sai da safe ya kama hanyar waje.

Abdulshakur na isa wellcare ya sami wuri yayi parking motar shi, sannan ya fito ya fara takawa a hankali ya na tafi yarshi ta kasaita, yana shiga wurin idan kowa ya fada kan shi, ba matan wurin kadai ba har mazan wurin sun bisa da ido kallan shi kawai suke yi, shi kuwa ko ajikin shi saboda in har kallo ne to ya saba, daukan shopping basket yayi ya fara hin siyyayyar shi, yin kumi yake cikin nutsuwa yana jin wasu mata a kusa dashi suna magana k'asa k'asa kuma ya sa ni sarai maganar shi suke, duk wanda ke wurin nan yasan shi kuma yasan shi waye, zai yi wahala ya bar wurin ba tare da wata mace ta mishi magana ba shi kuma abun da ya tsana a rayuwan shi, ya tsani matan da basu da aji shi yasa ma ya sha kunu, fuskar sa daure ba alamanun wasa a tattare da shi, yana cikin haka har ya isa wajan da yake a ranshi, yana zuwa hannun shi yasa akan stand din dan ya dauki abunda yayi niyya amma mai, hannu shi yaji cikin na wani, saukar da idanun shi yayi dan yaga wane dan rainin hankalin ne, yana kai idanun shi kan abu yaji gaban shi yayi wata irin mummunar faduwa, tuni zuciyar shi ta fara buguwa har yana jiyo sautin ta a kunnen shi, tsayawa sukayi suna kallon kallo da yarinyar, ba wanda yake mosti a cikin su, kallon junan su suke sosai kamar su kai dai ne a wurin, suna cikin haka suka ji karar abu tus a k'asa, dukkan su biyun idannun su suka kai wurin, mouthwash din dake hannun su suka saki bama su san sunyi ba.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now