Chapter thirty-two

1.4K 150 2
                                    

Ji yayi ya nemi numfashin shi ya rasa gaba d'aya hankalin shi ya gushe a lokacin da ya tsince ismail akan ruwan cikin Samira, hawaye ne masu zafi ke zuba a fuskar shi daya dube ta ya ga yadda ta lumshe idanunta itama hawaye na ambaliya a fuskar ta, ji yayi zuciyar shi na mishu wani irin rad'ad'i da ciwo yadda ya ganta a wurin, ya tabbata bazai tab'a mantawa da tashin hankali ta ya gani a ranar yau ba, ba zai taba mantawa da fuskar Samira ba wacce take d'auke da tsan tsan abun tausayi, ko mara imani ne ya ganta a wurin dole sai ta bashi tausayi bare me imani.

Gaba d'aya k'arfin shi ya saka ya d'aga Ismail daga kan samira, ismail bai arba ba yaji wani masifaffan naushi a kumatun shi, kan ya k'ara ankara ya k'ara jin wani a hancin shi, so yake ya kwace kanshi amma ya kasa, tsabar k'arfin da abdulshakur ya saka mishi gashi yayi mai diran bazata, wata irin azaba ce ta rufe fuskar shi gaba d'aya ciwo take mishi tsabar naushi da dukan da take sha, biyu biyu yake gani tsabar wahala, tun yana neman kwacewa har ya hakura,

Abdulshakur kuwa kamaninshi sun canza gaba d'aya, idanunshi sun k'ara yin ja ja wur, farar fuskarshi itama ta koma jaa, bayan hawayen dake kwarara a fuskar shi, kana ganin jijoyin shi dake kwance akan wuyan shi, zuciyar shi tafasa take yi, in bai kashe ismail yau ba to sai ya nakasa shi, gaba d'aya Ismail ya daina mosti a k'asan shi amma ko ajikin shi, dukan shi yake kamar Allah ya aiko shi, hannushi har fara tsage wa yayi amma abdulshakur bai daina bugun shi ba, fuskar Ismail ta fara kumbura ya ya fara fita daga hayyacin sa,

Shima kan ya ankara yaji an daga shi daga kan ismail, shure shure ya fara dan ya kwace ya k'ara komawa kanshi amma ina, wani irin mugun ri'ko suka mishi, waiga wa yayi yaga, Nasir, zayyan da al-ameen, gaba d'aya su ukun suka ruk'e shi gam gam, k'ara waigawa yayi ya kalli inda Ismail yake wanda jini yayi ma gaba d'aya fuskar shi ado, halitar fuskar shi ta fara canza wa, kumatun shi da bakin shi har idanunshi sun kumbora sunyi suntum, baya ko mosti, khalifa da shahid ya gani akanshi suna k'okarin tashin shi ga zuba sallatin da suke.

Mubarak dake gefe ne wanda ya kasa tabuka komi tsabar shock d'in da ya shiga ya fara cewa

"Shikenan abdulshakur ka kashe shi" tsabar yadda yaga ko gab'a d'aya a jikin ismail bata mostsi

Nasir ne yayi saurin kallan inda matan suke gaba d'aya sun rufe samira

"Wani daga cikin ku ya shiga gida ya dauko mata hijab"

Ya fad'a har lokacin hannushi basu bar rik'e abdulshakur d'in da suke ba ya tabbata in har d'aya daga cikin su ukun da suka rik'e shi ya rage k'arfin shi ko yaya ne sai abdulshakur ya kwace ya koma kan ismail, wani irin huci yake kamar zaki ga hawaye da har lokacin basu bar zuba a fuskar shi ba,

Asiya ce ta mik'e gaba d'aya jikinta ba kwari tayi hanyar cikin gida,

Abdulshakur kai idanunshi yayi kan samira, dukda matan sun kulle ta ya d'an hangi yadda take a lokacin, kuka take yi sosai ga jikinta da yake faman rawa, ta had'e tare da k'ankame jikinta guri d'aya, wani irin abu yaji ya taso mishi, me tayi wa ismail da yake san cutar da ita haka, me ta tab'a yi mishi a duniya da yake san ruguza mata rayuwa, wasu sabbabin hawayen me suka k'ara fitowa daga idanunshi, tausayin ta yaji ya baibaye gaba d'aya zuciyar shi, gaskiya ismail mugun mutum ne, wata irin tsanar shi ya ji ta mamaye dukan cikin jikinshi,

K'ara kwacewa yayi zai koma kan ismail, wannan karan kuwa ya fusge dan gaba d'aya k'arfin shi ya saka, gudu ya saka dan ya isa gurin ismail da yake kwance akan grass har lokacin bai farfad'o ba,  zayyan da nasir ne sukayi saurin binshi a baya kan ya k'arasa suka ci nasarar kamo shi,

"Abdulshakur dan Allah ya isa haka, kayi mishi jina jinan da sai yayi sati a asibiti in har kabi ta ziciyarka ka k'ara dukan shi to wallahi kashe shi zakayi"

zayyan ya fad'a tare da fara jan abdulshakur baya, haka suka kuma taruwa su uku har suka samu suka fitar dashi daga garden d'in gaba d'aya saboda sun tabbata in har ya ci gaba da ganin yanayin da samira take ciki to yau abdulshakur sai yayi kisa sai dai wani ikon Allah,

Al-ameen kuwa cewa yake a ranshi dama Ahmad yazo, dan shine k'ad'ai zai iya yi da abdulshakur a matsayin shi na soja, amma aiki yayi mishi yawa bai samu ya biyo su ba.

Suna isa parlor d'in suka zaunar da abudulshakur akan kujera, nasir ne ya tsaya a gaban shi tare da rik'e kafad'arshi guda biyun, ya fara matsawa kamar me yin tausa, k'asa yayi da muryar shi sannan ya umarci abdulshakur yayi addu'a itace kawai zata saka zuciyar shi ta rage rad'adin da take,

Abdulshakur lumshe idanunshi yayi, ganin fuskar Samira yayi lokacin da ismail yake kanta, ji yayi zuciyar shi ta k'ara harbawa, sa hannushi yayi akan sumar dake kanshi ya fara jan gashin shi,  zuciyar shi wata irin bugawa take kamar zata fito daga cikin k'irjin shi, zayyan da Al-ameen dake wurin sunyi shiru sun kawai zuba mishi idanu, jikin su yayi wani irin sanyi,

Bude manyan idanshi yayi, da har lokacin a jajayen su suke bayan hawayen da basu bar zuba ba a fuskar shi, kallan abokan nashi ya fara, ya kalli wancan sai ya kalli wancan, gaba d'aya fuskar shi ta koma abun tausayi, yau ce rana ta farko da suka tab'a ganin shi a cikin wannan yanayi, gaba d'aya ya tashi daga abdulshakur d'in da suka sani ya koma wani mutum daban,

"Baku ga abunda yayi mata bane da kuke so ku hanani hukunta shi"

yadda yayi maganar sai yayi mugun baka tausayi, maganar ta bal'in dakar zuciyoyin abokan nashi, al-ameen baisan lokacin da ya fara kwalla ba,

Tabbas sun gane sirrin da abudulshakur ke boye musu, a yau suka gane abdulshakur na SAN Samira, kuma SAN da yake mata ba d'ankaramin SO bane, shi ya saka shi acikin wannan tashin hankalin, wani irin tausayin shi abokan nashi suke ji,

Zayyan ne ya masto kusa da abudulshakur tare da tsugunawa da gwiwarshi a k'asan carpet d'in shima ya fara magana a hankali kamar jariri yake wa magana,

"Dukan da kayi mishi a baya ya wadatar ba sai ka k'ara mishi wani ba, hukunci kuma ba kai zaka d'auka da hannunka ba akwai hukuma, in har wani abu ya same shi kaima ka jefa kanka acikin matsala, dan Allah ka sauko da zuciyarka kaji"

Duk maganar da zayyan yayi idanunshi nakan abdulshakur, yana gani ya k'ara lumshe idanunshi sannan yayi wata irin ajiyar zuciya, yanzu hawayen dake zuba a fuskar shi sun fara raguwa,

Juyawa yayi da kanshi ya kalli garden d'in, su Samira basa wurin amma har lokacin khalifa da shahid suna kan ismail suna faman nema ya farfad'o, Mubarak ya hanga dake sauri dan ya iso parlor d'in, yana shigowa parlor d'in ya kalli sauran abokan shi,

"Wani yazo mu samu mu kama ismail mukai asibiti dan har yanzu yak'i' tashi" yadda yayi maganar muryar shi dauke da tsoro, shi dai yasan abdulshakur ya kashe shi,

Al-ameen ne ya kalli zayyan da nasir, yace musu bari yaje su su zauna da abdulshakur, yana gama fad'a yayi waje shi da Mubarak,

Da kyar abdulshakur ya iya tattaro dukan nustuwar shi, ya mik'e daga zaman da yake, zayyan da nasir ne suka had'a baki suka ce mishi Ina zaije, baima juyo ya kalle su ba balle ya basu amsa, suna gani yayi hanyar k'ofar da zata kashi side d'in su Samira, tashi sukayi da sauri suka bi bayan shi.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now