Chapter fifty

1.5K 176 21
                                    

Kan ta taji ya d'auki ciwo ga sanyin k'asa ya addabe ta bayan ciwon da jikinta ya fara yi mata, shine abun da ya saka ta ta fara mosti alamun zata tashi, bud'e idanunta tayi taga silin d'in katako, k'ara waiga wa tayi taga window d'in langa langa, abune ya shiga fad'o mata d'aya bayan d'aya bayan ta dawo daga wurin bello, zumbur tayi ta mik'e daga kwanciyar, kanta ne yayi wani irin juyowa sai da ta kulle idanunta, Ina ne nan, Ina aka kawota, kan ta ankara taji mutum a gabanta, tana d'aga ido taga wani jibgegen k'ato, mummuna bak'i k'iran da jan idanu bayan bak'in bakin shi, gaban Samira ne yayi mummnar fad'uwa, tsoro ya baibayeta, wane ne wannan mutumin, yadda yake kallanta ya saka zuciyar ta k'ara bugawa bayan tsoron da ya k'ara rufe ta, motsi ta fara dan ta tashi ta ruga tayi ta kanta amma sai jin hannunta tayi a k'ulle sai a lokacin ta lura hannunta da k'afarta gaba d'aya a d'aure suke, sai a lokacin abun ya fad'o mata sace ta akayi, jikinta ne ya fara mahaukacin rawa, me tayi musu suke san cutar da ita, d'aga kanta tayi ta fara jero wa jibgegen mutumin tambayoyi,

"Sace ni kayi, me na maka, me kake so daga wuri na"

A mugun rud'e tayi magana, ga muryarta ta ke faman rawa, jin k'atuwar muryar shi tayi, wacce ta k'ara razana ta,

"Easy, ayi tambayar d'aya bayan d'aya mana, mene na sauri"

Kwalla taji ta cika idanunta kaf, amma baza ta tab'a bari hawayen su zuba, tasan irin wannan mugayen mutane in suka ga kana da tsoro sunfi saurin cutar dakai, lumshe idanunta tayi dan ta kawar da tsoron da take ji ta fara addu'a a ranta, sai da taji nustuwa ta d'an fara zuwa sannan ta bud'e su, kar idanunta ta saki a kan shi, wanda yanzu ya nanad'e garadan hannun shi,

"Me na muku kuka sace ni"

Yanzu muryarta kwata kwata bata yi rawa ba, kuwa bata nuna alamun tsoro ba, abun ya bama mutmin mamaki, dan in sun sato wasu suna bud'e ido in sunga a inda suke suke saka kuka su fara kiran uwarsu da ubansu, tunda yaga yarinya yasan wannan daban ce za'a sha fama, kallonta yayi ya fara bata amsa,

"Ni ba abunda kikayi mun, laifin wata kika yi wa"

Gaban Samira ne ya fad'i, wata kuma, wace wata, ita duk zaman ta a duniya ba abun da ya tab'a had'a ta da wani da har zai saka a d'auke ta a rabata da iyayenta, itama maida idanunta tayi kanshi,

"Wace wata, ka fito ka gaya mun wace ta saka ka"

Dariya taji ya saki, irin dariya me d'auke da abun tsoro, wacce zata iya saka ka fitsari, in samira tace baya bata tsoro tayi k'arya, amma haka ta k'ara dake wa, ta k'i nuna tsoron ta, ji tayi yayi wa wani magana wanda bama ta lura dashi ba, saboda wurin akwai d'an duhu, shima jibgegen k'aton ne sai dai bai kai d'ayan girma ba, gani tayi d'ayanya mik'a mishi waya,

"Kada ki damu tace in har kin tashi a kirata dan ki ji babban jawabin daga gareta"

Yana gama fad'a taga ya saka wayar a kunnen shi, ba'a dad'e ba taji ya fara magana yana sanarda na d'aya b'angaran gata ta tashi, gani tayo ya fara matsowa, itama baya ta fara ja da jikinta saboda irin kallon da yake mata kallon kura taga nama, turo wayar yayi tare da sakawa a speaker, shiru ba'ayi magana ba, sai can aka fara muryar da Samira taji ta bala'in tayar mata da hankali, anya kunnanta dai dai yake jiye mata,

"Sannu da tashi, ai da na ga kin dad'e baki farfad'o ba na d'auka kawai zaki wuce ne ki kawo mana saukin aikin mu"

Tabbasa muryar ta ce, wani abu taji ya tsaya mata a k'irji bayan dukan da zuciyar ta take, kanta wani irin nauyi ya fara mata, jikinta yayi sanyi taji hawayen da bata so su zubo sun fara zuba,

"Nabila?"

A hankali tayi tambayar kamar wace bata da jini a jiki, kina ganinta kinsan tana cikin tashin hankali, baza ta tab'a yarda itace ta saka a mata haka ba, nabila ta take aminyar ta, y'ar uwarta, masoyiyarta, wacce kamar hanta da jini suke tsabar shak'uwa, dariya taji an saki,

"Ya kike tambaya ta kamar baki san nice ba, nasan daga muryata kin gane"

Hawaye yanzu ambaliya suke a fuskar Samira, komi na jikinta ya tsaya cak, baya mosti tsabar shock d'in da ta shiga, wani irin juyawa kanta yake bayan nauyin da yayi mata, so take ta tashi daga wannan mummunan mafarkin saboda tasan a zahira nabila baza ta tab'a cutar da ita ba, leb'anta ta saka ta ciza da mugun k'arfi wai dan ta farka, k'ara jin muryartan da tayi ne ya tabbatar mata ba mafarki take ba,

"Tunda aika ki lahira za suyi nan bada jimawa ba bari na gaya miki duk abun dake cikin raina, na tsane ki, na tsani ganin ki, tabbas akwai lokacin da na d'auke ki k'awa amma tunda kika kwace mun wanda nafi so duk duniya kika ruguza wannan dan gan takar tsakanin mu, kin yaudare ni, ba abunda biki cemun ba dan na rabu dashi ashe ta bayan fage ke munafuka ce san shi kike, ranar da na ganku tare a lagos ranar kika ruguza mun farin ciki na, na kai ku wurin malamai bazan iya k'irga su ba sunce aiki akan ku zai yi wuya kuma zai d'auki lokaci saboda ke dashi duka na tsaye akan adinin ku, na gaji shine na gane wannan ce hanya mafi sauki'"

Shiru tayi da maganarta da take wurin yayi tsit shima baka jin komi sai k'arar shahek'ar kukan samira,

"Saboda ke yazo har gida ya cimun mutunci, samira ke macuciya ce muguwa azzalima, tunda ya nuna mun bazai tab'a karba'ar soyayya ta ba ke yake so naji bama nasan ki zauna a doran k'asa, Ina so in saka mishi ciwon da ya saka mun Ina so in tarwatsa rayuwar ku yadda kuka tarwatsa tawa rayuwar, dan haka bari na fara miki addu'a tunda ga nan, Allah yaji k'anki saboda na tabbata miki baza ki fita daga wurin nan da rai ba, duk wani masoyin ki a gobe zai shiga k'unci da k'unar rai dan sai na tabbata sun ga gawarki a wulaqance yadda baza su tab'a mantawa ba kuma yadda abun bazai tab'a daina musu ciwo ba"

Ji tayi an kashe wayar bayan ta gama fad'an mugayen maganganun, samira yanzu kuka take sosai, zuciyar ta rad'ad'i take mata, ciwon me zata ji ciwon yau zata mutu ko ciwon muguwar cutar da babbar k'awarta ke san cimma wa akan ta, wai duk namiji ne ya saka nabila fad'uwa halaka irin wannan, k'ara tuna maganganun ta tayi taji wani kuka mai k'arfi yazo mata, shikenan baza ta sake ganin mama ba, da gwaggo da ya muazzam da ya murjanatu da iman, da tasan yau zata mutu da baza ta tab'a samun sab'ani da safiya ba y'ar k'anwarta, haka zata mutu tabar masoyanta a cikin k'unci, shakur d'inta, zata mutu bata fayyace mishi abunda ke zuciyar ta ba, zata mutu bata nemi gafar shi ba ta bashi hak'urin wahalar dashi da tayi, kuka take yi sosai bayan wani mugun tsoro da ya gama rufeta, tsoron da tunda take a duniya bata tab'a jinsa ba, irin tsoron da ke saka ko wace gab'a ta jikin ka ta fara rawa Ita kad'ai, kulle idanunta tayi ta fara addu'a, ko da taji muryar ogan nasu bata bud'e idanunta ba,

"Yanzu zamu d'an jin kirta aikin saboda hajiya tace kada mu tab'a ki har sai wani yazo shima yayi miki tashi sallamar, yanzu haka yana kan hanya"

Samira ta sallama wa Allah komi, ita haka k'arshen ta yake, haka zata bar duniya kuma ba wanda zai san mugayen mutanen da suka kashe ta. Wani zazzab'i ne me zafi ya rufeta tsabar tashin hankalin da take ciki, tasan ba wanda zaizo cicanta saboda wane ma zai san inda take, koma sun sani kan suzo aikin gama ya riga da ya gama, hawaye ne masu zafi suka sake bin fuskar ta.

(Dan Allah abunda nabila tayi ta kyauta..???

Mun kusa zuwa k'arshe dan Allah kar kuza bored dan gani nake chapters d'in kwanan nan ba dad'i 😭😭

Please vote and share ❤️)

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now