Chapter four

2.5K 192 2
                                    

(Zan dan yi muku labarin yadda samira da nabila suka hadu da abudulshakur kan mucigaba da dayan labarin)

Kwanakin nan duk ta kasa gane alamarin faruk, baya daukan wayar ta ko a makaranta ma bata ganin shi, kuma ada kullum suna tare, tana cikin tunanin nan taji wayar ta me k'irar iPhone 7+ tayi k'ara alamun text ya shigo aiko tana dago waya taga daga faruk ne da sauri da bude message d'in harda y'ar murnar ta amma abun da ta gani yayi mutukar daga mata hankali bata san lokacin da hawaye ya fara zubo mata, nabila dake gefanta suna hira da wata kawar su Farida ta dan juya tayi ma samira magana saboda taji ta shiru bata saka baki a hiran, aiko tana juya wa taga samira na hawaye ai kuwa tuni hankalin ta ya tashi ta matso da sauri kusa da ita tana tambayar ta lafiya, samira kawai wayanta ta mik'a mata tana ko k'arba ta karanta message din, wai faruk ne yace su rabu shi yanzu ya daina santa ya b'ata lokaci da yin soyyaya da wacce ba ajin shi ba yafita komi da kudi kyau da class, nabila ta saki sallati amma dai faruk dan iska ne na ajin farko ya rasa ma ta inda zai fada mata su rabu sai a ta text tabdi

tuni ta kama hannun samira wacce take faman zubar da hawaye tare da yima farida wacce take binsu da kallon tambaya sallama, tuni inda samira ke ajiye motar ta tayi sannan ta karbi handbag din samira ta ciro mukulin motar ta ta bude mata gaba ta saka ta aciki, sannan ta koma wurin driver ta shiga sannan taja motar daman sun gama lectures sun tsaya yin tutorials ne,

bata wuce da ita gidan su samira ba saboda kar hankalin maman su ya tashi ta wuce gidan su da ita, suna shiga nabila ta shiga rarrshin ta daman kamar samira jira take ta fashe da kuka sai da tayi mai isar ta sannan tace bokomi duniya ce yaje aishi ba autan maza bane, abun yayi ma nabila dad'i  tace yauwa yar uwa haka nake so yadda kika ce shi ba autan maza bane kuma ke da samari ke miki cha ai nasan bada jima wa ba zaki sami wanda ya fishi.

Tuni samira ta saka zancen faruk a bayan ranta taci gaba da sabgar ta kamar bata tab'a sanin faruk a duniya ba karatun ta kawai ta saka a gaba haka har suka shiga second semester a shekarar su da hudu, ranan tana zaune a gida suna hira ta kakar su ta wurin mamansu wadda tunda baban su samira ya rasu ta dawo gidan su tana zama dasu suna yar hira, can taji wayarta na kuka alamun ana kiranta tana kallan wayan taga nabila ce ki kira aiko tayi saurin latsa wa ta sa wayan ta kunne hade da yin sallama nabila dake daya bangaran ta tambayi samira me take yi, samira kuwa tace mata bakomin nan nabila ta fara ce mata dan Allah tazo gidan su ta taya su aiki ita da umma Abban su zai yi baki zasu zo dinner ga aiki yayi musu yawa sosai kuma ma unma tace tazo tayi musu daddad'an Shepherd pie dinta samira tayi murmushi sannan tace tom bari ta gaya ma mama

haka samira ta kama hanyan gidan su nabila aikuwa tana zuwa suka fara aiki girki kawai suke saboda ba kadan din mutane ne zasu gidan ba a yau, ga kuma maza da cin abinci haka sukai ta aiki kuma da girkin nabila da ummanta ta barta tayi samira ce tayi saboda nabila ba wani iya girki tayi ba daga magi da gishiri basu jiba sai sunyi yawa haka sukai tayi basu suka gama ba sai wajan 5 na yamma, suna gama wa umma tace musu su je su jera a dinning table dan baki bayan magrib zasu iso, haka su ka dunka jera wa dasu da masu aikin gidan sannan umma tace musu suyi shirin serving dinsu dan baza ta bar masu aiki suyi serving din bakin mijinta ba, su samira suka amsa da toh bayan sun gama jera komai yadda ya kamata nabila tace best friend muje daki mu dan huta ko kansu kara so samira tace yauwa ni har wanka nake so nayi, nan suka kara sa dakin nabila.

Shi kuma ta bangaran gogan naku wato Abdulshakur. Daddy ne ya kira shi a waya tun karfe biyu na ranar Abdulshakur daya ke zauna a office dinshi shi da wasu directors duk aiki ya mishi yawa saboda akwai wani deal da suke so su samu da wani babban company ah America kwanki da yawa baya ma dawowa gida sai kusan 11 na dare aiki kawai yake shi da ma'aika tan shi ba dare ba rana yana haka kawai yaji wayar shi na ringin me kirar iPhone 11 pro max yana dubawa yayi yaga daddy ne ke kiran sa, haka ya tsaida komai ya mike daga wurin saboda akwai mutane ya dan kara gefe sannan ya latsa wayan ya saka a kunnen shi tare da yin sallama, bayan ya gama gaishe shi, nan daddy ya fara masa bayani cewa yasan Naseer Abdullahi? Abdulshakur yace eh wannan dan siyasan me neman takarar governor daddy yace mishi yauwa shi ya gayyace su gidan shi dinner a yau bayan magrib, nan abudulshakur ya fara bama daddy hakuri aiki yayi mishi yawa bazai iya samun daman zuwa ba kan ya kara sa zancen shi daddy ya rufe shi da fada

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now