Chapter thirteen

1.5K 156 0
                                    

Bai dawo gida ba sai kusan karfe biyu na dare, shi kansa bai zata zaiyi irin wannan dad'e war a wajan su khalifa ba, hira sukayi sosai amma ko da wasa baiyi musu maganar samira ba, ita sirrin shi ce yanzu, bai san kowa ya sa ni, ya danne damuwar shi ko k'adan bai bari sun gane akwai abunda ke damun shi ba, dukda akwai tsoro a tare dashi har a lokacin da suke hin hirar, tsoran kar maganar da khalifa ya gaya mishi ta zama gaskiya. Daya dawo gida side dinshi ya wuce, shiga bedroom dinshi yayi ya fara rage kayan jikin shi, ba kai kallon shi kan wayar shi ba da take zaune akan dressing mirror dinshi, saboda in har ya saki idanun shi suka sauka akan wayar to tabbas ya san sai ya dauka ya k'ara kiran lambar ta, a lokacin ji yake ba abunda yake so yaji in ba muryar ta ba, yana haye wa kan gadon shi ya zira ma silin din dake da'kin shi ido, tunanin samira ya shiga yi da yanzu ya zame mishi jiki, in har ya kad'ai ce shi d'aya to tabbas ita zata cika mishi kanshi, yafi awa yana tunanin abu d'aya ko k'adan barci yaki zuwa mai, pillow din kan gadon shi ya dauka ya danna akan kanshi wai ko ya sami saukin tunanin amma abu ya k'i, tsoro ne ya k'ara ka mashi da wani irin fad'uwar gaba, yanzu haka zai ci gaba da rayuwa, wannan sabon abon da yake ji ajikin shi gaskiya masifa ne a gare shi, dole ya fitar da ita gaba d'aya daga cikin zuciyar shi ko ta halin k'ak'a ne, yana cikin way'annan tunanin kawai ya ji kiran sallar asuba, yau ma bai samu baccin ba, yanzu sam sam rashin baccin da baya samu baya bashi mamaki, mik'e wa yayi yai hanyar toilet ya dauro alwala, sallah yayi tare da azkar da duk addio'in shi yana gama wa ya hau kan gado, Yana hawa gadon Allah ya taimake shi bacci yayi gaba dashi.

Rurin da k'arar da wayar shi take yi ita ta tashe shi daga barci mai nauyin da yake, idan shi d'aya ya bude ya fara wai waye yana duban d'akin, wayar shi ya hango akan dressing mirror dinshi tana zuba k'ara, da kyar ya iya samu ya mik'e ya nufi inda wayar take, har lokacin idanunshi basu gama bud'ewa ba saboda akwai ragowar bacci acikin su, yana daga wayar yaga (first ♥️) akan screen din, shi ne sunan da yayi ma mommy saving, latsa wayar yayi ya saka a kunan shi tare da yin sallama, daga dayan b'an garan mommy tace

"Har yanzu banga ka fito ba na aika masu aiki su kai ma breakfast side dinka sunyi sahu yafi biyar baka bude musu k'ofa ba ko baka gidan ne?"

Ta k'arashe maganar da tambaya, abdulshakur ya d'an yi murmushi had'e da cewa,

"ban kwanta da wuri bane shi yasa ban tashi ba amma bari na bud'e musu yanzu"

ji yayi tace

"ai yanzu sai dai lunch wane breakfast kuma bayan azahar tayi, dan Allah ka shirya ka fito ka samu kasa wani abu acikin ka"

abdulshakur yace mata tom sannan suka kashe wayar, yana cire ta daga kunan shi yaga message akan screen din, shiga yayi ya bud'e yana ganin abunda yayi ma samira saving a wurin saman message din idanun shi suka bud'e tangararan, duk baccin da yake ji ya watse, karanta acount details dinta yayi da yake dauke acikin message din, a lokacin da idanun sa suka zo wurin sunan ta wani kyakkyawan murmushi ya saki da bai ma san yayi ba, finally, finally yasan sunan ta, SAMIRA, haka ya ambaci sunan a fili muryar shi cike da murmushi da farin ciki, can kuma ya saki dariya, wato duk yadda tace baza ta aiko mishi da account details dinta ba gashi tayi yanzu, wato duk jan aji ne, ji yayi tayi mutuk'ar burgeshi, shiga cikin app din bankin shi yayi ya kwafe duk details din data aiko mishi ya maida mata da kudin ta, sannan ya ajiye wayar ya nufi bathroom dinshi fuskan shi d'auke da murmushi, ya tabbata in ya fito ya duba wayan shi sai yaga missed calls dinta.

Samira na isa parlor, taga safiya bata nan, kitchen da k'arasa a guje nan ma bata nan, d'akinta ta k'arayi shima wayam bata ciki, can ta jiyo muryarta a d'akin gwaggo, da sauri ta k'arasa, tana shiga sai ga ta abaje akan gado, gwaggo da safiya dake hira jefi jefi kawai suka ji an fad'o daki, wani irin zabura sukayi, gwaggo ce ta tambayi samira ko lafiya ta fad'o mata d'aki ko sallama, bata ma bi takan ta ba, haye wa kan gadon tayi ta kamo kunnan safiya, murd'a kunan ta tayi da k'arfi sai da ta saki wata k'ara

"ban hana ki mun bincik'e a wayata ba iye? tsabar rashin mutunci da kin raina ni"

gwaggo ce ta shiga rik'e hannun samira tana bata hak'uri,

"gwaggo ki k'ale ni, biki san abunda tamun ba ne, na gaji da abubuwan da take mun a gidan nan"

ta juya ta kalli safiya

"dan kinga ina k'alle ki ko, to wallahi kin ishe ni yau sai na koya miki hankali"

haka ta dage ta dunk'a zubama safiya rankwashi, ita kuwa ba abunda take sai faman kurma ihu, mama ce ta shigo d'akin da sauri tana lafiya, tana ganin abunda ke faruwa ta juya ta fice d'akin tabar gwaggo da raban fad'a, ta sa ni sarai, safiya bata da mutunci bata da kunya, duk abinda zata ma samira kawai share take bata tab'a daukan mataki ba wani sa'in har fad'a take mata tace sanyin ta yayi yawa shi yasa duk ta bi ta raina ta, yau tabbas tama ta ba dan k'aramin abu ba, shi yasa ta k'alleta ta jubge ta san ranta yadda baza ta k'ara ba gobe. Bayan samira ta gama zuba ma safiya rankwashi ta k'ara jawo kunnanta da k'arfi suka fito daga d'akin gwaggo, d'akin mama sukayi safiya sai bata hakuri take amma samira tayi kamar bata jin hausa, suna shiga suka tarar da mama tana gyaran gado, cilla ta tayi kusa da mama sannan ta nuna ta da d'an yatsan hanun ta,

"wallahi ki ce mata ta fita daga idona, wayata ba sa'ar wasanta bace, na gaji da walaqanci irin nata, in ba haka ba zan karya ta a gidan nan"

tana gama fad'an ta, tayi waje tare da jawa mama kofar dakin ta kanta fita ta jiyo mama ta fara ma safiya fad'a, sama ta hau dan taje ta kira number din abdulshakur.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now