Chapter twelve

1.6K 170 0
                                    

Bayan ya kashe wayan, wani farin ciki ne ya rufe shi, kawai jin muryarta da yayi, ji yake kamar an yashe mishi bak'in ciki, kamar bai taba bak'in ciki ba a duniya, wani irin dadi da nishad'i yake ji, yayi mintuna yana kwance kawai laulausar murayar tace ke mishi yawa a kwakwalwa, sai murmushi yake shi kad'ai ah daki, da wani zai ganshi ah wannan yanayi zai ce mishi tab'abb'e, shi ko ya zaiyi?, wani irin new feelings yake ji a dukkan gab'obin jikin shi, lumshe idan shi yayi, yad'an jima a haka, sannan ya k'ara sakin wani murmushin, wayar shi yakai dai dai fuskan shi sannan ya kai hannun shi kan lambar samira, iMessage ya aika mata, "kada ki manta ki turo min da account number dinki" yana tabbata wa sak'on yaje, ya a jiye wayar a gefan shi, reflection dinshi yake gani a mirror yayin da yake a kwance, farin ciki k'arara ya gani a idanunshi, tunawa da maganar da khalifa ya gaya mishi yayi,

("kasan Allah randa zaka hadu da someone that is that special zaka kawai ji ajikan ka, sonta zaka yi tsakanin ka da Allah, zaka zamana me san duk wani farin cikinta kuma zaka zaman mai k'in duk wani bakin cikin ta, it's very different bazan iya misalta maka ba, da kanka zaka zo wata rana ka bani labari"),

Gaban shi ne yayi wata mummunar faduwa, duk maganar da sukayi da khalifa ce ta shiga dawo mishi daya bayan daya, wani bari na zuciyar shi ne ya gaya mishi "to kai wani sanin ta kayi da har zaka kira abunda kake ji da SO?, kai fa ba ajin ta bane, kafi karfinta ta ko ta ina, macen da kake so kuma kake so ka aura ita ce macen da kyanta baya misaltuwa, macen da kowa ya gani sai ya jinjina kyanta, macen da zama ta fika kyau kuma kasan wannan abu me wahala ne, yarinyar da kake tunani sam ba haka take ba, bata cikin irin jerin matan da kake so to mene zaka damu kanki?",  ya d'an ji hankalin shi ya kwanta,  sai kuma can d'ayan barin zuciyar shi ya fara gaya mishi nashi, "kai kasan zancen da khalifa ya gaya maka akwai kanshin gaskiya a ciki, me yasa kwana biyu duk ka canza ka lallace saboda mace?, ko barce ishasshe bakayi, gaba d'aya ka dai na walwala, kai a ganin ka me wanan yake nufi?"

Abdulshakur firgit yayi ya mik'e tsaye, zuciyar shi ce ta fara bugawa, wani mahaukacin tsoro ne ya kama shi ta farar d'aya, ya jik'e sharkaf da gumi dukda dak'in shi cike yake da sanyin ac, me yake shirin faruwa dani ne? Ya tambayi kanshi, da yaga kanshi na fara nemar yin ciwo yayi sauri yayi bathroom danyin alwala, gwanda yayi sallah ya mik'a lamrin shi zuwa ga Allah dan abun na nema yafi k'arfin shi.

Safiya kwance take akan kujera a parlor, tv a kunne take amma ba ita take kallo ba, hankalin ta gaba d'aya yana kan wayar samira dake rik'e a hannun ta, ta gama sending pictures din da ta dauka jiya da iman zuwa wayar ta, yanzu kawai bin cike take ma samira a waya ta fad'a can, ta kutsa can, har WhatsApp dinta sai da ta shiga, samira tasan sarai tana mata haka shi yasa bata cika bata wayar ta ba sai dai in har tana wurin, kuma kullum tana cikin canza password amma duk wanda tasa sai safiya ta gane, yanzu ma da ta tambaye ta wayar ta, ta bata abun ya bata mamaki sosai, sai da ta bita da kallo har ta gama haye wa sama, tana cikin danne dannan ta a wayar message ya shigo, ai kuwa zumbar tayi ta shiga, lambar da ba'ai saving ba ta gani, bud'e message din tayi ta ci karo da

"kada ki manta ki turo mun da account number dinki",

haba safiya wani tsalle da daka a zaune, yau ga damar ta tazo, daman ba ko sisi a account dinta tayi broke, yanzu kawai za tayi sending account details din ya samira, in koma wanene ya aiko da kudin zatayi sending wasu account dinta tunda ba lallai tasan nawa bane, tana sending sai tayi deleting, ai kuwa haka tayi, sending gaba daya account details din samira tayi, sannan tayi zaman jiran alert, shiru shiru bata ji komai ba, har kusan minti ashirin, wani takai ci ne ya zo mata, kawai ta dauka y'an scam ne, deleting gaba daya messages din tayi, da wanda aka turo da wanda ta tura sannan ta tashi ta nufi d'akin samira, tana shiga ta ganta a kan stool din da yake had'e da dressing mirror da towel daure a jikin ta, tana shafa mayukan da suke baje akan wurin, mik'a mata wayarta tayi ta kama gabanta, samira binta tayi da kallo, sanan ta juya ta ci gaba da harkar gabanta.

Abdulshakur na idar da salolin shi, ya dan samu saukin tunanin, shiga ban d'aki yayi, sai da ya gama wankan shi tsab sannan ya fito. Sanye yake da towel daure a kugun sa, rage sanyin ac din dake d'kin shi yayi sanan yayi hanyar walk in closet dinshi, daukan wani sweatpants yayi fari had'e da wata riga kamar ruwan toka ta Louis Vuitton, a cikin closet din shi yasa ka kayan, agogon Rolex dinshi ya dauko a cikin drawer din dake dauke ta tsadaddun agogunan shi ya manna a hannun shi, sanan yayi wajan dressing mirror dinshi, ya dauka daya daga cikin designer turararru kan da suke zube a wurin ya feshi jikin shi dashi, key din motar shi ya dauka me k'irar mercedes benz AMG G65 yayi hanyar fita, kobin inda wayar shi take bai yiba, wurin abokanan shi zai je duk da dare ya d'an yi sosai, ya tabbata in har ya zauna a d'akin shi to y'an gidan su zasu iya zuwa su tarar ya zare.

Tunda ta tashi da safe, tayi wanka da yin breakfast ta fara shirin komawa school, dan gobe in ta fara lectures tun safe sai karfe shida na yamma zata gama, jin gabanta ya fad'i tayi da ta tuna gobe dole sai ta had'u da nabila, can kuma ta share zancen ta ci gaba da harkar ta, tunda safiya ta kawo mata wayar ta jiya da daddare ta ajiye ta akan bedside drawer dinta bata k'ara bin takan ta ba, ta sani sarai abdulshakur yace ta aika mishi da account number dinta bata manta ba, ko sama da k'asa zasu had'e baza ta tab'a aika mishi ba duk da itama yanzu bata da wani kud'i a account dinta, ni bari ma na gama abinda nake nazo nayi blocking din number dinshi ta fad'a a kasan ranta, gwaggo ce ta kwala mata kira tun daga k'asa, samira ta bar duk abunda tak'e yi ta sauka dan jin me zata ce mata,

"dauko mun wayar ki kinji ki kira mun kalle (k'anin gwaggo) kwana biyu banji ya wajan su yake ba"

samira tace tom sannan ta k'ara haurawa sama, tana shiga d'akin ta ta nufi bedside drawer dinta ta dauko wayar ta, dannan wayar tayi ta kawo haske, tana bud'e wayar taga alamar an aiko da message shiga ciki tayi danta karanta, tana kai idonta kan message din, gabanta ya fad'i, zaro manyan idanun ta tayi waje, ta tsaya cak kamar wadda tayi mutuwar tsaya bata ko da motsi, bakinta ta hangame, sanan hannun ta ya fara rawa. Fita tayi daga dak'in ta da gudu tayi k'asa, Allah ne kad'ai zai rabata da safiya a gidan nan yau.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now