Chapter forty-nine

1.5K 176 10
                                    

Gaba d'aya manyan ma aikatan kamfanin ma zaune a wurin meeting d'in, abdulshakur na wurin shima ya nustsu yana kallon projector d'in gaban shi hankalin shi gaba d'aya na wurin, saboda business failure d'in da ya samu, tunda ya malaki kamfanin wannan karon ne karo na farko, su kansu ma'aikatan abun ya bala'in d'aure musu kai, dukda dai ba wani business deal d'in zafi bane amma still abun bai yi musu dad'i ba, Abdulshakur laifin shi yake gani saboda kamar kwana nan yana neglecting kamfanin saboda abubuwa da yawa da sukayi mishi yawa, kamar Samira da alamarin ta, tun bayan bikin khalifa kwata kwata bai samu hutu ba bashi da lokacin kanshi, baya dawowa gida sai can dare in ma ya dawo yana kan computer d'inshi yana aiki, daddy yayi fishi dashi har fad'a sai da yayi mishi shi yasa yanzu yake san gyara komi kan abun ya k'ara b'aci.

Suna gama meeting d'in suka fito shima office d'inshi yayi dan ya k'arasa wasu y'an aikin, usman na binshi a baya, yana shiga makeken office d'in nashi ya zauna akan kujera ya bud'e files d'in gaban shi, tare da saka reading glasses d'inshi, sannan ya kalli usman yace yaje ya kira mishi team leader d'in marketing, usman da toh ya amsa amma kan ya fita sai da ya tambaye shi abinci fa dan yanzu har k'arfe hud'u ta kusa, bai amsa shi ba yaci gaba da aikin gaban shi, shi kam da yaji shiru yasan amsar a'a ce.

Wayar shi ce tayi ringing ta tsai dashi daga abunda yake, d'auka yayi yaga sunan mu'azzam a screen d'in, abun ne ya bashi mamaki dan yasan bai cika kiran shi ba, latsa wayar yayi ya saka a kunne tare da yin sallama, mu'azzam amsa wa yayi daga d'ayan ba'angaran amma yadda yake maganar yasan something is off, soboda ba haka ya saba jinshi a waya ba, shiru akayi bayan sun gama gaisawa har abdulshakur ya d'auka ya kashe wayar ne sai da ya d'aga ta daga kan kunnan shi ya duba yaga layin bai katse ba, zai yi magana kenan ya tsai dashi,

"Kana aiki na kira ko"

Mu'azzam a sanyaye yayi maganar, abdulshakur baisan me yasa gaban shi ya fara fad'uwa ba, tsoro yaji ya kama shi haka kawai bai san daga ina ba, jikin shi yanzu ya gama gaya mishi kiran bana lafiya bane,

"A'a bakomi, zan iya amsa waya wani abun kake san gaya mun ne"

A dake yayi maganar amma tsoro ne fal cikin sa, ji yake baya san jin mai mu'azzam zai gaya mishi saboda zuciyar shi ta gama gaya mishi ba maganar d'adi bace, shiru shiru bai ji amsa ba daga d'ayan b'angaran, mu'azzam kamar bazai amsa ba can kuma yace,

"Yanzu awa biyar kenan da ba'a ga Samira ba, mun rasa inda take mun duba ko ina bamu same ta ba har wayarta mun kira mun kira a kashe"

Da wani mugun sauri ya mik'e daga kan kujerar shi har sai da jiri ya kama shi ya ruk'e tebur d'in yanzu zuciyar shi mahaukacin bugawa take, gumi ya gama jek'a shi sharkaf bayan rawar da jikinshi ya fara, inalillahi wani illahi rajiun kawai yake cewa a zuci, wani ciwon kai ne yazo mishi ta farar d'aya, baisan sanda ya kama kanshi ba, yayi shirin jin magana mara dad'i amma ba irin wannan muguwar magana ba, a d'an k'an k'anin lokaci ya nemi nustuwar shi ya rasa, so yake ya tanbaye shi garin yaya amma ya kasa bud'e baki yayi magana, mu'azzam ne ya k'ara cewa,

"Dan Allah alfarma nake nema, nasan kasan manyan mutane da yawa k'asar nan dan Allah zaka iya had'a mu da babban police ko soja wanda zai taimaka mana wajan nemo ta"

Zazzabi ne ke shirin kama shi, me tayi wa wani har yake san cutar da ita haka, me yasa kullum mugayen mutane ke harinta ne wa ta tab'a cutar wa, har lokacin ya kasa bama mu'azzam amsa har su usman suka turo k'ofa suka shigo office d'in, da suka ga yanayin da yake ba wanda ya bud'e baki yayi magana a cikin su, suka ja gefe suka tsaya, sai da kyar abdulshakur ya iya furta,

"Garin yaya, Ina taje, taya ya"

Haka ya jero ma mu'azzam tambayoyi, mu'azzam ya sanar dashi duk abunda ya faru, ta fita wurin wani shikenan bata dawo ba an kira shi yace ai da taje wurin shi bama suyi minti arba'in tare ba,

Yanzu k'walla taf ta cika idanun abdulshakur, duk inda Samira take tana cikin tashin hankali da masifa, ji yake kamar ya fad'i a wurin saboda gab'a d'aya wani iri yake ji a jikinshi, jinshi yake kamar baya numfashi isarshe, lumshe idanunshi yayi da ya tuna yanzu ba lokacin bane dole ya tattro nustuwar shi ya fita ya je ya nemo ta duk inda take a k'asar nan, kai koma k'asar ta bari sai ya nemota a yau d'innan, gaya ma mu'azzam yayi wurin da zaizo ya same shi tare da kashe wayar, ya fara takawa zai zagaya ya fita daga office d'in jiri ya kama shi, sauri yayi ya k'ara ruk'e tebur d'in kusa dashi, sai da yayi mintuna a haka sannan ya fara dawowa dai dai, yana jin jirin ya sake shi ya fita daga office d'in a guje tare da kiran number d'in samira be tsaya bi takan usman ba da yake faman mishi magana.

Gaba d'aya suna office d'in Ahmad abokin su da yake soja major general, yana ma mu'azzam tambayoyi, abdulshakur ji yake kamar yayi hauka a wurin mene zai tsaya sai ya mishi wani tambayoyi ana cewa y'ar mutane ta b'ata an neme ta an rasa, wayar shi da tayi k'ara ce ta katse shi da sauri ya latsa a kunnan shi, daddy ne yake gaya mishi ya kira inspector general of police yanzu zai saka a fara bin cike, tare da ce mishi wani daga cikin family d'in su samira yaje dan zai mishi tambayoyi, yana gama sanar mishi ya kashe wayar tara da cewa Allah ya kyauta kuma Allah ya saka a sameta,

yana kashe wayar ya d'ora hannun wan shi akan fuskar shi, shi k'ad'ai yasan me yake ji, kwalla gaba d'aya ta cika idanunshi, ga tsoro da ya cika mishi ciki, tsoron kada suyi mata wani abun su cutar da ita, magana Ahmad ya fara,

"Yanzu we are going to wait for atleast 3hours muga ko real kidnappers ne, tunda kace yanzu b'atan ta awa biyar, in har sune to zasu  kira su fad'i ransom in kuma basu bane kenan wani ne ya saka a d'auke ta sai mu fara tracking wayarta tunda yayanta yace basu ga wayar ta ba zai iya yuwa sun tafi da ita"

yaji me Ahmad yake fad'a dai dai kuwa, har awa uku za'a jira, in har a awa ukun suka yi mata wani abun fa, sauri yayi ya kulle idanunshi dan bama yasan yayi irin wannan tunani, kallon Ahmad yayi da shima shi yake kallo,

"Yanzu me yasa baza ayi tracking wayar tata ba har sai mun jira awa uku"

Shi kanshi baisan maganar da iho yayi ba sai da yaga ahmad ya d'an yi gefe da kanshi kamar k'ara tayi mishi yawa,

"We don't want to take any chances, yanzu in har mukayi zasu iya mata wani abun koma ba suyi niya ba saboda mun b'ata musu shirin su, dole ne mutsaya mu bi abunnan daki daki it's for her own safety"

Shiru abdulshakur yayi a wurin, mu'azzam ma haka, addu'a kawai yake a ranshi duk addu'ar da tazo mishi yin ta yake, haushin kanshi yake ji da bazai iya yin komi ba saboda shi ba hukuma bane ga Samira na can Allah ne kad'ai yasan halin da take ciki, kallon mu'azzam yayi ya gaya mishi abun da daddy yace tare da gaya mishi inda zaije in yaje ya fad'a yace shi ya aiko shi za'a kaishi har wurin inspector general d'in shi bari ya zauna da Ahmad, yana gama mishi bayani mu'azzam ya mik'e ya fita, haka suka zauna a office d'in jigum shi da abokin nashi ba wanda yayi wa d'an uwanshi magana, abdulshakur da yaga bazai iya ba ya tashi ya fad'a band'akin da yake a cikin office d'in yace bari yayi alwala, yana shiga yana kulle k'ofar hawaye suka fara zuba a fuskar shi, tausayin ta yake ji, in har ba kud'i suke so ba, in har wani abu suke son su cimma akanta fa, yana jin tausayin kanshi in ya rasa samira, in ya rasa ta to tabbas zai rasa zuciyar shi harda gangar jikinshi gaba d'aya, bai jin zai iya rayuwa a doran k'asar nan in har babu ita, k'ara lumshe idanun shi yayi wani sabon hawayen ya sake zuba, in har aka kama wanda suka mata wannan abun bazai tab'a yafe musu ba ko wace irin azaba suka bata sai ya tabbata a nin ninka musu ita ko ma su wane, kuma ko wane mugun mutun ne ya saka su shima sai ya tabbata an hukunta shi dai dai da abun da ya saka aka yi mata, da kyar ya iya yin alwala ya fito.

Banko k'ofar office d'in ahmad yayi bayan sun dawo daga sallar magriba, awa uku tayi amma har yanzu basu ji kira ba alamun kenan ba kud'i suke so ba wani ne ya sasu suyi, in kaga abdulshakur gaba d'aya ya birkice ya rikice, gashin kanshi da yake a kwance duk ya mik'e, idanunshi sun k'ank'ance kana ganin shi kasan yana cikin tsan tsan tashin hankali, Ahmad na ganin ya shigo shima ya mik'e yace suje a fara tracking d'inta, addu'ar shine Allah ya saka su kunna wayar tata, ahmad ko da wasa bai gaya ma abdulshakur sai wayar ta na kunne za'a iya tracking d'inta ba saboda yasan zai iya aika shi har lahira.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now