Chapter twenty-five

1.5K 181 2
                                    

Laptop d'inta nakan cinyoyinta, bayan ta na jingine da pillow, kallo ta saka wani netflix series amma gaba d'aya hankalinta baya wajan, daure wa kawai take amma jikinta baya mata dad'i, bata sani ba ko dan tayi bacci a zaune, ita kanta bata san addadin sallolin da tayi ba jiya, sai bayan asuba da sami bacci shima d'in akan abun sallah bata san lokacin da baccin ya sace ta ba.

Safiya ce ta shigo ta tashe ta wajan sha d'aya sannan a lokacin ta samu ta cire kayan dake jikin ta ta maida wasu marasa nauyi, da ta hau kan gado zata koma bacci kasa komawa tayi, haka tayi ta juyi saboda zuciyarta cike take da tunani kala kala, haka ta hakura da baccin ta fad'a bathroom tayi wanka ta shirya tana sauka k'asa sai ga sallamar farida da nabila, tayi murnar ganin su sosai saboda bama su gaya mata zasu zo ba, haka dai sukayi ta hira tayi musu tarb'a ta mussamman, can suka shiga d'akin mommy suka gaisa da ita, sannan suke tambaye ta in har zata bar Samira taje trip d'innan,

Da Samira taji sai da gabanta yayi mummunar fad'uwa dan ita sam bata san zuwa, daa dai taso taje amma yanzu da ta gane kullum zata saka shakur a cikin idanta shine babbar tashin hankalinta, sam sam bata san wani abu ya k'ara had'a su ko ganin shi bata sanyi saboda tsoro da mugun halin da zuciyar ta zata jefa ta aciki,

Addu'a ta dunk'a yi kada Allah yasa mama ta barta, amma ina mama murmushi tayi tace ba komi, murna kuwa wurin farida da nabaila bata misaltuwa har tsalle sukayi suka rungume samira a tare ita kuwa mama sai kallon su take tana dariya, ta danne dukkan damuwar dan bata so su gane ai kuwa tayi sa'a dan har suka gama suka kama hanyar gida ba wanda ya san akwai abunda ke damun ta.

Tunani take yadda zata b'ullo wa alamarin, ko tace bata da lafiya ne ranar da za'a tafi, har ga Allah tana so tayi wa farida abunda take so amma tana bala'in jin tsoron sake had'uwa dashi, so take yi ta raba zuciyar ta dashi komai wahala, abun bazai tab'a yiwuwa ba in har zata saka shi idanunta har na tsawon sati d'aya,

Ita tasan tashin hankali da azabar ta zata sha in har ta biye musu taje wannan trip d'in,

Kulle laptop d'in dake kan cinyarta tayi dan gab'a d'aya bata gane abunda take kallo hankalinta gaba d'aya baya wurin, idanta takai wurin agogan dake mane a jikin d'akin taga k'arfe goma da rabi, tun takwas ta shigo d'akin amma bata tsinana abun komai ba in banda sallar isha'i da tayi sai faman tunani take da basu da kan gado,

Kanta ne ke wani mahaukacin sara mata saboda rashin samun ishashen bacci, ga kwata kwata yau d'in bata saka abincin kirki a cikin ta ba, cinyoyinta da dago daga kan gadon sannan da d'ora habbar ta akan su tare da rungume cinyoyinta da hannuwan ta,

In ka ganta dole ne ta baka tausayi, har ta d'an fad'a a kwana d'aya, ta dad'e a haka ga kanta dake faman ciwo, zuciyar ta ce ta shiga bata shawara akan me yasa baza taje trip d'in ba k'illa ta sami wani abun a jikinshi da bai mata ba ko taga wani mummana hali da yake dashi ya ke boy'ewa, ance daman baka sanin halin mutum sai ka zauna dashi, watak'il in har tayi hakan komai zai zo mata cikin sauki,

Murna ce ta kama ta saboda ita ta tabbata babban mutum irin abudulshakur bazai rasa munanan d'abi'u ba, wani kwari taji ya zo mata tashi tayi ta fara shirin kwanciya, jinta take kamar bata da wata damuwa.

$$$$$$$$$$$$

Kowa yasan abdulshakur yasan ya canza gaba d'aya ya dawo wani daban, baya murmushi ballantana dariya, ko magana yanzu baya san yi, miskilancin shi ya ninku, yanzu kwata kwata d'an wasan da yake yi da usman ya daina, bama usman tsoro ma yake kullum in ya shigo office d'inshi zai bashi sak'o ko gaya mishi wani abun sauri yake ya bar wurin, kullum fuskar shi a d'aure take ba wasa acikin ta,

Ko Amal da Amra suma ya daina kula su, suma tsoron shi suke ji yanzu dukda manyan shekarun su, kwarjinin shi ya k'aru ya ninninka na da, yanzu wani irin halin ko in kuka ne dashi, ko abokan shi baya wani shiga harkar su.

Mommy da daddy sunyi sunyi ya gaya musu mike damun shi saboda wata irin rama da yake yi amma yak'i har su gama maganar su baya cewa da su k'ala sai da su gaji suce ya tashi ya tafi, da mommy ma ta fara matsa mishi da saka mishi ido barin gidan yayi gaba d'aya ya daina kwana a ciki, sai da tayi kwana biyar bata saka shi a idanunta ba, da taga dai abun na nema yafi k'arfinta shine ta samu ta lallab'a shi ya dawo gida, yanzu kawai ta zuba wa sarautar Allah ido, sai kuma addu'a take yawan yi mishi Allah ya fito dashi daga wannan halin.

Akwatina ne akan gadon shi, packing yake yi saboda yau ne zasu tafi lagos wannan trip d'in, ga flight dinsu 11 ne be samu ya shirya jiya ba saboda aiki da yayi mishi yawa ga bayan ya dawo suka tattra suka tafi gidan Shaheed dan k'arasa planning bikin,

shine ya biya kud'in flight d'in zuwa da dawowa gaba d'aya abokan ango da amarya harda ango da amaryar ma, Ismail da zayyan kuma suka kama musu resort din da zasu zauna, nasir da al-amin kuma su suka d'auki nauyin abinci, mubarak da sauran abokan suma sunyi abunda baza a rasa ba, sun d'auke wa khalifa nauyin komi,

Drawer d'in dressing mirror d'inshi ya bud'e dan daukar maganin baccin shi, dan yanzu gaba d'aya dashi yake rayuwa in har bashi to bazai tab'a iya yin bacci ba, jefa shi yayi cikin akwatin sannan ya rufe ya saukar dasu a k'asa, ajiyar zuciya yayi sannan ya shiga bathroom dan yin wanka,

Bayan ya fito yana shiryawa cikin wata maroon shirt da jeans ya saka rolex d'inshi a hannunshi, yayi mutuk'ar kyau kayan sun fito dashi sosai abunka da farin mutum,

Tunda ya tashi gaban shi yake fad'uwa kuma ya sani sarai me yasa, zai ga Samira yau, ya d'auka baza taje ba amma jiya da suna magana khalifa ya fad'o sunayan k'wayen amarya da zasuje trip d'in harda suna samira,

Yayi ma kanshi alkwarin cire Samira daga rayuwarshi ko ta halin k'aka ne bazai tab'a kai kanshi inda za'a wulaqantashi ba saboda yana da pride d'in shi har number d'inta yayi deleting a wayar shi, gaba d'aya maganar da sukayi da ya zainab ta ruguza mai rayuwarshi, da yasan abunda zai fito daga bakinta kenan da bazai tab'a gaya mata ba, ji yake bashi da sauran farin ciki a rayuwar shi saboda wacce aka ce yana so baza ta tab'a sanshi ba,

Tsayawa yayi yabar abunda yake saboda tsabagen bugawar da zuciyar shi take kamar zata tsage, kullum in zaiyi tunanin Samira to sai ya tsincin kanshi a wannan halin, shi yasa baya tab'a zama shi kad'ai sai dai in har akwai takardun aikin sa,

Wani irin tausaywa kanshi yake ji, da zaka gaya mishi zai yi hauka akan wata kace wata biyar da suka wuce da sai ya maka dariya kuma bazai tab'a yadda ba, tunawa yayi maganar khalifa kwanakin baya da suka wuce, Anya bashi da kambun baka, gaba d'aya maganar da yaga ya mishi ranar na shirin faruwa a gaske,

D'aga kanshi yayi ya kalli POP din d'akin shi ya d'an jima a haka, can kuma ya sauke ya ci gaba da abunda yake, sai da yagama shirayawa tsab ya d'auko shades d'inshi ya d'ora a fuskar shi sannan ya saka muk'ullin motar shi ya fara jan akwatin shi yayi hanyar waje, mommy da daddy zaiyi ma sallama sannan ya wuce inda zashi.

(Ga daishi, samira da abdulshakur basa sa so su SO juna amma kuma aka ce kana taka Allah na nashi, ku biyo ni kuji mai zai faru a lagos dan yanzu aka fara labari and guys kuyi commenting in kuna san picture d'in samira)

BA KYAU BA ✔️Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum