Chapter thirty-eight

1.5K 151 0
                                    

Samira tana shiga cikin gidan su d'akin mama tayi a guje, ko sallama bata yi ba ta fad'a kanta ta rungume ta gam a jikinta, mama dake kan abun salla ta idar da sallah kenan, ta fara binta da kallo, dan tasan dawowar su ba yau bane sai gobe, me ya saka ta dawo yau, bud'e bakin ta tayi dan tambayar samiran

"Ya nagan ki yau? Ba sai gobe zaku dawo ba? Ko kuma baki gaya mun ranar dai dai bane"

Samira da ta fara zubar da kwalla saboda jin dimin uwarta da tayi, wata rahama take ji da wata irin nutsuwa da ta dawo gidan su, dukda bama tayi cikakken minti goma ba acikin shi, k'ara kankame mama tayi a lokacin da duk abubuwan da ta fuskanta a lagos suka fara fad'o mata, baza ta tab'a iya gaya ma mamanta abun da ya faru da ita ba, bata so ta jefa ta cikin damuwa, tasan sai tayi mugun danasanin barin ta zuwa trip d'innan, sai da ta bari ta goge kwallar ta tsab sannan ta d'ago daga jikinta,

"Missing dinki ne yayi mun yawa naga gaskiya bazan iya jira har gobe ba" ta fad'i tare da yin murmushi, mama dariya ta saki ta fara tambayar ta yaya trip da su farida, samira sakin ranta tayi ta fara zuba ma mama hira kamar ba wani abun da ya tab'a faruwa da ita kamar bata da wata damuwa, suna cikin haka sai ga gwagggo itama ta shigo cikin d'akin, tana shigowa ta fara ma Samira tsiya,

"Da yake uwar ki kad'ai kika sani, kina dawowa wurinta kika fara zarcewa kin ma manta damu da rayuwar mu"

Samira sauri tayi ta mik'e tayi wurin da Gwaggo dake a tsaye ta rungume ta, harda d'an jujuya ta,

"Kiyi hakuri gwaggo na, yanzu nake shirin zuwa wurin ki, kinsan bani da wacce ta fiki" tayi maganar tana dariya, mama itama dariyar take,

"Ni d'aga ni kada ki k'arasa ni, daman ai duk dad'in baki kin iya shi" Gwaggo ta fada tare da ture Samira daga jikinta, haka ita da mama suka sake sakin wata dariyar sannan suka sami wuri suka zauna, suka ci gaba da hira, safiya bata nan wai taje gidan k'awarta, haka da sukayi ta y'ar hirar su, gwaggo na bata labarin shegan takar da safiya ta zuba a gidan da bata nan, basu suka mike ba sai da aka fara kiran sallar la'asar.

Samira na shiga cikin d'akin ta tayi wata irin ajiyar zuciya, an shigo mata da akwatin ta da handbag d'inta da ta bari a waje, wurin Jakarta tayi da sauri da taji wayar ta na ringing a ciki, addu'a ta fara Allah ya saka nabila ce, dan ta kira ta yafi sau takwas bata d'auka ba, bayan ta koma gidan bata tarar da ita ba, wai flight d'in 9am tabi ta dawo kano, kuma tun 7 ta fita daga gidan,

Tana dubawa kan screen d'in taga sunan farida, bata ji dadin abun ba taso ace nabila ce, amma haka ta latsa da danna wayar a kunnanta tare dayin sallama, farida daga d'ayan bangaren ta fara yi mata ya gajiya hanyar, har ta saka ta a speaker suka gaisa da sauran k'awayen nasu suma suka mata gajiyar hanya, suka ce mata suna nan dawowa suma gobe, sai da suka gama wasa da dariyar su sannan farida ta cere ta a speaker ta koma gefe ta fara ma Samira magana a hankali, k'ara bata hakuri tayi saboda duk ta sanadiyar tace, kuma ta mata alkwarin baza ta ga Ismail a bikinta ba kada da damu, samira bata ce komi har sai da ta gama sannan kuma tace mata bakomi, sukayi sallama suka kashe wayar,

Komawa tayi jikin gadon ta ta zauna tayi jigum, kallon kanta take a mudubin dressing mirror d'inta, ko ba'a gaya mata ba tasan ta canza, a yini d'aya kawai ta fad'a, tayi mamakin dasu gwaggo basu tambaye ta ba, maida kallonta tayi kan wayar ta ya k'ara danna kan number d'in nabila, yanzu gaba d'aya switch off,

Hawaye ne suka cika idanunta taf, shikenan ta tarwatsa kawacen ta dana aminyar ta, tabi son zuciyarta ta afka babar k'awarta a cikin mugun hali, Allah wadai da masu irin halinta, taji kunya ita kam, hawaye ne suka sake zubowa, ajiye wayarta tayi akan gadon sannan ta kama kanta da yake mugun sara mata saboda stress da rashin baccin da bata samu tayi ba,

Tana lumshe idanunta abdulshakur ne ya fad'o mata rai, gabanta ne yayi mumunar fad'uwa, fuskar shi ta tuno lokacin da ya shigo d'akin su, ranshi yayi mutuk'ar baci maganganun da taga ya mishi da kuwa marin shin da tayi, baza ta tab'a iya tsanar shi ba kuma bata so ta ganshi cikin halin nan, amma ya zatai dole ne ta ja layi dan taga suna so su wuce gona da iri, tana san farin cikin masoyanta fiya da nata, tana san farin cikin nabila kuma tasan farin cikin ta shine ta sami abdulshakur,

Wasu hawayen masu zafi suka sake zubo mata, ya zatayi, zuciyar ta na san ta kasance dashi, zuciyar ta nasan shi tare da ita, zuciyarta na kwadayi da muradin sa, zuciyarta bata san yayi tarai ya da wacce ba ita ba, kuka ne me k'arfi ya kwace mata, ta shiga uku ta lallace, haka dama so yake da muguwar azaba, tayi tunani zata iya cire shi daga cikin ranta amma ina ya bi duk jinin jikinta ya shiga cikin zuciyar ta ya rufe da kwad'o da muk'ulli ta ciki, baza ta tab'a iya budewa ta fito dashi ba,

Tana so ta barma nabila shi har abada, dole da saka zuciyarta ta hak'ura komai azabar da wuyar da zata sha, dan nabila ce ta fara ganin shi kuma ita da fara sanshi,

Kuka samira take yi wiwi, ga ta sa hannunta a k'irjinta sai dukan shi take tana fad'in,

"Me yasa bakya jin magana ta nace ki bar sanshi, ki fitar dashi daga ranki, dan ba naki bane kuma bazai tab'a zama naki ba, dan Allah ki fitar dashi daga rayuwar ki" yadda take a wurin kamar tab'arbiya gaba d'aya ta rikice,

Wani mugun zazzabi taji yana shirin kamata, ga ciwo da kanta yake yi kwakwalwarta nasan samun hutu daga gareta amma ko ajikinta, kuka kawai take rerawa me d'auke da tausayin gaske, yaushe rayuwar ta koma haka, yaushe ta fara hauka akan d'a namiji, ace mutumin da ta sani cikin k'ankanin lokaci ne ya wargaza mata rayuwarta haka, me ya tab'a had'a su da har soyyayar shi tayi k'arfi a cikin zuciyarta, ta tsani maza masu irin halinshi amma tayaya ya samu shiga cikin zuciyar ta har yayi mata irin wannan mugun kamu, tana cikin tsaka mai wuya.

Hawaye yanzu sun gama yiwa fuskarta wanka, fuskar ta jik'e sharkaf, tunda take a rayuwarta yau ne ta tab'a yin dana sanin sanin nabila, da bata santa ba da a guje zata k'arbi soyayyar shi, ta fitar da zuciyar ta cikin wanin muguwar azabar da take sha,

Ta dade a zaune a wurin tana kuka, sai da tayi kuka me isar ta sannan ta mik'e dan shiga bathroom ta d'an watsa ruwa saboda gaba d'aya bata jin dad'in jikinta, tana mik'ewa jiri ya kwashe ta, sai ji tayi ta zube a k'asa a sume.

BA KYAU BA ✔️Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt