Chapter forty-seven

1.4K 171 11
                                    

Sanye yake cikin bak'in yadi kana ganin shi kasan mai mugun tsada ne, ga babbar rigar tasha aiki, yayi masifar kyau da ma ga fari kamar balarabe, sauri yake dan yana so ya makara zuwa d'aurin aure, muk'ullin motar shi Range Rover ya d'auka yayi hanyar fita.

Yana isa gidan su farida dan anan za'a d'aura auran yaga abokan su a tsaye kowa yazo shine na k'arshe, fitowa yayi ya fara takawa a nitse har ya isa wurin suna gama gaisawa suka k'arasa cikin gidan,  basu d'ade da shiga ba aka d'aura aure, Alhmdulillah, a squad d'insu yanzu uku sunyi aure, da nasir da Ahmad da kuma khalifa, cikin gidan su farida suka shiga sai da aka gaisa nan ma aka d'auki hoto sannan aka tafi wurin reception anan Afficent, shima akayi buduri, sai da aka gama abdulshakur yayi ma sauran sallama dan yana da wurin zuwa.

Tunda ga nesa ya hango wata a tsaye a gaban gidan kamar an hanata shiga ne, k'ara ku'ura ido yayi yaga kamar motar samira, in har Samira ce tsaye a wurin baisan me zaiyi ba, yana k'ar yin gaba kuwa yaga ita ce, da wani mugun sauri yayi parking motar shi a gefe ya fito, wani abu ne ya tsaya mishi a mak'oshi, me take a nan, jiya bata ga wulaqan ci da cin mutuncin da aka mata ba, wani irin tafasa zuciyar shi take ranshi a mugun b'ace, yana ji ko jiya ranshi bai b'aci ba kamar na yau kuma jiya ranshi yayi bala'in baci, idanunta na kallon gate d'in gidan,

"Me kike yi anan"

Muryar shi sosai na d'auke da b'acin rai ga fuskar shi a d'aure ba wasa, gani yayi ta firgita ta juyo da sauri, yana ganin fuskarta ta nuna abun mamaki can kuma ta had'e ta, ta juya tayi banza dashi, abdulshakur k'ara zafi zuciyar shi tayi, ya k'ara k'ullewa,

"Kina so kice mun jiya cin zarafin ki da tayi be miki ba shine yau kika k'ara takowa zuwa gidan su"

Da iho yayi maganar har saida Samira ta k'ara firgita, k'ara yin banza tayi da shi, ran abdulshakur ya k'ara b'aci, ya tsani yana mata magana tana banza dashi,

"Wai zafin ki kawai akai nane, ni kad'ai kike kalla ki gasa ma magana, kina ganin maganganun da tayi miki" ya nuna gidan su nabila, "Ni kaina da bani aka yiwa ba sai da suka mun ciwo harda marin ki tayi amma baki ce komi ba yau kika k'ara zuwa inda take, Ina pride d'inki ne"

Yanzu fad'a yake sosai, idanunshi sunyi ja jaa wur kai har farar fuskar shi tsab'ar baccin rai, yadda Samira ke frustrating d'inshi ba wanda zai iya kai shi k'arshen bangon da take, yana gani ta juyo da sauri,

"In nazo gidan babbar k'awata ba gidan ka nazo ba, wannan tsakani ni da ita ne kuma ma wai sau nawa zan gaya maka ka daina shiga harkata,

Itama ihon take yi mishi, bayan wani mugun kallo da take binshi dashi, lumshe idanunshi yayi ko zai sami nustuwa, gaba d'aya haushin ta yake ji, baya ji tunda suka had'u ya tab'a jin haushin ta irin na yau, maganar da tayi ce ta saka shi bud'e idanunshi,

"Ka daina yi kamar I am your responsibility, ka daina yi kamar akwai wani abu a tsakanin mu, ba abunda ya had'a ka da ni, you should mind your business"

Tana gama maganar ta dubi wayarta ta danna ta saka a kunne sannan ta matsa gefe, yanzu har duhu duhu yake gani tsabar yadda zuciyar shi ke zafi da tafasa, share ta yayi yai wurin motar shi, ya shiga ya kunnanta sannan ya maida hancin motar wurin gate d'in su nabila ya danna horn, yadda yake danna horn d'in kana ji ba lafiya ba, me gadi da sauri yazo ya bud'e mishi, haka ya fusge motar yayi cikin gidan har yana tayar da k'ura.

Ko da yayi parking a harabar gidan bai fito ba, wayar shi ya d'auko ya danna kan number d'in nabila, tana ringing na d'aya ta d'auka, muryar shi a had'e ya sanar da ita yana waje tayi sauri ta fito tun kan ta amsa ya kashe wayar. Gani yake abunda yayi mata jiya yayi mata mugun sauk'i yau dole ya nuna mata Samira is off limits bata isa ta dunk'a wulaqanta ta ba, ba ayi minti biyar ba sai gata ta fito tana ta k'wad'i da yanga, wani irin haushi ta k'ara bashi, fitowa yayi daga cikin motar dan bama ya san ta shiga.

Tana k'arasowa ta fara washe mishi baki, abdulshakur k'ara had'e fuskar shi yayi dan he's not here to play,

" ya ka tsaya a waje, ai da ka shigo ciki"

Tayi maganar cikin muryar iyayi, da zata gane duk abunda take ba burgeshi take ba da ta daina wahalar da kanta, mai da idanunshi yayi kanta,

"Kinsan kina da bak'uwa a waje an hana ta shigowa"

K'ura mata ido yayi yana jiran ta bashi amsa,

"Eh na sani, we have nothing to do with each other anymore shine naga mene point d'in ta shigo"

Abun ya bala'in d'aure mishi kai da b'ata mishi rai, bata d'auki k'awancen su a bakin komi ba kenan, bayan d'ayar tana mugun so su sasanta dan a ganinta sab'ani suka samu, wani irin san Samira ya k'ara kama shi, gaskiya ita daban ce, bai ji akwai mata irin ta yanzu a duniya, k'ara maida idanunshi yayi kan samira,

"Be honest with me, duk rayuwar ki da ita have ever considered her as a friend"

Dariya ta saki,

"Eh mana, amma taso ta k'wace ka daga wuri na, dan haka tayi mun babban laifi,"

Shi yasa ko sau d'aya nabila bata tab'a burgeshi ba dan hankalinta ragage ne, bata da tunani ko guda d'aya ga bata da kamun kai, duk shegan takar da take yi a garin nan ya sani da wani bun mazan da take da bun malaman da take, yasan komi, mai da nustuwar shi yayi kanta sannan ya fara cewa,

"Let me make myself clear, ni da ke ba abunda zaiyi working tsakanin mu, bana sanki kuma bazan tab'a sanki ba balle har ta kaimu da aure, abu na biyu, samira bata tab'a cewa tana so na ba, ni k'ad'ai na ke kid'ana da rawa ta bata shiga ciki, abunda kike mata ba dai dai bane dan bata da laifi, abu na uku, bazan k'ara tsayawa naga kina cin mutuncin ta ba, dan she's the woman I love and adore, I want to spend the rest of my life with her dan haka kada ki saki ki k'ara walaqanta ta dan wallahi tallahi bazan d'auka ba kuma bazan kyele ki ba"

Yana gama fad'a ya bud'e motar shi ya shiga ya barta a tsaye, ko kukan da take bai gani ba dan ko ya gani ba kula ta zaiyi ba, kunna motar yayi ya fita daga cikin gidan a guje.

(Almost done with this novel 😌 Ina ga baifi chapters biyar bane suka rage in ma sun kai kenan,

Please vote and share ❤️)

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now