Chapter twenty

1.7K 160 0
                                    

K'arfe takwas ya isa gida, har yanzu jikin shi a sanyaye yake, sai tunanin kukan samira da ya cika kanshi, yana parking motar tashi be ma shiga gida ba yayi masallaci, sai da ya gama me zaiyi a can sannan ya koma, daddy baya nan so side din mommy ya fara shiga ya tarar da ita da amra da amal zaune a pallor suna kallo,

Durk'usawa yayi ya gaida mommy, itama amsa mishi tayi da fara'a amal da amra suma gaida shin sukayi, mommy ce tace mishi ya k'arasa dining yaci abincin dare, amma abudulshakur sam yak'i, yace mata ya tsaya yaci abinci a wani wuri, haka ta hakura dashi, yayi mata sallama ya nufi nashi side din.

Yana shiga bedroom dinshi ya fara cire kayan jikin shi sannan ya shiga bathroom, wanka yayi sosai dan ya dad'e a ban d'akin, yana fitowa ya wuce closet dinshi yayi shafa shafan mayukan shi, sannan ya dauki shirt din da samira ta siyo mishi da wani 3 quarter ya saka a jikin shi, da yazo daidai standing mirrior dinshi ya kalli kanshi ya saki murmushi,

Rigar da kika siyo mun tayi mun kyau sosai dama zaki gani da idanunki, murmushi ya ci gaba da yana shafa rigar kamar samira ce ke kwance a k'irjin shi, ya d'an jima haka.

Can kuma sai ya h'ad'e fuskar shi, samin wuri yayi ya zauna a bakin mak'eken gadon shi, duk hannun shi biyu ya saka ya rik'e kanshi tare da lumshi idanunshi.

Tunani abunda ya faru d'azu ya shiga yi, kukan samira da yadda hawaye ke zuba d'aya bayan d'aya a fuskar ta,

Tambayar kanshi ya fara yi, me yasa ya shiga cikin tashin hankali da ya ganta tana zubar da hawaye, bai tab'a jin abunda ya ji ba lokacin da ya kalleta yaga hawaye na kwarara a idanunta, lokacin da ya ganta a cikin yanayin lokacin ya gane, baya so ya ganta acikin bak'in ciki ko mai k'ankantar shi, baya so ya ganta halin da ya ganta a d'azu, me yasa yake son ya dunk'a ganinta cikin farin ciki, me yasa ya dunk'a jin zafi da ciwo a cikin zuciyar shi, me yasa yaji kamar hawaye za su zuba a fuskar shi a lokacin.

"Saboda kana SONTA" wani b'ari na zuciyar shi ne ya amsa mishi,

Gaban shi ne ya fadi, zuciyar shi ce kawai ke wani mahaukacin bugawa, Inna Lillahi wa inna ilayhi raji'un, ya fara yi a ranshi, yanzu tabbas ya fara yarda yana santa,

Shi dai bai tab'a soyayya ba, be san haka take da zafi ba, be san haka soyyaya keda rad'ad'i ba,

Baya so zuciyar shi ta so samira saboda har cikin ranshi yasan zai sha bak'ar wahala, jikin shi na gaya mishi baza ta tab'a sanshi ba, ko zata soshi ba nan kusa ba,

Kanshi ne ya fara saramai, zai fara yi mishi ciwo, d'aga kanshi yayi da yake jikin hannunshi sannan ya k'ura ma mirror din d'akin shi ido, idanunshi sun k'ad'a sunyi jaa tsabar tashin hankalin da yake ciki, murmushi ya sakar ma kanshi duk da halin da yake ciki

"Abudulshakur ina jin tausayin ka" ya fad'a fili,

Mik'e wa yayi ya dauko abun sallah daman yayi alwala da ya gama wanka, ya fara kaiwa Allah kukanshi da kuma neman sausauci acikin ranshi,

Yana idar da sallolin shi ya fad'a kan gadon shi, yanzu wayam ya ke jin kanshi, bak'in cikin shi ya ragu sosai, ya sami nutsuwa, yana rufe idan shi ya tuna da fuskar samira, yadda take cikin walwala da fara'a lokacin da tayi mai sallama zata wuce gida, wani murmushi ya k'ara saka, tunawa yayi yanzu kullum zai ganta in har tana da lectures, haka yayi tayin tunanin ta baisan lokacin da bacci yayi gaba dashi ba.

$$$$$$$$$$$$$

Samira zaune take a gaban tv ta saka bowl din fruit salad sai sha take hankalin ta kwance, safiya da gwaggo suma da suk'e parlor din sai dai su kalle ta su girgiza kai, kowa a gidan nan yasan in tana period cin masifa ne da ita,

Suna zaune suna ta kallo da hira a parlor har mama da ya muazzam suma sun shigo, sai wurarin k'arfe goma samira ta mik'e daga zaman dirshan da tayi a gaban tv,

Mai da bowl din da tasha fruit salad tayi kitchen had'e da dauraye shi sannan, ta koma tayi wa mama da gwoggo sai da safe dan tana so tayi k'aratu kafin ta kwanta sun kusa fara test.

Tana hayi wa sama band'aki ta fad'a ta k'ara yin wani wankan sannan ta fito daure da towel a jikinta, dressing mirrior dinta ta nufa dan yin abunda da saba shima nan tana gamawa tayi drawer ta dauko kayan bacci, wata doguwar riga ce da ta tsaya mata a gwiwar ta,

Bude drawer din ta take ajiye books dinta ta dauko su sannan ta koma kan desk kamar dai study chair and table da yake a gefe a cikin d'akinta, bata karatu a kan gadon ta saboda baccin da take yi,

Samira na bud'e books dinta ta fara karatu kamar gaske amma komi baya shiga, tunda da dawo gida ta zama busy saboda tasan in har ta k'aidaice to tabbas sai tayi tunanin shakur,

Idanunshi ta tagani d'azu a mota sun kasa barinta tayi sukuni, yadda ya zuba mata manyan rikitattun idanunshi kamar, kamar, sauri tayi ta girgiza kanta, ba taso ta kainan,

Yafi k'arfinta ta ko ina, kuma aminyar ta na hauka akanshi, tana mutuwar k'awnarshi, ajiyar zuciya tayi sannan ta k'ara taro nutsuwar lta ta maida kan litattafan ta dake baje akan table din,

Jikin ta taji yayi sanyi da ta tuna yadda yake shafa hanayen ta a hankali da kula, yadda taga damuwa k'arara a fuskar shi,

Hannunta na hago ta saka ta d'an mari kanta a fuska har sau uku,

Samira in har kika biye wa zuciyar ki zata kaiki ta baro ki, zata sa ki kizama macuciya wadda taci amanar babba aminyar ta, me yakai wanan abun kunya, ta yi maganar gaba d'aya a cikin zuciyar ta

Kwallar da ta fara zubo mata ta saka hannu ta share, tayi alkwarin baza ta tab'a barin zuciyarta taci galaba akanta ba, komai wuyar ta zata sha, ko mutuwa zatayi,

Tana gama wannan tunanin ta k'ara maida hankalinta kan karatun da take, yanzu kuwa ba laifi tana d'an ganewa.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now