Chapter thirty-six

1.5K 165 4
                                    

Suna shiga parlor d'in Samira ta samu wuri akan kujera ta zauna sannan ta sunkuyar da kanta ta fara kallan carpet, yanzu wata irin azababbiyar kunya take ji bayan ta shigo cikin gidan, tana ji matar tana tambayar ta tana jin yunwa, amma tama kasa d'agowa ta kalle ta ballanta ta bata amsa,

Zainab kyaleta ta tayi ta kwad'a ma me aikinta kira, me aikin na isowa parlor din ta ce mata takai samira guest room, sannan tayi mata duk abunda take so ita bari taje ta had'a mata abinci, haka kuwa akai, suna isa cikin d'akin Samira tayi wata irin ajiyar zuciya, ita kuwa me aikin bathroom ta wuce ta fara had' a ma Samira ruwan wanka, tana fitowa tace mata ta gama, har zata fita, samira tayi saurin jawo hannunta,

Ita dake yin period tana buk'atar abubwa da yawa, haka ta danne kunyar ta ta fara gaya me aikin abubuwan da take buk'ata, wurin dressing mirror tayi ta bud'e mata drawer, ba abunda babu, su toothpaste, toothbrush, harda pad

"Hajiya na yawan sawa a ajiye irin wannan abun In case the guests need it, amma bari naje na kawo sauran abun da babu kin d'an tsaya" me aikin tayi magana da broken hausar ta tana had'awa da turanci,

Tana fita ba'a dade ba matar ta shigo, d'auke ta wata leda a hannunta, tana kallan samira ta fara murmushi sannan ta dank'a mata ledar, tace tayi sauri ta fito daga wankan abinci na jiran ta, tana gama fad'a itama ta fuce daga d'akin, samira haka ta fara fito da kayan ledar, rigar bacci ce, da wasu dogayan riguna masu kyau guda biyu, tare da mayafin su, harda sabbaun panties, da ointment d'in da zata saka a ciwon bakin ta, kunya ce ta sake rufe ta, sauri tayi ta tashi ta shiga band'aki,

Bayan ta fito daga wanka ta shirya tsab a cikin rigar baccin ta, yanzu taji dad'in jikinta, taji an k'ara turo k'ofa an shigo, me aikin ce d'auke ya tray d'in abinci, haka ta ajiye shi a gaban Samira sannan ta fara zuba mata a plate, d'an kad'an Samira tace ta zuba, tana k'ara fita ta sauko daga kan gadon ta fara cin abinci, d'an k'adan ne ta samu ya shiga, sannan ta mik'e ta hau kan gado da shirin bacci,

Tana kwanciya tayi shiru, duk abunda ya faru yau ne fad'o mata d'aya bayan d'aya, yau Allah ya taimake ta da tuni shikenan, Sabin hawayene ya fara zuba a kuncinta, tana cikin tunanin kawai nabila ta fad'o mata rai, samira zumbur tayi ta tashi daga kwanciyar da take,

Taya akai ta manta ta rayuwar nabila, gaba d'aya ta manta da babbar aminyarta saboda bata cikin hayyacinta, k'ara tunawa tayi lokacin da abdulshakur yaja hannunta tasan farida da nabila na d'akin, sa hannu tayi ta ruk'e kanta da ya fara sara mata, nabila wacce ke mutuwar san abdulshakur, nabila wacce ke hauka akan abudulshakur, taga babbar k'awarta wacce ta yarda ta ita tabi saurayin ta, wasu hawayen ne suka k'ara zubowa daga fuskar Samira, tasan duk inda nabila take tana cikin kunci,

Sauri tayi ta mik'e ta dauki katon hijab d'innan ta mayar jikinta, yanzu ba abunda ke ranta ila taje taga halin da ta jefa aminyarta, dole kowa ya zata akwai wani abu a tsakanin ya da abdulshakur yadda suke rik'e da hannun juna har suka bar cikin gidan, abunda take gudu yau ya faru, ta shiga uku,

Tana fitowa a corridor d'in tayi kicibis da matar gidan wacce har yanzu bata san sunnan ta ba kuma baza ta iya tambaya ba, zainab da ta fito kashe fitilun gidan da tsaya tana kallan samira, wacce hawaye ne ke zuba a fuskarta, sauri tayi ta k'arasa wajanta ta kamo hannunta ta fara tambayar ta lafiya, itama lokacin hankalinta ya fara tashi yadda taga Samira duk a rikice,

Samira kallantan tayi ta hawaye sun cika idanunta

"Dan Allah ki bani kud'in taxi zan koma inda muka sauka akwai abunda nake sunyi wallahi bani da komi ajiki na ban fito da komi ba dan Allah ko ranta mun ne kiyi" tayi maganar ta sauri ga hawayen da basu bar zuba daga idanunta

Zainab zuba mata kallo take, ta fara tambayar kanta me ya faru ne, tasan zuwan su nan ba lafiya ba yadda taga har bakin yarinyar a tsage, amma bata tambaya ba saboda bata san takura mata, kuma tasan ta tambayi abdulshakur bazai tab'a gaya mata ba,

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now