Chapter fifty-two

1.7K 185 8
                                    

Yana tsaye a harbar gidan su kunnen shi d'auke da waya kana gani shi kasan yana cikin tsan tsan farin ciki, sai washe hak'ora yake yana sakin murmushi kana gani kasan yana bala'in jin dad'in wayar da yake da na d'aya b'angaran, yanzu ita ce sana'ar shi, in har baya tare da samira to suna waya ne, kowa ya rigada ya sani an sallama musu,

Jiran fitowar amra da amal yake wanda tun d'azu ya shiga side d'in mommy ya sanar dasu yana waje, wani abu aka k'ara fad'a daga d'ayan bangaran da ya sashi sakin dariya, sosai wayar na yi mishi dad'i, bai dad'e yana tsaye ba sai ga y'an biyun sun fito, dukan su na sanye da abaye, Amal navy blue amra black, yana hango su daga nesa ya sanar da ita gashi ma sun fito, yanzu zasu k'araso gidan nasu in har ba taraffic sukayi sallama duk da bai so ba amma ai yanzu zai saka ta a idanunshi, bud'e motar yayi ya shiga a lokacin y'an biyu suma suka iso suka bud'e suka shiga.

Sati uku da gano samira da akai, ko da abdulshakur ya ga harda had'in bakin ismail abun yayi mutuk'ar yi mishi ciwo, ace a banza ya b'ata rayuwar shi da wayon shi saboda son zuciya, da sauran abokan shi suka ji labarin suma abun yayi mutuk'ar sosa musu zuciya, ba yarda suka iya haka aka jefa ismail a prison da duk wanda suka kama a daran ranar saboda abunda ya cancanta dasu kenan, ta b'angaran nabila kuwa ita tana wurin hukuma abunda ta aikata yayi mutuk'ar girgiza duk wanda ya santa barin wanda suka santa tare da Samira, bayan sun gano ita ce musababbin had'a kumi ba rok'an da Samira da batayi mishi ba da dan Allah kada a tab'a ta, a kyaleta duniya zata nuna mata saboda a cewar ta iyayenta masu mutunci ne zai yi musu mugun ciwo ace suga y'ar su a cikin wannan halin, shi wallahi samira mamaki ta bashi, ace bayan halin da ta jefa ta amma har yanzu bata daina damuwa da ita ba, ranar kuwa sai da sukayi fad'a dan shi kwata kwata bai yarda da abun da tace ba, sai da tayi kwana biyu bata mishi magana sai can daga baya ta sauko.

A sati uku kawai shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin abdulsahkur da Samira, soyyarsu suke sha hankalin su kwance, kowa a gidan su Samira ya sanshi yanzu ya kuma san da zaman shi haka itama a gidan su, y'an biyu ne suka damu suna so su ganta, su kuma duba ta, itama d'in haka ne daga wurin ta, shi ya saka yau zai kaisu wurin ta su gana. Mommy ma ta damu tana son ta ganta shi ya saka ma in yazo d'aukar y'an biyu anjima da ita zai tafi ta ganta.

Shiga cikin gidan su Samira yayi ya sami wuri yai parking, yana kashe motar ya d'auki Waya ya k'ara kiranta, yana jin muryarta ta d'auka yaji wani dad'i ya ratsa ko wane sansa na jikinshi har saida ya lumshe idanun shi, santa da jinta yake a cikin k'asan zuciyar shi, ita k'ad'ai yake muradi a duniyar nan,

"Sweetheart muna waje"

Yadda yace sweetheart d'in a wani hankali, yayi k'asa da deep voice d'in nan nashi, ya tabbata ya kashe ma samira jiki saboda sai da ta dad'e bata amsa ba, can tace mishi gata nan fitowa sannan ta kashe wayar, ba'a dad'e ba sai gata ta fito sanye da k'aton hijab, yana ganinta ya fara washe baki, ji yake kamar bai tab'a farin ciki ba sai yau, su kuwa y'an biyu da suke cikin motar sun bishi da kallo, wallahi dariya yake basu kamar ba Ya abdulshakur d'in da suka sani ba, yanzu kullum fuskar shi a sake d'auke da fara'a ba kamar daa ba,

Samira bata bi ta kanshi ba, wurin amra tayi dake gaban mota ta bud'e mata k'ofa tare da bud'e k'ofar amal da take baya, suna fitowa ta had'a dukan su ta rungume tana sanin ku da zuwa y'an k'ane na, shi kuwa abdulshakur abun be mishi dad'i ba, taya za'a ce tayi banza dashi bayan tasan yadda yake missing d'inta dukda jiya da daddare suna tare, attention sosai ta bama amra da amal a wurin tana ta musu hira can sai ga safiya ta fito, gaishe shi tayi sannan ta samira had'a ta dasu tace su shiga gida tana zuwa, a ganinta tasu zata zo d'aya tunda shekarun su kusan d'aya ne, tana ganin sun shiga cikin gida ta maida hankalinta kan abdulshakur wanda ya fito daga cikin mota ya kasa d'auke idanun shi akanta sai kallon ta yake, itama kallon shin tayi,

"Me yasa kullum in muna tare baka dai aiki sai kallo, baka gajiya ne"

Dariya taji ya saki, har dimple d'inshi sosai sai da ya fito, ita kuwa binshi tayi da kallo,

"Bazan tab'a iya daina kallan ki ba har kina kusa dani, shi yasa ba abunda nake so a yanzu irin in malakeki ki zamo matata yadda zai zamto safa rana ina saka ki a cikin idona"

Yadda yanzu ya saba yi mata magana haka yayi mata, wace zata sakar mata da gwiwoyi, shi yasan bata cika son su kasance tare ba, saboda baya barinta in har ba gani yayi ta susuce da kalaman shi ba, sunkuyar da kanta yaga tayi ai kuwa, yadda take jin kunya abun ya k'ara mishi dad'i haka ya ci gaba da mata surutu kamar an k'ara kunna shi, sun dad'e suna hira sannan sukayi sallama yace zai dawo kamar wurin eight.

Bayan yaje gidan khalifa shi da sauran abokan nashi, hira suka d'unk'a yi bai fito daga gidan ba sai da yayi jam'in sallar isha, yana shiga motar shi ya d'auki wayar shi ya kira samira ya sanar da ita yana hanya, kan ya k'arasa sai da ya tsaya a Pizza Hut da yogurberry yayi take away, yasan safiya akwai san jin dad'i shi yasa kullum in zaije sai ya tafar mata da abun taunawa a baki.

Da ya isa gidan yayi parking zai da ya fito ya shiga ciki ya gaida mama da Gwaggo, sannan ya fito zaman jiran sauran su fito, bai dad'e ba sai ga su sun fito dukan su, samira itama yanzu abaya ce a jikinta maroon, tayi wa b'akar fatarta kyau sosai, fuskar ta na d'auke da make up ba da yawa ba amman tayi masifar kyau, abdulshakur rikicewa yayi, dole azo a saka ranar bikin su nan kusa in ba haka ba akwai babbar matsala, suna iso wa ya bud'e motar ya dan k'awa Safiya sak'onta, godiya ta shiga yi mishi, yana ganin samira tana banka mata harar ta yi mitar ya daina kashe kud'in shi akan safiya har ta gaji dashi, haka suka shiga mota suka kama gidan su abdulshakur.

$$$$$$$$$$

Kowa a family d'in su abdulshakur na mutuk'ar ji da Samira, yanzu sun saba sosai da k'annan shi da yayyanshi ko ya khadija wacce bata tab'a gani ba dukda suna yin FaceTime wani lokacin, samira ta farar d'aya ta shiga ran mommy, yanzu mommy ta maida ita kamar y'arta, ga itama yarda take ji da ita, tunkan ayi auran ta malake zuciyar kowa harta daddy, dan kullum tana cikin girka mai abincin gargajiya da yake so tana aiko mishi har mommy tace yanzu baya san cin girkin ta,

Shi kuwa abdulshakur sanda yake ma Samira ya ninka na da, dan yanzu safe da rana da dare yana gidan su, shi da mu'azzam sun zama abokai sosai, kullum soyyayar su k'ara k'arfi take, yacce suki son junan su da kula da junan su sai ya baka sha'awa, shi ya saka suka had'u kamar kar su rabu, sun bala'in sabawa da juna,

Daddy da yaga abun yayi yawa abdulshakur gaba d'aya hankalin shi ya koma kan samira baya kula office sosai dukda yanzu ba wata matsala abubuwa a kamfanin sai k'ara kyau suke, yaje ya sami kawun samira yanzu an tsaida ranar biki nan da wata uku, ranar da aka gaya ma abdulshakur wata uku ne ranar ya wuni cikin b'accin rai ya dunk'a mita shi an cuce shi, har sai da ya bama mommy haushi, shi in ta tashi ne a ranar ma a d'aura aure akai ta tunda yanzu ya rigada ya gama had'a gidan shi, bai yarda dangin samira suyi mata komi ba harta kayan daki ya ce shi zaiyi ya d'auke musu nauyin komi.

(Kawai ku kalli chapter d'innan dan akwai matsala lol and gobe zan gama littafin nan yeeeehh, I'm so happy 😂, zan saka ragowar 2 chapters d'in yadda na saba ko kuma zanyi posting d'insu a tare, sai dai goben zan gani...

Please vote and share ❤️)

BA KYAU BA ✔️حيث تعيش القصص. اكتشف الآن