Chapter forty-five

1.5K 190 10
                                    

Tsaye yake a gaban standing mirror d'inshi yana gera hular kanshi, ko ba'a gaya mishi ba shi kanshi yasan yayi kyau, yana jin abokan shi na hayaniya a parlor d'inshi da yake gidan su ne meeting point d'in, d'aukar designer turaran shi yayi ya feshe jikin shi dashi sannan ya fito, tsayawa cak yayi kanya k'arasa cikin parlor d'in saboda maganar da yaji suna yi,

"Gaba d'aya ya saka business partners d'inshi sunyi pulling out, ba abunda ke shigo mishi yanzu"

Ko baiji suna ba yasan hirar wa suke, k'ara gera tsayewar shi yayi, ya k'ara baza kunnan shi,

"Kullum Yana cikin kira dan Allah muyi mishi magana mu bashi hakuri, yace ko company d'inshi yaje baya sauraron shi"

"Kai yanzu kana tunanin in har kayi mishi magana kai zai saurare ka, ka manta zuciyar Abdulshakur ne, ai tunda ya ruga da yayi marking d'inshi sai dai kawai sorry"

"Yanzu a ko wane lokaci zai iya yin bankrupt, ga dukan shi da yayi ya saka shi sati a asibiti har hak'orin shi sai da ya fita"

"Ka gaya mun kada na saki na shiga bad side d'inshi, dan he can be very scary"

"It's so sad though, he used to be part of us"

"Kaga, ismail fa shi ya jawo wa kanshi bashi da matausaya, haka kawai yaso ruguza rayuwar y'ar mutane bata mishi komi ba"

Da yaji suna son zuwa wurin wato tuno mishi da ranar da ya tsana a rayuwar shi yayi saurin shiga parlor d'in, suna ganin shi kowa yayi shiru, kamar munafukai ga duka suka juyo suna kallon shi, shima yi yayi kamar baiji maganar da suke ba,

"Me kuka tsaya kuna kallo na, is there something on my face?"

Yayi maganar yana tab'a fuskar shi, ai kuwa kamar had'un baki gaba d'ayan su suka saka iho suna mik'ewa suna yin wurin shi, shi abun mamaki ma ya bashi, nan suka fara tafawa dashi suna cewa yayi kyau, share su yayi dan yasan so suke su wayance. Gaba d'ayan su fitowa sukayi harabar gidan, kowa ya shiga cikin motar shi, suka yi convoy Abdulshakur ne a gaba dan shi ne best man.

Tuk'i yake yi amma hankalin shi gaba d'aya baya wurin, yau zai saka samira a idanunshi, wani dad'i yake ji tare da tsoro, yana ji duk duniya ba wanda yake jin tsoro kamar ta, saboda ita ce wacce kalamunta kamar dafi ne a wurin shi, ita ce wacce zata iya tarwatsa mishi farin cikin shi a sakwan d'aya ta tura shi cikin ramin bak'in ciki in har ta bud'e bakinta, shi yasa yanzu baya tab'a so su had'u, kullum sai yaje asibiti da tana nan, ko washe garin ranar da yayi wannan mugun zazzabin sai da yaje da daddare dan ji yayi in har bai ganta ba to bazai tab'a samun kwanciyar hankali ba, ranar kuwa yaci sa'a dan yana bud'e d'akin ya tarar ba kowa ga ita kuma a kwance tana bacci, haka ya tasa ta a gaba ya dunk' kallo Yana murmushi bai tashi daga wurin ba sai da yaji alamun ta kusa bud'e idanunta, ranar yayi bacci harda munshari, tunda ga lokacin kullum sai yaje amma basa tab'a had'uwa dan baya bari, ga haisam na bashi update akan jikinta, akwai ranar da suka had'u da mu'azzam, ranar ba irin kunyar da baiji ba daga baya ya rok'eshi da kada ya gaya mata, yanzu dai shi da mu'azzam sun zama abokai, dan sunyi exchanging numbers kuma da aka sallame ta daga asibiti, shine ya dawo bashi update d'in.

Parking motar shi yayi a harabar gidan, tun kan ya fito yaga abokan shi suma sun gama isowa, gaban shi fad'uwa ya dunk'a yi, shi dai kawai addu'a yake yi, koda suka shiga parlor d'in da kyar, da kyar ya hana kanshi kai idanunshi wurin da matan amaryar ke zaune, yana ganin duka sauran abokan nasu sakayu wurin su suna gaisawa, shi dai wurin khalifa yayi, gaisawa sukayi da farida sannan suka fara tattaunawa da abokin nashi, hira kawai suke amma hankalin shi gaba d'aya baya wurin, so yake ya juya ya ganta amma yana tsoron in har ya saka ta a idanunshi bazai iya d'auke su ba, hira sosai suke da khalifa suna da dariya, ji yayi kallo yayi mishi yawa, irin feeling d'in nan in wani ya saka a gaba yana ta kallo, kai idanunshi wurin yayi sai ga yayi kicibis da idanun samira, tana ganin sun had'a ido tayi saurin sunkuyar da kanta, ita daman ke mishi wannan kallon, abun ne ya bashi mamaki sosai, me haka ke nufi kenana, k'ara k'ura mata ido yayi, numfashin shi cak ya d'auke, masha Allah kawai yake cewa a ranshi, tayi bala'in kyau, mai tab'a ganinta da irin kwaliya haka a fuskarta ba, shi har kyan da tayi ya mishi yawa ma, sauri yayi ya d'auke idanunshi daga kanta ya maida kan khalifa da yaga kallon nata da yake yi nasan yin yawa, amma yanzu gaba ki d'aya bama ya gane me abokin nashi yake cewa, ganinta da yayi ya gama susuta shi.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now