Chapter seven

1.7K 181 1
                                    

Sanye yake cikin riga bak'a short sleeve da kuma bakin sweatpants, yayi mugun kyau kayan sun kara fito da kyan shi da farin shi, sauri yake sosai ya karasa wurin daddy dan amal tafi 20 minutes da zuwa da gaya mai yana ne manshi, da sallama ya shiga parlor din, yana ko cusa kanshi ciki yaga daddy a zaune akan kujera mommy na gefan shi yayi saurin karasa wurin su tare da tsugunna wa a k'asa, yana zama ya dago kanshi yayi musu barka da dare sannan yace

"daddy ga ni, ance kana nema na"

daddy baice komai ba na tsawan mintuna biyar, Abdulshakur kuwa addu'a ya shiga yi Allah yasa ba wani laifin yayi ba, pallor din yayi tsit sai kawai karan tv da kake ji, sai da daddy ya kara wasu mintuna baice komai ba sannan can kuma yayi muting tv din ya dawo da hankalin shi ga Abdulshakur, mommy kuwa kanta na k'asa amma kuma duk nutsuwar ta tana gare su, daddy ne ya fara cewa

"yanzu fisabillahi abudulshakur abunda kayi ka kyauta? Iye?, yaushe zaka dai na nuna mun ban isa da kai ba?? Ace babban mutum kamar Naseer Abdullahi ya kira ka har sau ba adadi kaki daga wayan shi, wannan ya dace? Ka sanni duk lokacin da ka wulaqanta wani aboki na ko abokin hud'ata kamar ni ka wulaqanta ne, ka nuna ba ka dauke ni a bakin komai ba, ka nuna bani da wani matsayi a wurin ka, wannan ai nuna rashin respect ne k'arara, haka wasu za suce ba'ai muku tarbiya ba"

haka daddy yayi ta ma Abdulshakur fada, duk fadan da daddy yake mai kanshi na k'asa, kunan shi na sauraron shi, sai da ya bari daddy yayi mai isar sa ya tabbata ba wani abunda zai kara fitowa daga bakin shi sannan shima ya fara nashi bayanin,

"Kayi hakuri, agaskiya abunda nayi ban kyauta ba amma banyi haka da gangan ba, waya ta ce ta samu matsala kuma ban samu damar gyara ta ba sai jiya saboda aikin da yayi mun yawa, daddy bazan taba iya wulaqanta wani abokin ka ba saboda nasan in nayi haka kamar kai nayi wa, amma zan je har gidan shi na bashi hakuri, kuma kaima ina rokan ka da dan Allah ka gafarce ni"

jikin daddy yadan yi sanyi, ya tuna abunda matar shi ta gaya mai kan abdulshakur ya shigo dakin da a tsaya aji ta bakin shi, ba lalla haka abun yake ba, anya kuwa bai wa abudulshakur tsawri akan wasu al amuran? tuni yaji san danshi ya baibaye shi ya kuma gane bai kyauta mai ba amma kuwa ta wani bangaren yasan halin abdulshakur da shegen taurin kai tunda ya nuna mishi baya san diyar alhj naseer yasan ko mai za'a mishi kuwa bazai taba santa ba, yasan abudulshakur yana kula ta ne saboda shi badan kowa ba kuma ba dan komai ba sai dan ya mishi biyayya a matsayin shi na uba a wurin shi, kara jin tausayin dankan mishi zuciya, sai da akan dan jima kadan kowa yayi shiru a parlor din sannan daddy yace

"shikenan jeka, kuma ka tabbata kaje ka bashi hakuri kayi mishi bayani dan bana san surutu, Allah ya maka albarka"

Abdulshakur najin haka ya mike hade da yi musu sai da safe ya bar dakin. Mommy na tabbata wa ya bar side din gaba daya ta juyar da hankalin ta kan alhj yusuf tace

"Alhj, dan Allah zanyi wata magana?"

Alhj yusuf shima gera zama yayi ya tattaro hankalin shi kan ta

"ina jinki hajia"

mommy ta ci gaba da cewa

"ni dai a gani na abar yaran nan ya auri wacce yake so, kai daga ganin yadda yake kasan bai san ita wacar yarinyar, kuma munsan halin abdulshakur in har ya kafe akan abu daya to bazai taba canza ra ayin shi sai dai ba, kasan yana kulata me saboda yin biyyaya a gareka, na tabbata in har akayi auren na tabbas dukan su zasu sha hawala"

Alhj yusuf ya gyada kai "maganar ki haka take hajiya, amma ba zan ce abdulshakur yabar kula wannan yarinyar ba sai dai in har shine yazo da kanshi ya gaya mun baya san kasance wa da ita, inhar ya gaya mun wannan haka ni kuma nayi alkwarin barin shi ya aure duk wadda yake so"

haj aisha tayi shiru, indai abdulshakur ne to tabbas za'a shekara wannan yaran da baya ra'ayin mata, amma sai tace wa alhj yusuf

"shikenan Allah yasa shi yafi alkairi"

haka suka juya suka ci gaba da kallan tv suna dan hin hirar su.

Abdulshakur kuwa yana fita daga side din daddy side dinshi yayi, yana shiga ya zarce bedroom dinshi ya haye saman gado, wani irin haushin nabila yake ji da ma zai iya kiranta ya cici mata mutunci haka kawai ta hada shi da daddy dinshi, shi da am zai iya tun karar daddy yace mishi baya santa amma kuma shi a ganin shi wannan rashin kunya ne, haka ya ci gaba da tunanin shi har bacci yayi gaba dashi.

Gobe mama zata dawo daga abuja, su samira sun duk'ufa sai gyaran gida suke ita da masu aiki, su goge can su wanke can su share can, safiya kuwa tace yau ita ce me kula da iman dan haka ba aikin da zatai, gwaggo ko sai tsiya take mata da Allah wadaran irin wannan san jiki nata, haka dai sukai ta fama tun safe har kusan sallah magriba, suna gama wa samira tayi ban daki dan yin wanka saboda tana so taje Wellcare ta siyo wasu spices da zata ma mama girki dan na kitchen duk sun kare, tana gama wankan ta ta hada tare da alola ta fito, tayi dressing mirror ta zauna, yin duk abunda ya zaman mata al'ada tayi sannan ta tashi ta nufi drawer dinta dan daukan kayan ta zata saka, tana bude wa ta yi aran gama da rigan nabila da ta saka lokacin da taje taya su aiki abban ta zaiyi baki, ta dan tsaya tana kallan rigar sai kuma can ta juyar da kanta ta hau neman kayan da zata saka, ta watsar da al'amarin nabila acan kasan ranta ta ci gaba da rayuwar ta kamar ba abunda ya faru yau kwana kusan biyar da faruwan abun, ta boye damuwar ta saboda bata san gwaggo ta dago ta amma shekaran jiya sai da ta jawo ta cikin daki ta fara yi mata tamboyi in akwai abunda ke damun ta, duk ta fada kuma ta lura ba yadda take da ba, samira tayi saurin sha shantar ta zancen ta cewa kawai mamanta take missing haka gwaggo ta kale ta badan ta so ba hade da ce mata Allah ya yaye miki wannan zurfin ciki naki ace abu na damun ki amma baza ki fito ki fada ba wa kowa ba, wannan wace irin rayuwa ce kika dauko ma kanki, haka gwaggo ta dunk'a yi mata fada, can kuma daga baya suka kama wata hirar.

Samira ta shirya cikin doguwar riga blue ta material dinkin yayi kyau sosai, fara yin haramar sallah tayi sai da tayi har isha'i ta hada tare da shafa'I da wuturi ta gama adduo'in ta tsab sannan tashi ta ci gaba da shirin ta, yafa dan karamin farin mayafi tayi da yake rigar ta dogon hannu ne da ita ta sabi jakar ta da mukullin motar ta sannan tayi wuje. Ta na fita ta ci Karo da safiya itama ta shirya harda shirya iman, samira ta saki baki ta bita da kallo

"ke kuma sai ina"

safiya na washe baki tace

"ai raka ki zanyi"

samira ta ja wani dogon tsaki ta fara tafiya

"kinsan Allah baki isa ba, lokacin baccin iman ya kusa baza ki bini ki wahalar mun da y'a ba kuma nasan na tafi da ke sai kin sani kashe kudin da banyi niya ba dan haka koma daki kiji kisa mun yarinya bacci kinga ma harta fara gyangyadi"

ta nuna iman, safiya ta kumburo baki sannan ta fara buga kafa tana yin hanyar dakin ta daman already ta dauko kayan baccin iman daga guest room, samira kuwa bata ma bi ta kanta ba kama hanyar ta tayi ta fuce abunta amma sai da ta tsaya tayi ma gwaggo sallama.

Tayi parking motan ta a waje sannan ta kama hanyan cikin WellCare, mutane ne cike a wurin haka ta cusa kai tashiga yin abunda ya kawo ta, wayan ta tayi unlocking dan tayi list saboda kada ta manta bata siyi wani abun ba, siyyanta take hankalinta ta kwance har tazo kan aisle din mouthwash daman nata ya kare, tun daga nesa ta hango guda daya ne ya rage akan stand din da alama they're out of stock , addu'a take kada wani yayi saurin riga ta, tana isa tayi saurin kai hannun ta hadda yar murnar ta amma tana sa hannu taji hannun wani akan nata, juyo wa tayi da niyar sauke ma ko wanene buhun masifa amma sai tsayawa tayi cak. Ta kasa ko motsi, zuciyar ta ce take wani irin bugawa kamar zata fito daga kirjinta, idonta mai zai gane mata mata yau dinnan.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now