Chapter Three

2.3K 190 0
                                    

Wacece Samira

Mahaifin samira Malam Bashir labaran haifaffan dan garin jos ne amma kuma Allah yayi ma duk mahaifan sa rasuwa ya tashi cikin maraici daga shi sai shi wani abokin baban shi ne na kud da kud ya rike shi da yake mahaifiyar shi yar garin nijar ce duk yan uwanta nacan kuma basan auran ta da mahaifin shi suke ba koda ta mutu bawanda ya waiwaye shi

Malam bashir a garin jos yayi primary dinshi har secondry dinshi daya kammala karatun shi abokin baban shi Alhj tanko yace zai dawo kano domin yin kasuwanci aikuwa mlm bashir bai ga ta zama a jos ba daman bashi da kowa haka ya tattara kayan shi yabi alhj tanko kano da suka zo kano suka sauka a unguwar dorayi nan dai suka cigaba da sai da suka tara abun arziki sannan Malam bashir ya koma makaranta nan kano politicnic ba'a kuma dade ba ya kamala ya samu aiki iya rufin asirin ah wanan lokacin ya hadu da Asma'u wacce take diyar mai gidan sa kuma ita haifaffiyar garin kano hausa fulani sai dai malam bashir ya dan tara kudin shi sannan aka musu aure kuma shima bada jima wa ba ta haifi yan biyu murjanatu da muazzam yaran basu da laifi suna da kyawun su dadai gwargwado ba jimawa da haihuwar su, malam bashir ya samu karin girma wurin aikin sa aiko suka fara ganin canjin rayuwa sun mallaki gidan su harma ya samo wa matar shi Asma'u aiki aiko tuni aka samo musu me kula dasu suka da suna bawa yan biyun su lokacin basa rashin lura dasu haka rayuwa ta cigaba da gudana suna rufin asirin su zasu ci maikyau kuma susha mai kyau

bayan shekara hudu da haihuwan murjanatu da muazzam Asma'u ta kara samun ciki bayan wata tara ta haifi diya mace wacce bata cika Kyau ba can sosai amma kuma akwai yalwan gashi ya cika kanta taf sunyi murna sannan ran suna aka saka mata Samira, samira ta tashi cikin yan uwanta da yayyanta da mahaifatan masu mutukar santa haka ta fara girma har ta shiga nursery school samira nada shekaru uku Asma'u ta sake samun ciki suka dunka murna har ta haihu ta samu yarta mace aka saka mata suna safiya.

Safiya nada shekara biyu a duniya Allah yayi ma Malam bashir rasuwa yayi accident yayin da yake hanyar shi ta zuwa jos ba karamin tashin hankali Asma'u tashiga ba tayi kuka mai isharta sannan ta bar komai ga Allah ta gama takabar ta sannan Malam tanko ya tattaro gadon su samira ya danka mata nan fa Asmau ta du kufa kula da yayan ta suka daine a gaban tana dan aikin ta kuma yayan ta na taimaka mata haka ta saka su makarantar boko da islamiyya masu kyau da karatu haka aka cigaba da rayuwa har muazzam da murjanatu suka gama secondary suka sanna da yardar Allah suka sami admission a BUK murjanatu na karanatar Microbiology shi kuma muazzam na karantar accounting a lokacin samira na jss2 kuma shakarunta basu wuce 13 ba

Samira bata da kyau duk yan uwanta sunfi ta kyau amma duk tafi su gashi da kyan fata, fatar ta wani irin laushi ne da ita kuma bakin fatar ta nada masifar kyau kuma ga kyan hali samira ta kasance yarinyar mai mugun san jama'a da tausayi baza ka taba jin anyi cece kuce da ita ba ko fada da ita, ba ruwan ta rayuwar ta kawai take yi wannan halin nata shi ya haifar mata da farin jini da wuya ka zauna da samira taki shiga ranka tana da saurin shiga rai duk wanda ya santa yana ji ta ita sosai ga addin duk da kankantar shekarun ta samira na jss3 ta haddace Alqurani ka kira'ar ta masha allah har gasa ake daukan ta daga makaranta kuma da wuya ta dawo bata dauki 1st ba haka samira na shiga ss1 ta hadu da nabila,

nabila kyakyawar gaske ce bazan taba iya misalta muku kyanta ba gata fara ya gashi maihaifin ya dan siyayasa ne kan kice mene shakuwa ta kankama tsakanin su mai karfi sun zama manyan kawaye duk yan gidan su nabila sun san samira haka ma duk yan gidan su samira sunsan nabila haka har suka saka iyyayen su mata abokantaka suna cikin haka har suka gama secondary school samira na mutukar san zama doctor so medicine take so tayi nabila itama tace mata shi zatai sai dai mahaifin nabila yaso yafitar da ita kasar waje ta karasa karatun ta amman sam sam taki tace ita tana tare da samira haka da dunka rigima har sai da ya barta a nigeria haka suka zana jamb kuma sunci sosai sun samu makin da ake so tuni aka fara shirin shiga BUK

ana haka aka fara shirye shiryen bikin murjanatu wato yar samira wacce zata aure wani dan kasuwa mai kudi me suna sadiq marshal anyi biki kuma hajia Asma'u tayi ma murjanatu duk abun da uwa zata ma yarta tayi kokari sosai bayan an gama bikin da watanni su samira suka fara shekarar su ta farko a buk koma ranar mijin ya murjanatu ya mata albishir da sabuwar mota me suna civic joker motar dai dai da ita kuma ta isheta rayuwar makaranta samira tayi murna sosai tuni ta fada driving school lokacin da sukai nisa a first year dinsu samira ta hadu da faruk wanda shima course dinsu daya sai daishi a shekarar shi ta uku yake sun fara soyayya da shakuwa me karfi kuma duk da haka samari basu bar zuwa gurin samira ba abun kuwa na batama faruk rai wata rana har tsokanan ta nabila tayi tace duk da tafi ta kyau amma kuma samira ta fita farin jini da samari kawai samira dariya tayi ta canza zancen haka suka gama first year suka fada second year ai kuwa karatu ya fara zafi sun dan yi nisa ya murjanatu ta haifo diyar ta mace me suna maryam sunan kakar su taci amma ana ce mata iman samira ta dauki san duniya ta dora mawa iman ko da suka zo wankan jego ita take mata kome bayan arbain da zasu koma su murjanatu suka alkawarin kawo mata ita yaye haka rayuwa ta ci gabar wa samira ita da babbar kawarta nabila da kuma saurayin ta faruk wanda soyayya sosai suke har su nabila suka fara semester su ta farko a shekar su ta hudu a jami'a.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now