Chapter fourteen

1.5K 172 2
                                    

Zagaye d'akin ta kawai take tayi tunda ta shigo cikin shi minti biyu da suka wuce, safiya ta cuce ni fad'a a ranta, wannan wani irin zubar da aji ne, tasan ko ta gaya mishi ba ita ce tayi sending message d'innan ba bazai tab'a yarda ba, yanzu ya zatayi, wani zagi ta k'ara d'ura ma safiya a cikin ranta, duk da tana da laifi da ta bata wayarta bayan tasan halinta, k'ara daga wayar ta tayi ta karanta alert din, ga sunnan shi k'arara a jiki, ji tayi kamar ta kurma iho, dan ma tsabar rainin wayo irin nashi, me yakon ya turo dadai 50,000 din shine ya tura mata da 500,000, me ya mai da ita?, talaka?, wani haushin shi taji ya zo mata mak'ogaru, bata san lokacin da ta dannan number dinshi ba ta kira shi dan ta sauke mishi buhun masifa, har layin ya gama ringing bai dauka ba, k'ara kira tayi, shima bai d'auka ba, haka tayi ta yi har sai da ta kira shi sau biyar amma duka bai dauka ba, wani dogon tsaki ta ja, da bata yi sending message dinnan ba da ba abunda zaisa na kira shi har yak'i daukar waya ta, tuni ma da na danna mishi block an wuce wurin, k'ara jan wani tsakin tayi, tayi hanyar gadonta ta zauna, mintsinin lebanta ta shiga yi yayin da ta k'ura ma wayar ta ido, tunanin waye abdulshakur ta fara, da gangan zai iya ganin wayar ta yak'I dauka, wani masifaffan girman kai ne ya mishi yawa, ba tasan maza masu shegen iyayi, yanzu da ta zauna ta fara tunanin ya tara abubuwa da yawa da bata so ga d'a namiji, ita bata san mai mata suke so ajikin shi ba, mutum sai fari kamar aljani, da idanu kamar na mage, can ta k'ara tunawa saboda shi ne tayi fad'a da aminyar ta wadda shekara da shekara suna tare, ba wanda ya tab'a jin kansu, wani haushin sa ta k'ara ji ya rufe ta, yau ko ta mutu ko tayi rai sai ta gaya mishi bak'ak'en maganganu in har ya dauki wayarta, k'ara danna mishi kira tayi again har ta gama ringing baiyi picking ba, masifa ta shiga za zaga mishi acikin ranta zagin shi ne kawai batai ba, can da taga bashi da niyar daukar wayar ta, ta mik'e ta shiga toilet danyin alwala dan ana ta kiran sallar azahar.

Shima din da yayi wanka ya shirya tsab, masallaci yaje, bayan ya dawo wurin mommy ya nufa dan cin abinci, sai da ya gama duk abunda yake yi a tsanake sannan ya koma side dinshi, yana shiga wurin da wayar shi take a ajiye yayi, daukar ta yayi ya kunna, missed calls dinta ya gani guda bakwai, wani murmushi ya saka, yau ita ta kira shi har sau bakwai, wani dad'i ne ya kama shi dukda yasan kiranshi da tayi bawai kiran arziki bane, samun wuri yayi akan gadon shi ya zauna ya k'ura ma wayar shi ido, sai murmushi yake zubawa, kana gani kasan jira yake ta k'ara kira, shima sai ya rama ja mishi ajin da tayi, ai kuwa yana cikin tunanin sai ga kiranta ya shigo, ka'ara sakin wani murmushi yayi har duk hakwaranshi sai da suka fito, yayi kamar zai dauka can kuma ya fasa, har sai da kiran ya katse, kan ya ankara har ta sake kira, wannan karan dai ya dauka, amma sai da kiran ya kusa tsinke wa, bai ce komi ba da ya saka wayar a kunan shi, ji yayi tayi ajiyar zuciya, kana ji kasan akwai tsora tare da ita kuma k'okari take ta taro dukkan nutswarta, sauran k'iris ya fashe da dariya da kyar ya iya k'unshe ta, can yace

"kin kira ni kinyi shiru, in ba abunda zaki ce zan kashe wayar saboda ina da abun yi in ke baki dashi"

yadda yayi maganar kwata kwata ba alamar wasa a muryar shi.

Samira wani dogan tsaki taja a ranta, haushin kanta take ji, yana daukar wayar taji jikinta yayi sanyi duk yadda tayi alkwarin ci mishi mutunci ta kasa, husky voice dinshi na dakan kunnan ta, taji gabanta ya fad'i, hankalinta da nutsuwarta ta tattaro, ta fad'a a hankali,

"ka k'ara zero guda d'aya, kud'in ba haka suke ba, ka aiko account details dinka in mai da maka da ragowar kudin ka"

shiru taji anyi, sai can daga d'ayan b'angaren aka ce

"ina da idanu nasan me na iko miki, kuma ganin dama ce ta saka nayi, in bakya so ki bayar, ko ki saddaka koma ki zubar ya rage naki" yana gama fad'a ya kashe wayar.

Samira cak ta tsaya ko dauke wayar daga kunanta ta k'asa tsabar mamaki, amma ya cika dan rainin wayo, jin zuciyarta take tana tafarfasa tsabar masifa, taga in yar zatai yi mishi magana a waya to tabbas baza ta tab'a amayar mishi da dukkan abunda ke cikin ta ba, kan number dinshi ta latsa ta shiga message, nan ta fara sauke mishi buhun bala'i, typing kawai take yi sai da ta gama tsab a karshe hadda ce mishi, zata nuna mishi ko ita wace sannan tayi sending, tana ko aika wa da sak'on tayi blocking number d'insa, wani sanyi taji a ranta, mik'e wa tayi ta fara shirin fita.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now