Chapter twenty-six

1.4K 159 0
                                    

Tunda ta fito daga gida gabanta ke fad'uwa, ji take yi kamar ta bud'e k'ofar motar ta zura da gudu, ya muazzm se kallanta yake ta gefan idanshi, daman shi ne zai kaita airport, ita tasan kallan me yake mata, tayi wani shiru kamar wata kurma shi yasan ba haka suka sa ba ba in har suna mota d'aya labarai sukeyi kamar baza su daina ba,

Duk yanzu bashi ne a gabanta ba, ita kad'ai ta san halin da take ciki, suna shiga airport d'in gabanta yayi wani irin mummunar fad'uwa, ita ko ta shiga uku yau, ina zata saka kanta, dama bata zo ba, har zuwa jiya ji tayi kamar ba abunda zai d'aga mata hankali in taga shakur amma yau tunda ta tashi da asuba ta neme confidence d'in nata ta rasa, gaba d'aya yin abu ta d'unka yi salalo salalo kamar wadda bata da jini sai da gwaggo da mama suka ce mata tayi sauri in ba haka ba za tayi letti, sannan ta d'an fara hanzartawa,

Tun daga nesa da hangi mutune a wajan, har ta hango nabila, hannatu da meena, farida da wasu k'awayen nasu ma alamun kawo ya kusa hallara, kwata kwata bata kai duban ta zuwa inda abokanan ango suke a tsaye ba, saboda bama taso ta ga ko ta had'a ido ta mutmmin da yanzu ta tsani gani a duk duniya,

Ya muazzam ya sami wuri yayi parking dai dai inda su nabila suke, ai kuwa suna ganin ta acikin mota suka saki murna har y'ar rige rigen bud'e mata mota suke ita da farida, sun kuyawa sukayi suka gaishe shi har da sauran k'awayen farida suma sai da suka gaishe shi,

Samira na fita daga mota nabila da farida sukayi kanta,

"Kinsan Allah da mama tace mana zaki zo kawai dai nace tom ne, gani nake zata canza mind dinta" farida ta fad'a yayin da take gera ma Samira mayafin da ta yafa a kanta,

Nabila ce ta fara jan hannun samira da farida dan su k'arasa inda sauran mutanan suke had'e da cewa,

"Kin manta mama ne, Kinsan da wuya ta canza magana, ba tayin magana biyu, in tace eh to eh ne kuma tace a'a a'a ne"

Samira kuwa ba abunda take sai murmushi, tana bala'in san k'awayenta, yanzu d'an ganin sun da tayi har sun rage mata damuwar ta,

Haka suka tsaya suna jiran sauran mutanen su gama hallara sai kawai su shiga tare, ba ayi minti ashirin ba kowa ya iso amma banda abdulshakur,

Khalifa da ismail ne suka k'arasa inda farida da k'awayenta ke tsaye, angon ne ya fara duban nabila,

"Wai dan Allah Abdulshakur bai gaya miki inda zai tsaya bane?, sai kiranshi muke muji yana ina amma shiru baiyi picking call d'in ba kuma na kira amra tace mun ya fito tun d'azu gashi yanzu kawai shi ake jira"

Samira najin an ambaci abdulshakur zuciyar ta fara bugawa, da wani irin k'arfi take bugawa sai da ta kalli meena dake kusa da ita taga ko taji, gani tayi hankalinta bama ya wurin ta dan kowa a wurin nabila yake kallo wato ana jira aji amsar ta, addu'a takeyi Allah ubangiji yasa ya fasa zuwa, Allah yasa aiki ne zai rik'e shi saboda bata shirya ganin shi ba,

"Nima dai rabun da muyi waya tun jiya da daddare kuma ni bai gaya mun wani abu zai tsai da shi ba amma nasan ya kusa zuwa mu d'an k'ara mishi 10 minutes"

Bin babbar aminyar tata tayi da kallo, wai yaushe zata dai na k'arya ne akan abdulshakur, duk ya mai da k'awarta tata wawiya kuma mak'aryaciya, mene zai cinyeta in ta fad'a misu gaskiya ita ta tabbata ba wata wayar da sukai,

Tana wannan tunani taji an shek'e da dariya, kai duban ta tayi taga khalifa na jan ismail ta baya da wuyan rigar shi, k'ara kallan su farida tayi fuskar ta d'auke da alamar tambaya,

Farida na dariya ta fara jawabi,

"Ismail ne ya dage sai zuba miki kallo yake bai ji lokacin da khalifa yace mishi su tafi ba su koma wajan suaran tsabar ya saki baki yana ta kallon ki shine shi kuma khalifa ya gaji ya fara jan shi ta wuyan riga" dariya kowa yake yi a wurin har abokan ango bayan farida ta gama bada labari

"Ina ji dai kin sami shiga" meena da take kusa da samira ta rad'a mata a kunnan ta

Wata irin azababbiyar kunya ce ta rufe samira, sauri tayi ta sunkuyar da kanta, ita bama tasan yana yi ba saboda tana can duniyar tunani

Suna tsaye a haka, suka ga wata dalleliyar motar ta shawo kwana, nabila ce tace finally gashi ya iso,

Gaba d'aya wuta d'auke wa Samira tayi, jin wani irin fad'uwa gaba takeyi zuciyar ta sai faman harbawa take, kanta ta k'ara saukarwa k'asa ta shiga yin addu'a, tana ji abokan khalifa suka fara hayaniya da suka ga abdulshakur, sai mitar ya shanya su a rana suke, ko da wasa bata d'ago ta kalli inda suke ba,

Ji tayi an fara jan hannunta, sai a lokacin ta d'ago kanta, taga abokan ango har sunyi nisa sun kusa isa cikin airport, itama fara jan akwatin ta tayi tabi bayan su.

$$$$$$$$$$

Tunda yayi kwana ya hange ta, yau dai yana ganinta yayi saurin kwada idanun shi, be kula zuciyar shi ba da take faman bugawa a k'irjin shi samun wuri yayi parking dai dai wurin abokan nashi,

Shima ko da wasa bai kai kallanshi inda k'awayen amaryar suke ba, yana isa yaga su shahid sun fara mishi complaining hak'uri ya basu ya gaya musu taraffic ne ya tsai dashi sanna suka fara yin haramar cikin airport d'in,

Tun da ya samu ya zauna a seat d'inshi na business class bai juya ba, ya sani sarai su wane a gefan d'ayan side d'in, k'awayen farida dan gaba d'aya business class ya kama wa kowa,

Wata magazine ya bud'e ya fara karantawa, kunnuwan shi biyu d'auke da AirPods , wani ya ganshi zai rantse yana fahimtar abunda yake karantawa yayinda gaba d'aya tunanin shi na wata duniyar, shi kad'ai yasan rad'ad'i da azabar da zuciyar shi ke mishi saboda yak'i bata abinda take so, wani b'arin na zuciyar shi ke azalzalar shi da ya juya ya saka ta a idanunshi ko ya sami sausauci amma sam taurin kanshi yak'i barin shi,

Alkwarin yayi ma kanshi koma komai rintsi komai wuya bazai tab'a sab'awa, komai zafi da k'unar da zuciyar shi zatai mishi sai ya cire Samira daga ranshi, kai daga rayuwarshi gaba d'aya, sai ya tabbata ba abunda zai sake had'a su in har suka gama bikin nan, koma a yanzu da ake shirin fara bikin zai tabbata ba wani abu da zai shiga tsakanin su, shi yasan zai sha bak'ar  wahala amma kallen shi da zata yi cikin idonshi ta gaya mishi rashin amincewar ta da zancen zai fi mishi komi muni a rayuwar shi,

Lumshe manyan idanunshi yayi, gaba d'aya bama yaso yayi tunani saboda jin zuciyar shi yake a cikin mak'ogron shi kamar zata fito ta bakin shi tsabar yadda yake jin zafi da ciwon abun,

Yana wannan yanayin yaji pilot d'in na cewa suyi fastening seatbelts d'insu and they should remain in their seats saboda yanzu jirgin zaiyi landing.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now