Chapter thirty-four

1.5K 190 1
                                    

Motar tayi tsit tunda suka shige ta ba wanda ya cewa kowa komi, ko kukan da samira takeyi yanzu ta daina yin mai sauti, sai dai kawai hawayen da suke kwarara daga idanunta, da kuma ajiyar zuciyar da takeyi jefi jefi,

Abdulshakur yayi ma steering wheel din motar wani irin mugun rik'o jijiyoyin hannayen shi sun fito b'aro b'aro kana ganin su, bayan wani mahaukacin gudu da yake shararawa akan titin, zuciyar tafasa take yi, har wani d'aci d'aci yake ji a bakin shi, kana kallan shi kasan har lokacin bai dawo cikin hayyacin shi ba,

Wayar shi ce ta fara ringing wace take zaune a cikin back pocket din wandon shi, banza yayi da ita, ya share ta har ta gama rurinta ta gaji, amma tana katsewa aka k'ara kira, sa hannu yayi ya cirota daga aljihun wandan nashi, bai tsaya kallan screen din ba ya duba wane ya kira kawai ya sauke glass din kusa dashi, ya cilla wayar ta window d'in motar, sannan ya zuge glass d'in, a lokacin bai damu da SIM card d'inshi ba ballan tana abubuwa masu mahimmanci da ke kan wayar, wanda ya kira bai wuce daya daga cikin abokan shi ba kuwa a yanzu shi baya san damuwa.

Tunda suka shiga motar ko da wasa bai kai dubanshi inda samira take ba, yasan in har ya kalle ta ya ganta a cikin yanayin nan zuciyar shi zata iya bugawa,

Bai tab'a tsintar kanshi ba a cikin halin da ya tsince kanshi yau tunda yazo duniya, ji yake dama zai iya tattaro dukan damuwar Samira ya maida kanshi, dama zai iya mantar da ita bak'ar ranar yau, duk d'igon hawayen da ya fito daga idanunta ji yake kamar an saka almakashi ko wuk'a mai kaifin gaske ana yankar zuciyar shi, numfashin shi har wani irin sark'ewa yake, zuciyar shi wani irin mugun zafi take mishi da rad'ad'i, kwalla ce ta sake cika idanunshi, bai tab'a zubar da hawayen da ya zubar ba yau tunda yake a rayuwar shi, ita ba kowan kowan shi ba amma gaba d'aya tabi ta haukata shi ta rikiti shi, bai tab'a zata zaiyi wa mace wannan irin mahaukacin son ba.

Samun wuri yayi yai parking a gefan titi, lumshe manyan idanunshi yayi, tunani ya fara, da bai dawo gidan ba abunda da zai faru, ya tabbata da sai ismail ya keta ma samira mutuncinta, hawaye ne ya zubo mishi, saurin k'okari yayi ya tattaro dukan nustuwar shi da kyar ya samu yayi, bud'e murfin motar yayi ya fito sannan ya fara takawa a hankali ya zagaya wurin samira, yana isa ya bud'e kofarta, ya ganta kanta a sunkuye ga hawayen da sun kasa daina zuba, cire seatbelt d'inta yayi sannan ya tsugunnawa akan titin dake wurin,

Kafa mata wannan mayun manyan idanun nashi yayi baya ko k'iftawa, so yake ya rarrashe ta amma bai ma san daga ina zai fara ba, saboda bai saba rarrashin mace ba ko acikin yayyensa da k'annansa, kuma bai tab'a san wata mace ba itace ta farko,

Ya d'an jima a tsugunnan da yake da yake kuma har lokacin bai d'auke idanunshi daga kallantan da suke ba, sa hannunshi yayi akan cinyoyinta ya juyo da ita ya zamana k'afafunta na waje kuma jikinta gaba d'aya yana kallanshi, wannan abun da yayi ne ya saka samira saurin d'ago da idanunta ta sauke so akan nashi, kallan da yaga tana mishi akwai tsoro k'arara a ciki akwai kuma yarda,

Dole ne abunda ya faru yau ya saka mata tsoro da fargaba, amma shi bazai tab'a cutar da ita ba, bazai tab'a saka ta acikin halin da take ciki ba, hannushi yakai kan fuskarta ya fara share mata hawayen ta, sannan ya k'ara kai hannushi kan l'ebanta wanda ya d'an tsage saboda marin nan da ismail yayi mata ya shafa wurin a hankali, d'ayan hannun shi dake kan cinyarshi ya damk'e da wani irin k'arfi,

Ismail har ya isa ya d'auki k'azamin hannunshi ya saka a fuskarta har yaji mata rauni, hak'oranshi ya saka a k'asan leb'anshi ya ciza ko zuciyar shi zata daina azalzala shin da take,

Yayi alk'awarin sai ismail yayi dana sanin zuwa duniya, sai ya ruguza mishi rayuwarshi yadda yaso ruguza ta samira.

$$$$$$$$$$$$

Bata tsani maza ba a yanzu, amma me ya saka ta biye mishi har ta biyo shi a mota, in har yana san cutar da ita fa kamar Ismail, wani barin zuciyarta ne yace mata, bazai tab'a iya cutar da ita ba, wani barin kuma yace mata lokacin da ismail yake shirin wulaqantata ta ya sanar da ita? ta tab'a zatan zai iya yi mata wannan cin mutuncin da yayi mata?, shima ai haka ya siyeta ya dunk'a nuna mata kula da kuma dad'in baki har ta biye mishi da fara kula shi,

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now