Part 4

111 11 0
                                    

*RIJIYA TA BA DA RUWA...?*
     _GUGA YA HANA_
                              
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ* 

*WATTPAD@ Oum-Mumtaz123*
*INSTAGRAM@itz_me_real_oum_mumtaz*      

           *charpter 4*

******** "Hmm,wallahi Alhaji na gidannan yanayin abin da bai da ce ba kwata kwata a cikin gidannan,kuna ganin yadda yake zuba ma mutane rashin mutunci a kan waccan yar tasa? Wanda kuma daga ciki har matar gidan da babu ruwan ta bai k'yale ba ballantana kuma oga Mustapha?"

'Daya daga cikin su ne ya cafe zancen da fadin "Ai idan ta wannan fannin ne da sauk'i ma! Kuna gani fa tsabagen mugunta da rashin imani irin na mutumin nan yanzu muna cikin watanni na biyar babu albashinmu bacin kuma yasan cewa kaf cikinmu babu wanda ba shi da iyali,kullum cikin aiko mana da sak'o yake wai mu yi hak'uri yana kokarin kashe wata 'yar matsala ne ba shi da kud'i alhalin kuma jiya-jiyan nan kuna gani ya saya ma 'yarsa mota ta kusan million asshirin bacin wanda yake saya mata duk kusan ko wani wata amma dan an ga mu ba mu da gata sai ana mana wasa da hankali"

Ya yi maganar cike da tsananin takaicin halin uban gidan nasu,dayan da tunda suka fara bai yi magana ba ne ya buga wani uban tsaki kamar harshensa zai tsinke shi ma cike da takaici ya d'aura da nasa fadin "Ai mutumin nan idan dai a haka ya ce zai ci gaba da tafiyantar da rayuwar sa ba zai gama da duniya lafiya ba daga shi har fitsararriyar 'yar Tasa! Akoi fa ranar da wata kanwata ba ta da lafiya shekarar da ta gabata na je wurin mutumin nan ina masa rok'o da magiya kan ya taimaka man da kud'in da zan kai k'anwar tawa asibiti idan ya so a cire cikin kud'in albashina,ya ce man na je waje na jira sa kan zai ba da a ba ni dubu hamsin d'in kamar yadda aka buk'ata a asibitin,wai kawai ina jira akawo man kawai na ga dubu biyar wai ya ce na yi hak'uri kud'in ba zai kai ba dake wurin sa? Wanda daga k'arshe ma sanadiyyar rashin aikin da aka ma k'anwartawa ne Allah Ya anshi rayuwarta!"

"Yo ai da ma haka nan halinsa yake,alk'awari da rashin cikawa kam ba daga baya ba,sai fa idan Hajiya Mami ce ta ji tausayinmu take dan taimaka mana da wasu yan kud'ad'e saboda kashe wasu larurinmu,ai matar nan sai da mu ce Allah ya saka mata da alheri ba dai kirki da hak'uri ba!"

Haka nan suka zauna suna ta sakin zance kan abubuwan da ake yi a gidan da bai kamata ana masu ba,d'aya kuwa cewa ya yi shi kam jira yake a biya sa kud'insa tas ya canza wurin aiki domin kuwa ba zai iya wannan kasada ba na zaman gawar shanu babu wani ci gaba.

Abba da Musty ne suka shigo gidan sanye da jallabiya bayan sallar isha'i,wanda suka tar da Zulaykha zaune a inda take tun d'azun ba tare da ta motsa ko nan da can ba. "Sannun ku da zuwa Abbana"  Ta fad'a a lokacin da ta gyara zaman ta daga kishingid'en da ta yi tana mai kallonsu da murmushi a fuskarta da ba kasafai yake ba ce wa ba!

"Yauwa sannu da hutawa Mamana, nan kike zaune kenan?" Abba ya fad'a yana mai shafa mata kanta fuskarsa da murmushi shi ma,"Ummi nan kike zaune kenan?" Musty ya katse masu 'yar guntuwar hirar tasu yana mai ma Zulaykha wani irin shegen kallo ba tare da sun lura da hakan ba saboda da hankalin su bai ta'ba kawo musu wani abu makamancin hakan ba ko da wasa.

Sun dan ta'ba hirarsu a wajen wanda suka d'auki tsawon lokaci kamin suka wuce zuwa cikin babban parlon nasu,sun tar da Mami da wayarta a hannun ta zaune kan luntsumemen kujerarsu ta alfarma da ke cikin parlon.

Kamar babu abin da ya faru d'azu sosai ta sake masu tana masu sannu da zuwa had'i da tarairayar Zulaykha da ke narke jikin Abbanta tana buga game d'in ta na gado.

Abinci Mami ta gabatar musu tuwon semo da miyar d'anyen kubewa da ya sha namar rago daga-daga a cikin miyar yana tashin k'amshin mai na shanu.
Sosai kuwa suka ba je cikinsu suka kwashi gara domin kuwa kaf gidan idan mutum na son ganin cin abinsu da yawa har haka to had'a musu kalar wannan abincin,bacin sun gama zama suka yi a parlo suna hirar su na yau da gobe kan lamarim duniya,sai wajajen 11 kamin suka yi sallama kowa ya wuce zuwa mak'wancinsa.

Sai da ta yi wanka ta kintsa cikin sexy sleeping dress nata had'i shafe jikin ta da daddad'an lotion da ke sake fito mana da madarar kyau na asalin kalar fatar ta,kamin ta d'auko wayarta daga cikin caji bayan ta lume cikin lallausar bargon ta,kan luntsumemen gadon nata.

Datar ta ta kunna inda ta laika shafinta na sada zumunta wato instagram. Saboda post da aka yi na pics tare da vedio take bi d'aya bayan daya tana kallo,idan kuma ta ga wanda ya birge ta takan musu like kamin ta wuce.

Cikin wani irin slow motion ta mike daga kwance da take zuwa zaune,hannun ta rike da wayar tata da ta tsura ma ido sosai saboda ganin sunan ~ZULAYM AHMAD SHUWA~ ya yi appearing a cikin jerin mutanen da suka yi post na photo.

Tsaye yake jikin wata langa-langa da gaba d'aya tsa tsa ya gama masa dameji saboda yadda ya ga duniya,jikin sa kuwa sanye yake da wani d'anyen yadi ruwan sararin samaniya mai saukin kud'i,inda kuma hannun sa ke rik'e da na wata kyakkyawar budurwa da ke gefensa suna kallon tsakiyar idanun junansu a lokacin da aka masu wannan photo duk,fuskarsu kuwa kallo daya idan mutum ya yi mata zai fuskanci cewa lallai ba k'aramin farin ciki suke ciki ba a dai-dai  wannan gabar.

Fari ne fat da shi tsayayyen namiji,mai faffad'an k'irji,idanunsa kamar sexy eyes,sannan kuma yana da dimple ta ko wanne gefe,ga kuma wani irin kwantaccen saje da ke lafe akan kuncinsa da ke shek'i irin na usil shuwa Arab.
La'b'ban bakin sa kuwa sun kasance pinkish colour ne sosai ba kad'an ba wanda haka kuwa ba k'aramin sake k'awata masa kyakkyawar fuskarsa ta yi ba,gashin girarsa ma kad'ai abar kallo ce saboda yadda yake bak'i sid'ik da shi da ya kusan had'ewa wajen guda da na d'ayan gefen,wanda idan mutum ya yi masa kallo d'aya tabbas ba zai so d'auke kansa ba saboda had'uwar tasa ta zarta zuwa duk inda mutum ke tunani!

Wani irin ajiyar zuciya mai k'arfi ta sauke had'i da lumshe tsumammun idanunta tana jin yadda zuciyarta ke dokawa kamar za ta faso k'irjin ta ta fad'o kasa. Sake ware idanun ta ta yi kan pic d'in a karo na biyu,inda ta ga ya ruwa kalmar "Alhamdu Lillahi" Daga can kasa.

Ta d'auki tsawon lokaci tana kallon mutumin da ta shafe kusan watanni biyu ba tare da ta sake kallon wani sabon post da ya dangance sa ba. Wanda har ta fid da rai da tsammani amma sai ga shi Allah cikin ikon sa a lokacin da ba ta yi tsammani ba ya sake dawo mata da "sanyin idaniyarta" Duk da tana da tabbacin shi wanda take hakan domin sa bai san da wanzuwar wata halitta mai kama da ita ba a fad'in duniya.

Tun wajen watanni takwas da suka wuce taga account nasa a shafin ta na insta garin shige-shigenta,harma takai ga tayi following nasa sabida yadda ya tafi da imaninta cikin lokaci kankani! Abin da ta fara yi shi ne bin post nasa tun daga farko tana kallo d'aya bayan d'aya tare da like saboda yadda yake birge ta.

Sannan kuma wacce ke jikin wannan hoton tabbas jikinta na ba ta tana da kusanci mai k'arfi da shi Zulaym din saboda duk cikin pic d'in da yake post guda daidai ne ba ta ciki,wanda kuma haka nan kawai Zulykha take ji yarinyar na masifar birgeta har cikin jini da tsokarta, duk da ma dai a wani gefe na zuciyarta tana kishi da yadda take ganin su kusan ko a wani lokaci tare da mutumin da tun a "Kallon farko" ta ji ya sace mata zuciyarta da bai sa ta kalli wasu mazajen a matsayin maza sai dai mata-maza.

Sai da ta gama tunane tunanenta tsaf,kamin ta koma wajen kwanciyarta bacin ta tofa addu'ar bacci ta rungume wayar tata,a haka nan wani daddad'an bacci ya yi awon gaba da ita mai cike da mafarkan Zulaym.

********'Yan asalin cikin garin Maiduguri ne a unguwar Madina,wanda akasarin mutanen cikin wannan unguwa kuwa yarensu shi ne Shuwa.

Waali da Alina na d'aya daga cikin mazaunan wannan unguwar tare da iyayensu da kuma yan'uwansu,wanda suka kasance yara wa da k'ani ne,wato 'ya'yan maza-biyu.

*vote*
*comment*
*share*

*OUM MUMTAZ✍🏿*

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now