Part 8

75 10 0
                                    

*RIJIYA TA BA DA RUWA*    

           *charpter 8*

********Rik'e da hannun Zulaykha Abba yake yana murza mata su,fuskar sa cike da tsananin damuwa a lokacin da ya iso asibitin har an fito da ita zuwa d'akin da za ta huta. Saboda sun yi nasarar dawo mata da numfashin nata da ya d'auke,a halin yanzu ma bacci take,inda dayan hannunta ke mak'ale da laidar da ake mata k'arin ruwa.

Cikin ciwon da bai gaza na awanni biyu ba sai ga ta ta zam to wata yar shafal da ita,hasken ta ya sake fitowa sosai. Sosai hankalin Abba ya tashi a lokacin da Kabeer ya fad'a masa,wanda babu 'bata lokaci suka wuce asibitin tare da amininsa da kuma masu take masa ba,shi ne fa ya same ta cikin wannan yanayi na barci d'in,sannan kuma dik wasu kudin da aka buk'ata a lokacin ya yi settling,'bacin ya kira Mamy ya shaida mata abin da ake ciki ne yake zaune hannunsa rike da na 'yar tasa da yake jin kamar za ta yo masa nisa,sai aminin nasa ne da ke zaune keta faman tausar sa,had'i da nuna masa mahimmancin d'aukar kaddara mai kyau da kuma akasin haka.(Abokin k'warai kenan).

*****   "Ai kuwa Allah shi kara akan abin da Alh ya yi maka yau! Idan ban da jaraba da kuma naci irin naka mai za ka yi da yarinyar da ubanta bai d'auki uwarka da kai kanka darajaba akan ta? Ban da shisshigi da tusa kai irin naka ko burburwar mutuwa ka gane wannan yarinyar na yi akan titi ai ba ka taimaka mata ba,saboda ubanta sam-sam mutum bai taba masa gwanin ta inda ta dalilin ta ne? Kai kuma ma ba wannan ba! Allah ko duniya sama da kasa za ta had'e ba za ka aure wannam yarinyar ba,gara ma tun wuri na sake jaddada maka saboda ka san da zaman hakan,bawai daga baya ka ce mani ba ka san zance ba!"

Mamy ce ke wannan maganar cike da tabbatar wa har cikin zuciyarta! Shi kuwa Musty da ke ta faman kai kawo cike da tsananin jin haushin Abba da ita kanta mahaifiyar tasa,sai faman sauk'e ajiya zuciyar yake,k'wafa ya yi had'i da ficewa a parlon mahaifiyar tasa ba tare da ya sake ce mata uffan ba.

*****    "Kai a gaskiya yau d'in nan ba k'aramin yunwa ba ce ta azalzaloni tun daga makaranta Ammana" Waleed yaro dan shekara goma sha hud'u ne ke wannan maganar,a lokacin da yake kai lomar joloup d'in shinkafa bakin sa.

Cikin muryarta na dattawa,matar da za ta kai kimanin shekaru hamsin a duniya ta ce "Kai! Amma a gaskiya yau yunwa bai kyauta ma magajin Babana ba,kuma Yayana na kaina!" Ta fad'a tana sakin wani irin murmushi da ke tattare da tsananin rauni ga duk wanda ya san mai ake kira da murmushin da ke fitowa daga k'asan zuciya,ko kuma wanda mutum kan iya-yinta iyakacin samar labbansa.

Da shike yaro k'arami ne,sai bai fuskanci komai ba,sai ma dariyarsa daya kwashe da ita,ya ce, "mene ne kuma magajin Babana Amma na ta kaina?" Tun kamin ta ba sa amsa,Husnah ta shigo d'akin nasu tana rawar sanyi saboda iskar bishiyar tsakar gidan nasu da ke ta faman hura mata farar fatar jikinta da ke jik'e da laima.

"Iyayen surutu an dawo kuma za a d'aura daga inda aka tsaya ko?" Husnah ta fad'a a lokacin da ta wani shige jikin amma kamar wacce za ta koma cikin ta,hak'oranta na had'ewa wuri d'aya muryarta na harhard'ewa.

Dariyar sa ya yi shi kuwa Waleed ya ce "Hmm! Su Aunty Husnah ba dai son jiki ba,ji yadda kika wani shige jikin Amma kamar za ki koma ciki! Wanda ko ni magajin Babanta da ke matsayin d'an auta ban yi hakan ba saboda wariyar launin fata da ake nuna mana."

"Waleed maza maza tashi ka je wajen Yaya ka ce ya ba ka guntun d'auri na maganin Husnah da ke wurin sa saboda na wajena ya kare." Ammah ta yi maganar cike da tsananin damuwa saboda gano kamar ciwon Husnah d'in ne ke k'ok'ari tashi,sanadiyyar sanyin da ya yi mata yawa.

Wanda shi ma sai a lokacin ya lura da yanayin da 'yar uwar tasa ke ciki,bayyi wata wata ba kuwa ya fice daga d'akin da gudun sa zuwa zaurensu,a inda d'akin Yaya yake.

*****    "Amma dai ban taba sanin cewa ba ki da mutunci har haka ba sai yau Alina!! Ashe abin da kike aikata ma mijin naki kenan a bayan idanuna,ba tare da-na-sani ba duk da kasancewar muna cikin gida daya? Mugun halin da shegen son abin duniyar taki dana rasa inda kika kwaso su,suna nan cikin jinin ki har yanzu ashe? Tir da irin halinki wallahi! Gwanda ma ki yi wa kanki fad'a,tare da karatun ta natsu tun kamin lokaci ya 'kure miki! Shashasha kawai wacce ba ta san inda yake mata ciwo ba."

Iyami ce ke wannan maganar cike da tsananin fushi da kuma 'bacin- rai d'in da tunda take Alinar ba ta ta'ba kunsa mata irin shi ba sai yau! Wanda dawowarta daga unguwa kenan yau,wata matar mak'watansu ta tare ta da zancen,tare da irin dibar albarkar da take ma Wali muddin tasa k'afar ta zuwa unguwa,wanda kuma ashe duk gidan da ka fad'a a unguwar za ka tadda ana mai da zancen ne,tare da nuna cewa ai laifin na Iyami ne da ba ta tsawatar ma 'yar tata,ya sa take ma mijin ta rashin kunya,wanda kuma baiwar Allah sam, ba ta san ma ana haka d'in ba sai da yau aka fad'a mata,da kuma maganganun da ta ji yo ita Alinar na fad'a ma Wali a yanzu,wanda hakan ya sa ranta ya yi masifaffen 'baci ba kad'an ba!

Sannan ta d'aura da fadin "Kai kuma wato ga ka sakarai saboda wata banziyar soyayya ka zuba ma yarinya ido,tana maka abin da ta ga dama? Duk ta bi ta gama raina ka ko? To wallahi kai ma ahir d'inka! Idan dai ka ce a haka nan za ka zaune kana ta faman wani lallaba ta kamar kwai,hakan shi ne zai 'bata damar ci gaba da kawo maka iskanci kala-kala. Gara tun wuri ka yi ma tifkar hanci kamin ka zo ka yi da-na-sani daga baya akan son zuciyarka."

Tana gama fad'ar abin da ya shigo da ita kewayen,ta sake sharara ma Alina mari mai rai da lafiya,kamin ta wuce zuwa nata 'kewayen cike da tsananin takaici na wannan halin 'yar tata.

Alina kuwa tun marin farko da Iyami ta mata,ta fashe da wani irin rikitaccen kuka kamar wacca akana wani abin kirki! Abinka ga farar fata,nan da nan fuskarta ta kad'a ta yi janur kamar wacca aka shafa ma jajjagen attarugu.

Wanda kuma mari na biyun da Iyami ta yi mata,shi ne ya sake hargitsa mata lissafi kukan nata ya sake samun matsuguni mai lasisi! Kuka take ba ji,ba gani,wanda hakan ya haddasa mata wani irin matsanancin zazza'bi lokaci da ta fara rawar d'ari!

Wali kuwa tun shigowar Iyami gidan ya dawo daga gajeruwar tunanin daya fad'a,sadda kansa k'asa ya yi a lokacin da Iyami keta faman balbale su! A lokacin da ta mari Alina ma kuwa ji ya yi kamar shi a aka mara har da dafe kumatunsa,yana rintse idanun sa! Tabbas yau da a ce ba Iyami ba ce ta aikata wannan marin babu tantama hukuma ce za ta raba su,saboda soyayyar da yake ma Alina ya zarce misali a rubuce.

Sosai ta sake ba sa tausayi,saboda yadda ya ga tana rawar dari ba ji ba gani,d'aukar matar sa ya yi zuwa cikin d'aki duk da tutture sa da take ta faman yi saboda wani masifaffen tsanarsa da ta mata dira cikin zuciyarta,dalili kuwa shi ne marin da mahaifiyar ta-ta ta yi mata a dalilinsa.

Haka nan suka kwana suka wuni gidan babu wani armashi,ga wani irin matsanancin zazza'bi da ya rufe ta tin jiya har kawo yau babu sau'ki,wanda hakan kuwa ba k'aramin d'aga ma Wali hankali ya yi ba! Haka nan yau ya wuni ko nan da kofar gida bai fita ba yana jinyar matar sa! Inda Iyami kuwa ta d'au fushi da yar ta-ta sosai ko leken inda take ba ta yi ba, duk da kuwa ita ma tana son ganin halin da tilor 'yar tata ke ciki amma haka nan ta yi mirsisi abinta!

Ba don komai ba sai don ta nuna mata kuskurenta,da kuma nuna mata amfanin da Wali ke da shi a cikin rayuwarta ko da kuwa babu aure tsakaninsu! Tausayin Wali take ba na wasa ba,saboda rashin uwa da uba a kusan lokaci da ya ba karamin abu ba ne cikin shekara guda,ga babu wasu dangi na a-zo-a-gani.

*vote*
*comment*
*share*

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now