Part 13

67 8 0
                                    

*RIJIYA TA BADA RUWA...!!*

*©️OUM MUMTAZ✍️*

           *charpter 13*

***** Dawowar Waali daga kasuwa wajen sayayyar da yayi ma y'ar tasa ya fara jiyo kukan yar tasa na masa maraba tin Shigowarsa, da gudun sa,gami da sassarfa ya k'arasa idasa shigewa cikin d'akin!
Kallon d'akin yayi gaba daya babu Alina babu labarinta, sai y'ar tasa dake ta faman callara kuka kamar tasan abubuwan dake faruwa cikin duniyar iyayenta!
Daukar y'ar tasa yayi ya rungumeta! Kamin tayi shuru! Luf tayi a jikinsa tana sakin ajiyar zuciya alamun ta jima tana kuka! Wani irin tausayinta ne ya kamasa!  

Dik inda yasan zai samu Alina cikin gidan ya duba,babu ita babu dalilinta! Wanda hakan yasa shi dawowa dakinta yaga ashe har kayan ta ma rabi da kwata babu! hakan kuwa daya gani ya sake tabbatar masa da hasashen sa na cewa Alina tasa kafa ta gudu tabar jinjirar data haifa ayau yau ba tare da tayi tunanin abinda zai iya zuwa ya dawo mata ba sabida son zuciya da kuma kwad'ayin abin duniya!

Kewayen iyami yayi da nufin sanar da ita halin da ake ciki, amma kuma sai me? Abinda ya tarar ne yayi masifar d'aga masa hankali fiye da misali! Domin kuwa dai bai tarda iyami a duniya ba,Allah ya anshi abinsa!

Wani irin kuka Waali ya fashe dashi! Mai cike da zallar damuwa da kuma bakin ciki! Had'i da t'sant'sar t'sanar Alina sabida yasan itace silar komai akan dik wasu abubuwa da suka faru ayau dinnan sabida dogon buri irin nata a cikin duniya!

Cikin kankanin lokacin rasuwar Iyami ya karade cikin unguwar tasu a wannan daren, tare da guduwar da Alina tayi tabar karamar jinjirar data haifa a wannan ranar! Wanda dik wanda yaji abinda ya faru yakanyi ma Alina Allah wadai!
A tsakankanin wannan lokacin kuwa sosai Waali yayi wani rama mara kyan gani,domin kuwa dashi da yarsa sun tabbata marayun ta ko wanne fanni!

Washe gari da safe akayi ma iyami suturarta aka mika ta gidan ta na gaskiya! Ba tare da an b'ata lokaci ba Waali ya saka gidan nasu a kasuwa dikda yana da sanin cewa itama Alina tana da nata kason,amma kuma yasan hakan da zayyi yafiye masa koma a rayuwa!

Y'ar sa kuwa da nono akuya yake shayar da ita,yaki barin kowa yayi masa rainon ta! A ranar da akayi sadakan bakwai a ranar ya rada ma y'arsa suna *ZULAYKHA* wato mai sunan mahaifiyarsa dayake da burin sawa!
Gidan yazamana daga shi sai y'arsa da wani irin shakuwa na ban mamaki ke sake shiga tsakanin su!

A lokacin da *Ummi nah* (kamar yadda yake fada mata) ta cika sati uku a duniya, ya samu wani Alh zai sayi gidan nasu, aikuwa an ma gidan tayin mutunci, domin kuwa mak'udan kud'ad'e mutumin yasa ya sayi gidan,wanda haka kuwa yayi ma Waali dadi sosai ba kad'an ba!
First abinda ya farayi shine raba kudin tsakanin sa da ita Alina din kamar yadda musulunci ya tanada, Inda nasa kason yafi nata yawa kasancewarsa d'a namiji!

Sannan ya saida shagon sa dake kasuwa, dik wasu basis sikan dake kansa saida ya sauke kamin ya tattara ya nasa da nasa yayi ma garin Maiduguri hijira na har abadan da yake jin bazai taba sake taka kafafun sa cikin su!
Tare da yarsa suka bar gari da itama sam bata yarda da kowa idan ba mahaifinta ba zuwa garin Kano ta dabo tumbin giya,koda me kazo an fika!

*Bangaren Alina kuwa*

Ashe dama sun hada plan tare da wannan Alh,saida ta faki idanun yan unguwar tasu kamin tayi wuf ta fada motar da Alh ya shaida mata zasu gudu da ita,dake ta can gaba da gidan su kadan, A cikin wannan daren suka bar cikin garin Maiduguri zuwa Ben sheik! Inda washe gari suka d'auki hanya tare da Alh ,da kuma driver nasa zuwa can garin Zamfara kamar yadda Alh ya fad'a mata can suka nufa!

Sunsha tafiya kuwa ba dan kad'an ba,kamin suka isa can cikin dare! Abinda zai bama mutum mamaki da halin Alina sam ita bata tunanin jinjirar yarta data baro tare da mahaifiyarta take ba,sai tunanin abin duniyar da zataje ta tarar acan garin Zamfara din,tana jin zuciyarta wasai sabida rabuwa da talauci da tayi na din-din-din!

RIJIYA TA BA DA RUWA???? Where stories live. Discover now